Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da NIjar da sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Imam Saleh, Buhari Muhammad Fagge and Umaymah Sani Abdulmumin
Rufewa
Muna godiya da kasancewa da mu har zuwa wannan lokaci, sai dai masu iya magana kan ce laifin dadi karewa. Da haka zamu yi bakwana da ku.
Ku kasance da mu gobe da yardar Allah za mu dawo dauke da wasu labaran da rahotanni kai-tsaye kan irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa Bisallam.
'Sauyin yanayi zai tilasta wa mutum miliyan 216 yin ƙaura'
Bankin duniya ya ce matsalar sauyin yanayi za ta tilastawa mutum miliyan 216 yin ƙaura daga ƙasashensu zuwa shekarar 2050.
A rahoton da Bankin Duniya ya wallafa a ranar Litinin kan munin matsalar sauyin yanayi, ya ce mutum miliyan 86 za su yi ƙaura daga ƙasashen Afrika da ke kudu da sahara.
Rahoton ya ce idan har ba a ɗauki mataki ba, sauyin yanayi zai tilastawa mutum 216 daga nahiyoyin duniya shida ƙauracewa ƙasashensu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Sanwo-Olu ya sanya hannu kan dokar hana kiwon-sake a Legas
Asalin hoton, SANWO-OLU
Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanya hannu kan dokar hana kiwon-sake a fadin jihar.
Gwamnan ya bi takwarorinsa na kudancin Najeriya wajen sanya hannu a dokar.
Sanwo-Olu ya sanya hannu kan dokar kwanaki 11 bayan majalisar dokokin jihar ta amince da dokar sannan ya mikawa bangaren zartarwa domin mayar da shi doka.
Wannan doka ta janyo ce-ce-ku-ce a wasu jihohin Najeriya, da haifar da zarge-zarge kan abubuwan da ke biyo bayan kiwon-sake.
Tuni dama dai gwamnonin Rivers da Ondo da Enugu da Akwa Ibom suka sanya hannu kan dokar.
An hallaka matashi garin kwace masa waya a Kano
Rundunar
yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shuna Muhammad
Sulema da ake zargin wasu Matasa suka kashe tare da kwace masa waya.
Yan
sandan sun ce an kashe matashin ne a lokaicn da yake kan hanyarsa ta komawa
gida tare da iyalinsa matasan suka tasar masa a kan titiun Yahaya Gusau a dare
jiya.
A saurari rahoton Khalifa Shehu Dokaji kan lamarin
Bayanan sautiRahoto kan matashin da aka cakawa wuka a Kano
Harin sama ya hallaka kwamandan mayakan jihadi a Syria
Wani harin sama ya hallaka wani kwamandan wata kungiyar masu ikirarin jihadi a yankin arewa maso yammacin Syria.
Wata kungiya mai fafutukar kare hakkin dan Adam mai suna Syrian Observatory for Human Rights ce ta sanar da aukuwar lamarin, wanda ta ce kawancen da Amurka ke jagoranta ne ya kai harin ta hanyar amfani da wani jirgin sama marasa matuki.
Rokan da aka harba ya tarwatsa wata mota tsakanin biranen idlib da Binnish.
Sai dai kungiyar ta Syrian Observatory ba ta bayyana sunayen wadanda aka kashe a harin ba.
Amma wata majiyar ta ce sun fito ne daga kungiyar Huras al Din mai daukar makamai, wadda kuma ake alakanta wa da kungiyar al-Qaeda.
An yi cinikin dalar Amurka a kan naira 575 a Najeriya
Farashin dala ya kai tsakanin naira 572 zuwa 575 a sassan Najeriya a wannan Litinin din, kwana biyu bayan sanyawa shafin canji na Aboki FX takunkumi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a Abuja an yi cinikin dalar kan 574 wanda ya haura naira 570 da aka sayar da dalar a ranar Juma'ar da ta gabata.
A Legas kuma ana cinikin dalar kan naira 572, a Kano kuma 575.
Ana sayar da fam a kan naira 780 wanda ya haura farashin ranar Juma'a naira 770.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya zargi mai shafin AbokiFX da yi wa kasuwar canji zagon-kasa.
Emefiele, ya ce bankin ya dakatar da ayyukan AbokiFX saboda ayyukan da ya ke yi sun haramta.
Kungiyar Dattawan Arewa: Ba wanda zai tilasta wa ƴan arewacin Najeriya zaɓen ɗan kudu
Asalin hoton, Hakeem Baba Ahmed
Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya ta ce babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta zaɓen wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin ƙasar a zaben 2023.
Ƙungiyar ta mayar da martani ne ga matakin da ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya da wasu ƙungiyoyi suka ɗauka cewa lokaci ya yi da mulki zai koma bangarensu.
Kakakin kungiyar dattawan na arewa Dr Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa arewa tana da yawan masu zabe, don haka "yankin ba ya shakkar ko wace irin barazana."
A wani taron da gwamnonin kudancin Najeriya suka gudanar a watan Yuli sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na karɓa-karɓa daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban ƙasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin ƙasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci.
Kasancewar Najeriya mai bambancin kaɓilu da addinai, bisa al'ada jam'iyyun siyasa kan yanke shawarar yin karɓa-karɓa tsakanin yankin arewaci da kudanci. Kuma mutanen yankin kudanci na ganin yanzu lokacinsu ne, kasancewar yanzu shugaban da ke mulki ya fito ne daga yankin arewaci.
Rasha ta ce zaɓukanta na karshen mako su ne mafi sahihanci a ƙasar
Gwamnatin Rasha ta kafe cewa zabukan da aka gudanar na majalisar kasar a karshen wannan makon sun kasance mafi sahihanci da samar da zabi ga al'ummar kasar, kuma ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi cewa an tafka magudi.
Jam'iyyar United Russia wadda ke goyon bayan Shugaba Putin ta lashe kusan rabin kuri'un, wanda koma bayan kashi hudu cikin dari ke nan idan aka kwantanta da zaben shekaru hudun da su ka gabata.
Sai dai duk da koma bayan, ta iya lashe kashi biyu cikin uku na kujerun majalisar wakilan kasar.
Yayin da ake kusan kammala kidayar kuri'un, sakamakon zaben ya ba jam'iyyar 'yan gurguzu kusan kashi ashirin cikin dari na kuri'un.
Wani kakakin Tarayyar Turai ya ce ba a kyale kungiyoyin masu sa ido kan zaben yin aikinsu ba, kuma an rika muzguna wa 'yan adawa.
Likitoci sun bayyana dalilinsu na rashin janye yajin aikin da suke yi
Bayanan sautiSaurari rahoton Khalifa Shehu Dokaji kan wannan batu
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa a
Najeriya na ci gaba da yajin aiki, duk da umarnin da kotun harkokin masana’tu
ta basu na janyewa kwanaki hudu da suka gabata.,
A ranar Juma’ar karshen makon da ya gabata ne
kotun harkokin masana’tu ta Najeriya ta umarci kungiyar likitocin masu neman
kwarewa a kasar da su janye yajin aikin da suka shiga tun a ranar 2 ga watan
Agusta, shekarar da muke ciki su koma bakin aiki.
An toshe layukan sadarwa a Sokoto
Asalin hoton, Others
An toshe layukan sadarwa a jihar Sokoto fiye da mako biyu bayan an toshe hanyoyin sadarwar a jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar.
Gwamnatin jihar ta tabbatarwa BBC ta matakin, inda kakakin gwamnan jihar Muhammad Bello ya ce an toshe layukan ne a ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Wasu mutanen jihar sun ce idan an kira layukan MTN ba a kamawa, wasu kuma sun ce matsalar ta shafi har da masu amfani da layin Airtel.
Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.
Hukumomin jihohin sun ce an ɗauki matakin domin ƙoƙarin magance matsalolin ƴan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar.
Toshe layukan na zuwa bayan wasu ƴan bindiga sun abka garin Tangaza sun kashe mutane tare da satar abinci.
Dakarun Najeriya sun kashe 'yan bindiga 42 a yankin Shiroro da suka gudo daga Zamfara
Asalin hoton, Getty Images
Dakarun Najeriya da suka hadar da sojoji da kuma 'yan sanda sun kashe wasu 'yan bindiga a kauyen Alawa da ke yankin Shiroro a Jihar Neja.
Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa dakarun hadin gwiwar sun yi wa 'yan bindigar kwantan bauna ne, wadanda ke kokarin tserewa aikin da sojojin Najeriya ke yi a jihar Zamfara.Wata majiya ta kuma shaida wa jaridar cewa yayin wannan dauki ba dadi an kashe soja guda da kuma wasu da suka ji raunuka."Dakarun sun samu rahoton sirri na fitowar 'yan bindigar daga Zamfara sun nufin kauyen Alawa.
"Sun tsallake wasu wurare da sojoji suke bincike a cikin dazuka, amma mun samu damar far musu a Manganda. a kalla an kashe mutum 42 daga cikin su da yawa sun tsere da ciwuka a jikinsu.
"An kashe mana soja daya, an kuma dauki sauran mutanenmu da suka jikkata zuwa Asibitin Asma'u da ke Kagara.
"Mun kwace wasu makamai da babura da dai wasu abubuwa masu yawa, in ji wannan majiyar tasu.
Iyayen yaran kwalejin Yawuri da ke Jihar Kebbi sun ce 'ya'yansu sun cika kwana 93 a hannun 'yan bindiga
Bayanan sautiSaurari rahoton Buhari Muhammad Fagge
Iyayen
daliban kwalejin Tarayya ta Yawuri da ke Jihar Kebbi a arewacin Najeriya, sun
koka kan yadda ake ci gaba da garkuwa da yaransu ba tare da sanin wani
kwakkwaran yunkuri da hukumomi ke yi ba.
Korafin
na zuwa ne lokacin da yaran wadanda adadinsu yakai 91 suka cika kwana 93 a
hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
'Yan Boko Haram sun tarwatsa turakun wutar lantarki a Borno
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin
Najeriya sun ce ma’aikata sun koma bakin aikin gyaran manyan turakun wutar
lantarki, bayan da ‘yan Boko Haram reshen ISWAP suka tarwatsa manyan layukan
wutar ranar Asabar.
Hare-haren Boko Haram dai sun yi wa turakun wutar lantarkin
mummunar illa tsawon lokaci, abin da yasa birnin Maiduguri ke fama da rashin
wutar lantarki tsawon watanni, amma hukumomin jihar sun ce sun dukufa wajen
gyarasu. Ga karin bayanin da Zahraddeen Lawan ya aiko mana daga Abuja.
Hare-haren Boko Haram dai sun yi wa turakun wutar
lantarkin mummunar illa tsawon lokaci, abin da yasa birnin Maiduguri ke fama da
rashin wutar lantarki tsawon watanni, amma hukumomin jihar sun ce sun tukufa
wajen gyara su.
Wani mutum da ya bukaci a boye sunansa ya
shaida wa BBC cewa a ranar Asabar ne kungiyar Boko Haram reshen ISWAP suka
dasa wa manyan turakun hudu bam al’amarin da ya yi sanadiyar tarwatsewarsu, a
dai-dai kauyen Kuturu kusa da Auno cikin kaaramar hukumar Kondiga a jihar
Borno.
Sai dai mutum ya ce ya ga ma’aikata suna kokarin gyarasu.
Hon Babakura Abbajato, Kwamishinan yada labarai na
jihar Borno ta waya, ya tabbatar wa BBC cewa ana aikin gyaran manyan turakun
wutar.
Ya ce ba su da wutar lantarki a Maiduguri fiye da wata
shida, saboda haren-haren Boko Haram da suka yi sanadiyar tintsirewar turakun
wutar har guda takwas a baya, inda ya ce suna kan aikin gyaransu ne, sai ga shi
‘yan ISWAP sun sake lalata wasu.
Haka kuma Hon Babakura ya ce kamfanin mai na NNPC zai
samar da wata tashar wutar lantarki mai karfin mega watt 50 a cikin Maiduguri,
nan da wani lokaci karin akan kokarin da suke yi na dawo da hasken wutar
lanatarki a birnin Maiduguri da sauran sassan jihar.
Sabon Firaiministan Lebanon ya bayyana manufofinsa kan kasar
Asalin hoton, GN
Sabon firaministan Lebanon ya bayyana wa majalisar kasar alkiblar da gwamnatinsa ke son bi, kuma ana sa ran majalisar za ta kada kuri'ar amincewa da gwamnatin a zaman da za ta yi.
Najib Mikati ya yi alkawarin ci gaba da tattaunawa da asusun ba da da lamuni na duniya, IMF, yayin da yake kokarin shawo kan matsanancin matsalar tattalin arziki da kasar ke fama da shi.
Sai dai an fuskanci matsalar daukewar hasken lantarki a cikin zauren majalisar.
Irin wannan matsalar na cikin tarin matsalolin da suka janyo rugujewar tattalin arzikin Lebanon.
An dai shafe fiye da shekara guda babu gwamnati saboda jam'iyyun siyasar kasar sun rika rigima kan wadanda za su rike mukamai a sabuwar gwamnatin kasar.
An kama Rusesabagina da laifin ta'addanci
Wata kotu a Rwanda ta kama mutumin da aka nuna a fim din "Hotel Rwanda" a matsayin gwarzon da ya ceci rayukan mutane da yawa yayin kisan kiyashin da aka yi a Rwanda da laifin ta'addanci.
An samu Paul Rusesabagina da laifin daukar nauyin kungiyar 'yan tawaye wadanda suka kashe fararen hula a wani hari da aka kai a 2018.
Iyalansa na ikirarin an tursasa ne zuwa Rwanda.
Masoyansa da iyalan nasa sun kuma ce ba a gurfanar da shi ba a gaban kotu mai zaman kanta ba.
An fara sanya shi cikin masu kin gwamnati bayan da ya fara sukarta a baya.
Macron ya nemi afuwa kan wulakanta gwarazan Algeria
Asalin hoton, AFP
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nemi afuwa kan Harkis-r wanda ya yi yakin neman 'yancin Algeria daga Faransa.
Mista Macros a fusace ya ce Faransa ce ta kasa sauke nauyin da ke kanta na gwarazan Algeria.
Ya yi alkawarin za a rika tunawa da mutanen da kuma samar da dokar biyan diyayya a karshen wannan shekarar.
Za a samar da wata hukuma da za ta rika sauraren korafe-korafe daga 'yan uwan sojojin da suka tsira da iyalansu, wadanda suka tashi a wani sansanin zagaye da waya a cikin sansanonin Faransa.
Ɗan bindiga ya kashe mutane 6 a Rasha
Asalin hoton, Reuters
Wani dan bindiga ya kashe mutane shida a wata jami'a a Rasha.
Ƙarin wasu ashirin da hudu sun ji rauni yayin harin na jami'ar Perm, Urals.
Dalibai da malamai da dama sun buya a ginin jami'ar; yayin da aka ga wasu suna tsallake katanga.
'Yan sanda sun ce sun raunata tare da tsare maharin - abun da ya saba da rahotannin da aka bayar na cewa an kashe shi.
Maharin wanda aka ruwaito cewa dalibi ne ya bar sako a kafafen sada zumunta inda yake nuna tsantsar ra'ayinsa na son zubar da jini.
Ana nuna damuwa kan bullar masara 'mai guba' a Kano
Kwararru
a harkar abinci da lafiya a Najeriya sun fara bayyana damuwarsu dangane da
samin bullar wata masara da ake zargin akwai guba a cikinta, kuma ake sayar da
ita a Kano.
Masanan
dai na da da ra’ayin cewar duk da cewar ba a sami labarin wanda ya ci ko aka
siyarwa da irin wannan masara ba, amma akwai bukatar hukumomin jihar su fada
bin cike dan tabbtar da cewar ba ta fantsama cikin al’umma ba.
A
karshen makon da ya gabata ne, hukumar yaki da cin hanci da rashawa da
karbar korafe-korafe a Kano ta ce, ta kama mota biyu dauke da masarar a kasuwar Dawanau a Kano.
Ga dai rahoton Khalifa Shehu Dokaji:
Bayanan sautiRahoton Khalifa Dokaji kan masara mai guba
An kwashe ɗaruruwan mutanen da suka yada zango a ƙarƙashin gada a Amurka
Asalin hoton, Reuters
An kwashe ɗaruruwan mutanen da suka yada zango ƙarƙashin wata gada da ke iyakar Amurka da Mexico da niyyar shiga Amurka a matsayin ƴan ci rani inda aka mayar da su ƙasarsu ta Haiti.
Jami'an hukumar kula da shige da ficen Amurka ba su yi ƙarin haske kan lamarin ba, sai dai rahotanni na cewa an cika jirage uku taf da jama'a inda aka mayar da su Haiti.
Sai dai babban jami'in masu kula da iyakar Amurka Raul Ortiz cewa ya yi, "abin da muke sa rai shi ne mu kwashe ƴan ci rani sama da 3,000 daga ƙarƙashin gada zuwa wurin da za mu tantance su ko kuma wurin da za su hau jirgi nan da awa 24.
Sama da mutum 13,000 ne wadanda akasari ƴan Haiti suka taru a ƙarƙashin gada a birnin Del Rio da ke kan iyakar Amurka da Mexico.
Kamar a Najeriya, ƴan Burtaniya na kokawa kan ƙaruwar farashin gas
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren kasuwanci na Birtaniya Kwasi Kwarteng yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki a masana'antar makamashi game da hauhawar farashin gas.
Tuni wasu kananan kamfanonin makamashi biyar suka durkushe sanadiyyar kasa jurewa hauhawar kashi saba'in cikin ɗari a watan Agusta kawai.
Farashin da gwamnati ta sanya yana hana kamfanonin shiryawa da kwastomominsu.
Yanzu haka matsalar ta fara janyo karancin abinci.
Kamfanonin taki biyu da ke samar da kusan kashi sittin cikin dari na iskar carbon dioxide na Biritaniya sun rufe saboda tsadar iskar gas din.
Nick Allen, babban jami'in kungiyar masu sarrafa nama ta Burtaniya, ya ce nama na iya bacewa a manyan kantunan Burtaniya a cikin makonni biyu.