Haramta amfani da Twitter ba shi da muhalli a dimokuraɗiyya - Amurka

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Macron ya ce marin da aka yi masa ba zai hana shi shiga mutane ba

    Macron

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce marin da aka yi masa ranar Talata, ba zai sa ya daina zuwa kusa da al'ummar ƙasar ba, a duk lokacin da wata mu'amalar kai tsaye ta taso.

    Matakin na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa masu bincike sun gano makamai da kwafin wani littafin da Hitler ya rubuta a gidan ɗaya daga cikin mutum biyu da ake zargi da marin shugaban Faransar.

    Cikin makaman da aka gano a gidan mutumin da ya naɗi marin da aka yi wa Macron, har da takobi da adda da wata bindiga da ya mallaka ta halartacciyar hanya.

  2. Shugaba Biden na halartar taron G7 a Burtaniya

    Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Joe Biden ya sha alwashin sake gina kawance da kasashen duniya da ke mutunta mulkin dimokradiyya da yakar gwamnatocin kama-karya a ziyararsa ta farko zuwa wata kasar waje tun rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka.

    Jim kadan bayan isarsa Burtaniya domin halartar taron kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki, Shugaba Biden ya fada wa dakarun Amurka da ke cike da farin ciki cewa wadanda suke tunanin zamanin dimokradiyya ya shude, sun yi kuskure.

    Shugaban ya isa yankin Cornwall amma kafin ya isa yankin sai da ya soma kai wa sansanin sojin Amurka na Mildenhall da ke Suffolk ziyara, inda ya gabatar da jawabai da zayyana irin kalubalen da ke gabansa.

    Ya yi alkwarin daukar tsatstsauran mataki tare da takwaransa na Rasha Vladmir Putin yayin tattaunawar makon gobe a Switzerland.

  3. Buhari zai kai ziyara Legas

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    An tura jami'an tsaro da dama Legas gabanin ziyarar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari inda zai ƙaddamar da wasu ayyukan gwamnati a yau Alhamis

    Akwai fargaba a faɗin ƙasar yayin da ake sa ran gudanar da zanga-zanga ranar 12 ga watan Yuni a ƙasar wato ranar Demokuraɗiyya.

    Masu fafutuka a Legas da sauran manyan birane a ƙasar na fatan yin zanga-zanga don nuna ɓacin ransu dangane da matsalar tsaro da ke ta'azzara da barazana ga ƴancin tofa albarkacin baki musamman yanzu da aka haramta Twitter.

    Jaridar Punch a Najeriyar ta ruwaito cewa tawagar Shugaban ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na ƴan sanda Usman Baba ta riga ta isa Legas.

    Ziyara ta ƙarshe da Buhari ya kai Legas a watan Afrilun 2019 ne.

  4. An kara gabatar da karin tuhume-tuhume kan Aung San Suu Kyi

    Aung San Suu Kyi

    Asalin hoton, Getty Images

    An kara gabatar da karin tuhume-tuhume kan tsohuwar shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi wadda sojoji suka hambarar da gwamnatinta cikin watan Fabrairu.

    Kafofin yada labarai na gwamnati sun ce a yanzu tsohuwar shugabar tana fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci da ke da alaka da wata gidauniyar agaji da ta kafa domin tunawa da mahaifiyarta.

    An kai samame ofisoshin gidauniyar jim kadan bayan sojoji sun karbe mulki.

    Dama Aung San Suu Kyi na fuskantar tuhume-tuhume da dama har da tunzura jama'a da saba dokokin kasar.

  5. Bautar da ƙananan yara na ƙaruwa a faɗin duniya- MDD

    Child Labour

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya na gargadin cewa matsalar nan ta bautar da kananan yara na karuwa matuka a fadin duniya.

    Wani sabon rahoto ya ce adadin yaran da ake tilastawa yin aikatau ya kai miliyan dari da sittin.

    Asusun kula da kanana yaran na Majalisar Dinkin Duniya ya ce fiye da rabin yaran yan tsakanin shekara biyar zuwa 11 ne.

    Babbar daraktar UNICEF ta ce rufe makarantu da dokokin kulle da kuma rasa ayyukan yi da iyayensu suka yi ya shafi yaran

  6. Buɗewa

    Barkanku da safiyar Alhamis kuma barkanku da kasancewa da mu a wannan shafin wanda ke kawo maku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da ma sauran ƙasashen Afrika.

    Shayi mai Na'a Na'a