An toshe layukan sadarwa a Sokoto

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da NIjar da sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh, Buhari Muhammad Fagge and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. ISIS ta kashe ƴan Taliban 45 yayin sabon harin da ta kai Afghanistan

    Mayaƙan ISIS

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar IS ta yi ikirarin kai hare-hare na farko a Afghanistan waɗanda aka kai wa Taliban tun bayan da ta karbi mulkin kasar a watan Agusta.

    Kungiyar reshen Afghanistan ta ce ta kai hare-haren guda bakwai a Jalalabad a ranakun Asabar da Lahadi, abun da ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun Taiban 45, da raunata wasu da dama.

    Wani shaida ya ce ya ga lokacin da ake kai 'yan Taliban da dama da suka jikkata asibiti.

    Birnin wanda ke gabashin Afghanistan ya kasance wata durka ta kungiyar ISIS.

  2. Wauta ce sake ciyo wa ƴan Najeriya bashi - Obasanjo

    Oluseagun Obasanjo

    Asalin hoton, Oluseagun Obasanjo

    Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya mayar da martani ga shirin shugaba Muhammadu Buhari na karbo sabbin rance, yana mai cewa yin aro don tara bashi ga ƴan gobe babban laifi ne.

    Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a gefen wani taro a Afirka ta Kudu, Obasanjo ya ce cin bashin da ake yi sannan ake kin biyan wanda ake bin kasar na iya zama gagarumar matsala ga gwamnacin da za su zo a gaba.

    Ko da yake ya ce cin bashi ba matsala bane, tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana cewa abin da zai iya zama matsala shine biyan bashin.

    ''Idan ana ciyo bashi don aiwatar da ayyukan da za su iya biyan kudinsu ne to wannan ba matsala bane, in kuwa don aiwatar da ayyukan al'amuran yau da kullum ne to wannan babbar wauta ce'' inji Obasanjo.

  3. Koriya Ta Arewa ta yi tofin Allah-tsine ga sabon kawancen Amurka da ƙasashen Turai

    Kim Jong Un

    Asalin hoton, Getty Images

    Koriya ta Arewa ta yi tofin Allah-tsine da sabuwar yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka, da Birtaniya da Ostiraliya, tana mai cewa hakan na iya haifar da "rigegeniyar mallakar makamin Nukiliya''

    Wani jami'in Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ya ce yarjejeniyar ta Aukus za ta '' kawo tarnaki a yankin Asiya da Pacific ''.

    Karkashin yarjejeniyar dai Amurka da Burtaniya za su ba Ostraliya kwangilar kera jiragen ruwa masu amfani da makamashin nukiliya.

    Ana kallon ta a matsayin wani yunkuri na dakile tasirin China a tekun Kudancin China da ake takaddama akai.

  4. Jam'iyyar shugaba Putin ta yi iƙirarin lashe zaɓen ƴan majalisa a Rasha

    Vladmir Putin

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Vladmir Putin

    Jam'iyya mai mulki a ƙasar Rasha ta yi iƙirarin samun nasara a zaɓen ƴan majalisar dokin ƙasar mai cike da taƙaddama.

    Gidan talabijin na ƙasar ya nuna wani babban jami'in jam'iyyar ta United Russia Party, Andrei Turchak yana taya dandazon magoya bayan jam'iyyar murna a birnin Moscow bisa abin da ya kira nasara ba tare da wani maguɗi ba.

    Mista Andrei din kenan ke cewa yaaaa ku jama'a, bari na yi muku murna kan nasarar da muka samu, yanzu na gama magana da shugaban jam'iyya, ba shi da lafiya, ba zai iya kasancewa damu a yau ba, amma ya ce na miƙa saƙon gaisuwarsa a gareku."

    An dai ta bayar da rahotanni na rashin bin tsari wurin zaɓen kuma tun kafin zaɓen ƴan adawar ƙasar suka yi ta koke kan cewa ba su ga alamun za a musu adalci ba.

  5. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    Bismillanku fa..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Bismillanku fa..

    Masu bibiyarmu ta wannan shafi Assalamu alaikum da fatan kun wayi gari lafiya.

    Imam Saleh ke muku maraba a wannan rana ta Litinin, inda muke fatan kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya musamman Najeriya da NIjar.

    Sai ku gyara zama, ko caja wayoyinku don kasancewa da mu.