Macron ya ce marin da aka yi masa ba zai hana shi shiga mutane ba
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce marin da aka yi masa ranar Talata, ba zai sa ya daina zuwa kusa da al'ummar ƙasar ba, a duk lokacin da wata mu'amalar kai tsaye ta taso.
Matakin na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa masu bincike sun gano makamai da kwafin wani littafin da Hitler ya rubuta a gidan ɗaya daga cikin mutum biyu da ake zargi da marin shugaban Faransar.
Cikin makaman da aka gano a gidan mutumin da ya naɗi marin da aka yi wa Macron, har da takobi da adda da wata bindiga da ya mallaka ta halartacciyar hanya.