Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Haramta amfani da Twitter ba shi da muhalli a dimokuraɗiyya - Amurka

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafin.

    Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya

  2. Haramta amfani da Twitter ba shi da muhalli a dimokuraɗiyya - Amurka

    Amurka ta sake yin Allah-wadai da matakin gwamnatin Najeriya na toshe dandalin sada zumunta na Twitter a ƙasar, tana mai cewa toshe shafukan zumunta "ba shi da muhalli a dimokuraɗiyya".

    Cikin wata sanarwa a yau Alhamis, Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken ya yi kira ga Najeriya da ta tabbatar da 'yancin faɗar ra'ayi.

    "Amurka na Allahh-wadai da haramta dandalin Twitter da gwamnatin Najeriya ta yi da kuma barazanar kama masu amfani da shafin," a cewar wani ɓangare na sanarwar.

    "Hana 'yan Najeriya damar bayar da rahoto da taro da kuma yaɗa bayanai da ra'ayoyi ba shi da muhalli a dimokuraɗiyya. 'Yancin faɗar ra'ayi a fili ko a dandalin sada zumunta na cikin turakun kafuwar dimokuraɗiyya.

    "Muna goyon bayan Najeriya game da yunƙurinta na haɗa kan ƙasa da samar da zaman lafiya. A matsayinmu na ƙawarta, muna kira ga gwamnati da ta mutunta 'yancin 'yan ƙasarta ta hanyar janye wannan haramcin."

    Kazalika Amurka ta nuna damuwa game da umarnin da hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta NBC ta bai wa kafofin cewa su goge shafukansu na Twitter.

    Sai dai gwamnatin Najeriya ta kafe cewa Twitter "yana raba kan 'yan ƙasar" kuma ta sharɗanta wa kamfanin cewa sai ya yi rajista a matsayin kamfanin kasuwanci a Najeriya kafin ta ɗage haramcin.

  3. Kenya ta janye haramcin saukar jirage daga Somalia

    Kenya ta dage haramcin saukar jiragen sama daga Somalia wata ɗaya bayan ta dakatar da sauka da kuma zuwan jiragen a ƙasarta.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Kenya ta ce tana fatan matakin zai zama sanadiyyar dawo da cikakkiyar hulɗar difilomasiyya a tsakanin ƙasashen biyu.

    Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce dukkan dokokin kariya daga cutar korona za su shafi matafiyan da suka fito daga Somalia.

    Kenya ta haramta wa jirage daga Somalia sauka a tsakiyar watan Mayu ba tare da bayar da wani dalili ba.

    Rikici tsakanin ƙasashen ya kwna biyu sakamakon taƙaddama kan iyaka, batun da yanzu haka yake gaban Kotun Duniya.

  4. Kotu ta ɗaure mutumin da ya gaura wa shugaban Faransa mari

    Kotu a Faransa ta yanke wa mutumin nan da ya sheƙe Shugaban Ƙasa Emmanuel Macron na Faransa da mari hukuncin ɗaurin wata huɗu a gidan yari.

    Damien Tarel ya faɗa wa kotun cewa abin da ya aikata saurin hannu ne kawai, amma mai shigar da ƙarar ya ce "da gangan ya aikata tayar da fitina".

    An faɗa wa kotun cewa Tarel na da tsattsauran ra'ayin siyasa ko kuma na riƙau sannan kuma yana da alaƙa da ƙungiyar nan ta masu yaluwar riga wato yellow-vest movement.

    Mista Macron ya ce bai kamata a ɗauki marin da wasa ba amma kuma kar a tsaurara, yana mai cewa hakan ba zai hana shi ci gaba da zuwa kusa da jama'a ba.

    Lamarin ya faru ne ranar Talata, inda mutumin wanda ke cikin waɗanda suka taru a bayan wani ƙarfe ya tsinke Macron da mari jim kaɗan bayan ya bar wani otel a garin Tain-l'Hermitage da ke kudancin Faransa.

  5. 'Yan sandan Najeriya sun kama 'mai haɗa wa 'yan IPOB layu da guraye'

    'Yan sanda a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun kama wani mutum da ake zargi da haɗa wa 'yan ƙungiyar IPOB laya da guraye.

    Uzoamaka Ugoanyanwu mai shekara 40 yana haɗa wa mayaƙan Eastern Security Network (ESN) layu, wato ɓangaren soja na ƙungiyar IPOB mai fafutikar ɓallewa daga Najeriya, a cewar Kwamishinan 'yan Sandan Imo Abutu Yaro.

    Cikin wata sanarwa da SP Bala Alkana ya fitar a madadinsa, CP Yaro ya ce jami'ansu sun kama wasu mutum tara da ake zargi da kai hari kan gidan Gwamnan Jihar Hope Uzodinma.

    Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama su ne sakamakon wani bincike mai tsanani da jami'an rundunar na musamman suka yi sannan ya shawarci miyagun da suke riƙe da makaman da suka ɗiba daga wajen 'yan sanda da su mayar da su da kansu.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa 'yan sanda tare da taimakon sojoji sun daƙile wani hari kan hedikwatar 'yan sanda a Imo ranar Lahadi sannan suka kashe mayaƙan ESN biyar.

    Jihohin kudu maso gabas a Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan, waɗanda hukumomi ke cewa 'yan ƙungiyar IPOB ne masu son kafa ƙasar Biafra.

  6. Kenya: Tsofaffin matan da masu gadi suka yi wa fyade a gona sun fadi halin da suka shiga

    Wasu mata biyu wadanda suka ce masu gadi sun yi musu fyade a gonar Kakuzi da ke kasar Kenya sun bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki.

    Sun yi zargin ne a daidai lokacin da kamfanin da ke da gonar ya ce zai shigar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasar kara a kotu kan abin da ya kira zarge-zargen karya da suka yi masa game da cin zarafi.

    Masu suka sun ce kamfanin da ke kula da Kakuzi zai shigar da karar ce da zummar sake samun kwantaragin da wani babban shago na Birtaniya ya daina ba ta saboda zarge-zargen cin zarafin mata.

    Kamfanin ya shaida wa BBC cewa dole a gudanar da bincike kan sabbin zarge-zargen kuma ba zai amince da masu aikata ba daidai ba.

    Mudhikwa Musau, mai shekara 88, tanazaune a wani kauye da ba shi da nisa daga da gonar ta Kakuzi da ke tsakiyar Kenya.

    Ta ce a shekarar 2009 masu gadin gonar sun yi mata fyade da karfin tsiya. Da take jawabi da harshensu na Kamba, ta bayyana yadda ta yi zargi an yi mata fyaden.

    "Ya kama ni kamar haka kuma ya kama ni a nan. An zagaya da ni. Ya tashi tsaye ya tsaya a kaina. Ya taka muyana. Ya rike muyana sanna ya juya si. Ya rufe mini baki a yayin da nake ihu."

    Mudhikwa Musau ta ce ya je wurin 'yan sanda ta kai kara kan abin da aka yi mata, sai dai ba ta sake jin an ce komai a kan batun ba.

    Da suke mayar da martani kan batun, masu gonar Kakuzi sun fito da wasu takardun kotu da ke nuna cewa an hukunta daya daga cikin ma'aikatansu kan lamarin amma an wanke shi daga zargin yi mata fyade.

    Kazalika ita ma Marium Wanja mai shekara sittin da biyar ta bayyana yadda aka yi mata fyade a gonar. Ta ce ta haifi 'ya'ya biyu sakamakon lalata da masu gadin gonar Kakuzi suka yi da ita a shekarun 1990.

  7. Kotu ta ɗaure jagoran hamayayya a Guinea

    Wata kotu a Guinea ta yanke wa wani dan hammaya mai fafituka hukuncin daurin shekara uku a gidan yari saboda shirya zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwmnatin shugaba Alpha Conde.

    Kotun ta samu Omar Sylla da aka fi sani da Fonike Mengue da laifin taro ba tare da izinin hukuma ba da kuma yaɗa labaran ƙarya.

    A shekarar da gabata ne shugaba Conde mai shekara 82 a wancan lokacin ya zartar da dokokin da za su tsawaita wa’adin mulkn shugaban kasa daga wa'adi biyu.

    Zaɓensa da aka sake yi mai cike da cecekuce ya haifar da zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar gwmman mutane.

  8. Wata mace ta farfaɗo daga dogon suma na wata 10

    Wata mata a Italiya ta farka daga dogon suma da ta yi bayan wata 10.

    Jaridar La Nazione ta ruwaito cewa Cristina Rosi mai shekara 37 na da cikin wata bakwai a lokacin da ta fuskanci bugun zuciya a watan Yulin 2020.

    An yi mata tiyata inda aka ciro 'yarta mai suna Caterina sannan aka ƙyale ta a sume ɗauke da matsalar ƙwaƙwalwa.

    Yanzu haka ta farka har ma ta faɗi kalma ta farko, "Mamma", a cewar mijinta.

    "Ba mu yi tsammani ba, mun ji daɗi matuƙa bayan irin wahalar da aka sha," in ji Gabriele Succi.

    A watan Afrilu aka mayar da Ms Rosi wani asibiti a ƙasar Austria domin samun kulawa ta musamman. Mijinta da mahaifiyarta suna kusa da ita a lokacin da ta farka.

  9. Gwamnatin Najeriya ta bayyana Litinin a matsayin ranar hutu

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin, 14 ga watan Yunin 2021 a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya.

    Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola wanda ya bayyana hakan, ya shawarci 'yan ƙasar da su bai wa gwamnatin jam'iyyar APC haɗin kai "domin samar da dunƙulalliyar ƙasa kuma mai arziki".

    Ana gudanar da bikin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya duk ranar 12 ga watan Yuni, sai dai za a gudanar hutun ranar ne a Litinin saboda ta faɗo ranar Asabar.

    Wannan ne karo na huɗu da za a gudanar da bikin a ranar 12 ga Yuni tun bayan da Shugaba Muhammdu Buhari ya sanar da sauya ranar daga 31 ga Mayu a Yunin 2018.

    Ministan ya nemi 'yan ƙasa da su guje wa duk wani abin da zai jawo wa haɗin kan ƙasa tangarɗa.

  10. Gwamnatin Syria ta kashe shugabannin 'yan tawaye a hari ta sama

    Rahotanni sun ce wani harin makami mai linzami da gwamnatin Syria ta kai ya halaka aƙalla mutum takwas a lardin Idlib da ke karkashn ikon 'yan tawaye.

    Wata ƙungiyar kare hakin dan Adam mai sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Syriar ta ce wasu manyan shugabanin wata kungiya da ke ikirari jihadi biyu na cikin wadanda suka rasa rayukansu.

    Haka kuma an samu farar hula a cikin wadanda aka kashe.

    Sau da yawa ana saba wa yajejeniyar tsagaita wuta sai dai wannan harin shi ne mafi muni cikin shekara sama da ɗaya.

  11. Minti Ɗaya Da BBC Na Rana

  12. Mutum 11 sun mutu a rushewar gini a Indiya

    Masu aikin ceto a birnin Mumbai na Indiya na ci gaba da tona baraguzan wani gini da ya ruguje da fatan samun wasu a raye.

    Mutane goma sha daya ne, galibinsu kananan yara aka tabbatar da sun rasu.

    An ba da umarnin gudanar da bincike amma wani minista ya ce akwai yiwuwar ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya ne ya janyo rishewar ginin.

    Faduwar gini abu ne da aka saba gani a Indiya musamman a wannan yanayin na ruwan sama.

    Jami'ai sun ce sun fitar da mutane daga tsofaffin gine-ginen da ke kusa da inda ginin ya faɗi saboda akwai yiwuwar za a ci gaba da samun mamakon ruwan saman.

    Haka kuma, ruwan na ambaliya a wasu yankunan garin.

    Ƴan sanda sun ce kawo yanzu sun zaƙulo mutum 18 daga baraguzan kuma mutum bakawai ne a cikinsu kawai suka rayu.

  13. Ƴan ƙabilar Ibo ba za su iya ɓallewa daga Najeriya ba- Rochas Okorocha

    Tsohon gwamnan jihar Imo kuma ɗan majalisar dattijai a Najeriya, Sanata Rochas Okorocha ya ce akwai buƙatar gwamnati ta yi amfani da sarakuna wajen magance rikicin `yan a-ware a shiyyar kudu maso gabashin ƙasar.

    Sanatan wanda ya fito daga yankin da ke fama da rikicin na ƴan aware, ya ce jagororin al'ummar Igbo ba sa goyon bayan abin da ke faruwa a yankin yanzu, ko da yake, ba sa iya fitowa su soki lamarin, saboda gudun fushin matasansu.

    "Yawancin mutane suna da tsoro, ka fada kuma gobe a je a samu yaronka a kashe". in ji shi.

    Kalli bidiyon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da shi:

  14. Bidiyon Buhari yana ƙaddamar da titin jirgin ƙasa a Legas

    Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke ƙaddamar da titin jirgin ƙasa na Legas zuwa Ibadan a unguwar Ebute Metta a jihar Legas.

  15. Najeriya ta tilasta wa shafukan sada zumunta yin rajista a ƙasar

    Hukumar NBC mai kula da kafofin yaɗa labarai a Najeriya ta buƙaci duka shafukan sada zumunta da masu yaɗa labarai ta intanet da ke aiki a Najeriya da su fara neman lasisin watsa labarai.

    Shugaban hukumar Armstrong Idachaba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jaridun ƙasar ranar Alhamis.

    Wannan ya biyo bayan sanarwar gwamnatin Najeriya mai cewa shafin Twitter da sauran shafukan sada zumunta su yi rajista a matsayinsu na kamfanonin Najeriya don samun damar yin aiki a ƙasar.

    Sanarwar ta ce duk kafar yada labarai mai aiki da intanet da ba ta nemi lasisi ba, ta kauce wa ƙa'ida.

    Ministan yaɗa labarai a Najeriyar Mista Lai Mohammed ce dole ne shafuka kamar Facebook da Netflix su yi rajista, kuma sai an ba su lasisin aiki a ƙasar.

    Mista Lai ya ce baya ga haka, dole ne su amince da daina amfani da shafukan wajen ayyukan da ka iya yi wa ƙasar barazana.

    Wasu na ganin wannan matakin a matsayin shirin gwmnatin na sa ido kan amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya.

    Haramta amfani da Twitter ya janyo fushi bisa abin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan dam suka ce wani yunƙuri na hana ƴan Najeriya amfani da ƴancinsu tofa albarkacin baki.

  16. An zargi gwamnatin Ethiopia da kashe matashi mai shekara 17

    Ana zargin gwamnatin Ethiopia da kashe wani matashi ba a bisa ƙa'ida ba, a cewar wani rahoton ƙungiyar Human Rights Watch.

    An kashe matashin mai shekara 17 Amanuel Wondimu Kebede a yankin Oromia na Ethiopia a watan Mayun da ya wuce, kuma yana cikin fararen hula da ake tunanin sun mutu tun da faɗa ya ɓarke a yankin shekaru 3 da suka gabata.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna lokutan ƙarshe na Amanuel Wondimu. An ɗaure masa hannuwa a bayansa, da bindiga a rataye a wuyansa kuma fuskarsa duk jini yayin da yake magana a gaban kyamara.

    Human Rights Watch ta yi zargin cewa ɗan lokaci ƙanƙani bayan ɗaukar bidiyon ne jami'an tsaron Ethiopia suka bai wa matashin umarnin kauda kansa sannan suka harbe shi sau biyu a gaban shaidu a ƙalla huɗu.

    A lokacin gwamnati ta ce Amanuel ya harbi wani mutum ne kuma ya yi masa rauni, sannan an ce yana da hannu a kisan wani ɗan jarida.

    Sai dai an musanta wannan batu inda wata shaida mai ƙarfi ta ce ɗalibi ne mai ƙwazo kuma yan yi wa cocin unguwarsa huduma.

    Rikin na shekarar uku tsakanin gwamnati da ƙungiyar ƴan aware ta Oromo Liberation Army ta yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun yi zargin jami'an tsaro da cin zarafin da kisan jama'a.

  17. Dakarun Isra'ila sun kashe jami'an tsaron Falasɗinu a yayin wani samame

    Dakarun Isra'ila sun kashe jami'an tsaron Falasɗinu biyu lokacin wani sammae a gaɓar Yamma da Kogin Jordan, a cewar hukumomin Falasɗin.

    Dakarun Isra'ilar sun shiga garin Jenin ne da Falasɗinawa ke iko da shi don kama wasu da ake zargin ƴan bindiga ne, kuma an kashe ɗaya daga cikinsu a ba-ta-kashi kusa da hedikwatar hukumar leƙen asirin Falasɗinu, acewar rahotanni.

    Isra'ila da hukumomin Falasɗinu na haɗa kai kan batutuwan tsaro kuma dakarun Falasɗinu ba su cika tunkarar dakarun Isra'ila ba.

    An ji wa wani jami'in tsaron rauni a ba-ta-kashin.

  18. Shugaba Buhari ya isa Legas don ƙaddamar da wasu ayyuka

    Shugaba Buhari ya isa Legas inda zai ƙaddamar da titin jirgin ƙasa na Legas zuwa Ibadan.

    Wannan titin wani bangare ne na aikin gwamnatin na Railway Modernization Project na sabunta ɓangaren jirgin ƙasa a ƙasar.

    Tare da shugaban akwai gwamnan jihar Legas Babjide Sanwo-Olu da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da MInistan Ayyuka, Babatunde Raji Fashola da sauran manyan ƴan siyasa a ƙasar.

    Shugaban zai fara isa unguwar Ebute Metta inda tashar jirgin take sannan ya zarce tashar jirgin ruwa ta Apapa don ƙaddamar da wani aiki na Integrated National Security and Waterways Protection Infrastructure ko Deep Blue Project.

  19. Firai ministan Mali zai kafa sabuwar gwamnati ran 13 ga Yuni

    Firai ministan farar hula a Mali Choguel Kokalla Maiga ya ce zai kafa sabuwar gwamnati ran 13 ga Yuni bayan tattaunawa da jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin fararen hula.

    Firai ministan ya yi magana da tashar rediyo ta RFI ran 8 ga watan Yuni bayan tattaunawa da wata tawaga daga Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS da ke ziayara a ƙasar.

    Ana sa rai sabbin hukumomin Mali masu sa ido kan kafa gwamnatin za su shirya zaɓe zuwa Fabrairun 2022 yayin da suke fatan mayar da mulkin ƙasar na farar hula.

    Maiga ya yi alƙawarin cewa cikin mako shidda, za a miƙa tsarin zaɓen da jadawalin ga Majalisar Kafa Sabuwar Gwamnatin.

  20. Lauyoyin Navalny a Rasha za su ɗaukaka kara kan hana shi tafiya

    Lauyoyin jagoran yan adawa a Rasha Aleei Navalny sun ce za su daukaka kara kan hukuncin kotun da ya haramta masa yin tafiyarsa ta siyasa.

    Alkalai a Rasha sun bayyana kungiyoyin da ke da alaka da Mista Navalny a matsayin masu tsatstsauran ra'ayi.

    Wakilin BBC ya ce yayin da ya rage watanni uku a fara zabe, da alama hana yan hamayya shiga zaben shi ne abin da shugaban kasar ya sa a gaba.

    Tuni Burtaniya da Amurka suka yi tur da hukuncin kotun.