Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

APC ta ɗage ranar gudanar da taronta na jihohi

Wannan shafin na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh

  1. 'Dole Taliban ta mutunta fararen hula'

    A tattaunawar da suka yi tsakaninsu, shugaba Joe Biden da Firai ministan Birtaniya Boris Johnson sun tattauna kan muhimmancin amfani da matakin diflomasiyya da agaji domin kaucewa sake dagula lamura a Afghanistan.

    Mai magana da yawun Mr Johnson ya ce shugabannin biyu sun amince duk wani mataki da kasashen duniya za su dauka, dole Taliban ta mutunta hakkokin farar hula.

    Sun kuma tabo batun kasuwanci maras shinge a tsakanin kasashen biyu, a tattaunawar ta tsahon minti 90

    Yace za mu tattauna kan batun kasuwanci a ranar Alhamis, batu ne mai muhimmanci. za a cimma matsaya kan wannan batu nan ba da jimawa ba.

  2. Amurka ta yi na'am da matakin China kan sauyin yanayi

    Wakilin Amurka kan sauyin yanayi John Kerry, ya ce yana cike da farin ciki kan alkawarin da China ta yi na dakatar da gina sabbin tashoshin wutar lantarki masu amfani da makamashin Kwal a kasashe masu tasowa.

    Shugaba Xi Jingping na China ne ya sanar da hakan, a jawabin da ya gabatar a shalkwatar majalisar dinkin duniya, wata guda bayan taron kolin da aka yi domin magance sauyin yanayi a duniya.

    Mista Xi ya ce China za ta yi kokarin amfani makamashi mai amfani da hasken rana kafin karshen 2030, sannan za ta rage amfani da kwal daga nan zuwa shekarar 2060.

    A cewar shugaban wannan na bukatar jajircewa, kuma su yi kokarin ganin sun tabbatar da hakan.

    Wani kiyasi da aka yi, ya nuna kusan kashi 70 cikin 100 na tasoshin lantarki da China ta gina a shekarun nan, ta kona kusan rabin Kwal din duniya.

  3. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

    Jama'a Assalamu alaikum. Daga nan BBC Hausa Imam Saleh ke muku marhabun lale da zuwa wannan shafi da muke kawo muku labaran irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman Najeriya da Nijar.

    Sai ku gyara zama don kasancewa da mu a wannan rana ta Laraba da Hausawa ke yi wa kirari da Tabawa ranar samu.