Kungiyar IPOB ta kabilar ibo da ke neman ballewa daga Najeriya ta yi barazanar tilastawa mutane zaman gida na wata guda a yankin kudu maso gabashin Najeriya, idan ba a gurfanar da shugabanta, Nnamdi kanu a kotu ba a ranar 21 ga watan Oktoba.
Jami'in yada labarai na kungiyar, Emma Powerful, ya shaida haka ne a wannan Larabar ga manema labarai a birnin Akwa na jihar Anambra.
Ya ce majiyoyinsu na tabbatar musu da cewa ma'aikatar tsaron cikin gida ba za ta kawo Kanu kotu ba kamar yada aka tsara a ranar 21 ga watan Oktoba domin ci gaba da masa shari'a.
Ko a farkon watan Agusta sai da aka shiga zaman zullumi da rashin tabbas a yankin sakamakon irin wannan umarnin da kungiyar 'yan a-ware ta IPOB ta bai wa mazauna yankin da kada su fito wuraren ayyuka da harkokinsu na kasuwanci.
Hukumomin Najeriya na zargin kungiyar da kai hare-hare kan jami'an tsaro da cibiyoyinsu inda suke kashe jami'an tsaron da kona ofisoshinsu da kuma kwashe makamai. Hakan nan suna zargin kungiyar ta IPOB da kisan farar hula.
To amma kungiyar IPOB na cewa matakan da hukumomi ke dauka kan shugabanta da kuma yankin baki daya rashin adalci ne.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ma, a wani rahoto a baya-bayan nan, ta zargi jami'an tsaron Najeriya da yin amfani da karfi fiye da kima kan 'yan awaren da ma wadanda ba su ji ba su gani ba a yankin.
A cikin watan Yuni ne aka sake kamo Nnamdi Kanu bayan da ya gudu zuwa kasar waje bayan da aka bayar da belinsa a 2017.