CBN na neman mai shafin canji na AbokifX ruwa a jallo

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. CAN ta dakatar da shugabanta na Gombe saboda taya Pantami murnar zama Farfesa

    Isah Pantami

    Asalin hoton, Isah Pantami

    Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta dakatar da shugabanta na jihar Gombe Sunday Congo, saboda wasikar da ya aika wa ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Internet na Najeriyar Isa Pantami, inda a ciki yake taya shi murnar zama Farfesa.

    A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga Satumba, da sakataren kungiyar Daramola Bade ya sanya wa hannu, ya sanar da dakatar da Mista Congo saboda zargin wuce gona da iri.

    Sanarwar ta ce an fitar da sanarwar ne ba tare da amincewar shugabancinta na kasa ba.

    “Biyo bayan sakin saƙon taya murna ga Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Internet Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, mun aiko maka wannan wasika don sanar da kai cewa abun da ka yi ya haifar da damuwa a tsakanin 'ya'yan wannan kungiya''.

    Ta ce “Wannan ba dai-dai bane, ka yi ne ba tare da wani izini ba', don haka ana umartarka da ka bar mukaminka nan take''.Inji wasikar.

  2. An yafe wa sojojin da suka kifar da gwamnatin Mali

    Mali

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Mali ta sanar da cewa an yafe wa sojojin da suka jagori juyin mulkin ƙasar na farko da na biyu da aka yi a bara.

    Hakan na nufin Colonel Assimi Goita da sauran sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Boubacar Keita da kuma Firaiminista Bah Ndaw ba za su fuskanci wata tuhuma ba.

    An amince da wannan matakin ne bayan mafi rinjaye daga cikin ƴan majalisar riƙo na ƙasar sun amince da wannan mataki. Kanal Goita dai ya ce zai yi biyayya ga wa'adin da aka bayar na 2022 a gudanar da zaɓe irin na dimokraɗiyya a ƙasar.

  3. Marabanku..

    Kosai

    Asalin hoton, Kosai

    Bayanan hoto, Bismillanku ga kosai da dumu-duminsa fa..

    Jama'a barkanmu da safiya da fatan kun wayi gari lafiya.

    Imam Saleh ke muku barka da wannan rana ta Jumma'a daga nan sashen Huasa na BBC.

    Kamar yadda aka saba yau ma za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya, don haka sai ku kasance da mu.