EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 17 a kan Rochas Okorocha

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Muhammad Annur Muhammad

  1. Daular Larabawa ta lalata makaman da 'yan Huthi suka harba mata

    Yemen

    Asalin hoton, EPA

    Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da gano tare da lalata wasu makamai masu cin dogon zango da ‘yan tawayen Houthi na Yemen suka harba mata.

    Ma’aikatar tsaro ta ce babu wanda ya ji rauni a aikin sannan ɓurɓushin makamai masu linzamin sun faɗi ne a wani yanki da ba mutane da yawa a wurin.

    Harin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Isra’ila Isaac Herzog ya isa ƙasar a ziyara irinta ta farko a hukumance.

  2. Ƙarin mutum 22 sun kamu da korona a Najeriya

    Ƙarin mutum 22 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya ranar Lahadi, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

    Waɗanda suka kamun sun fito ne daga jiha biyar da suka haɗa Osun (9) da Abuja babban birnin ƙasar (6) da Delta (4) da Rivers (2) da kuma Kano (1).

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 253,023 ne suka harbiu da cutar, sannan kuma ta kashe mutum 3,135.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Assalamu Alaikum

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya tare da BBC Hausa.

    Sai dai za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da Nijar da maƙotansu.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi.