Bournemouth 1-0 Man United, Shekara 29 kenan rabon da haka ta faru!
Rabon da United ta yi irin wannan rashin katabus tun a shekarar 1990. Rashin nasararta ya fi nasararta yawa a Premier ta bana - Hudu kawai ta ci cikin 11
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sharhi kai-tsaye kan wasannin Premier mako na 11
Umar Mikail
Rabon da United ta yi irin wannan rashin katabus tun a shekarar 1990. Rashin nasararta ya fi nasararta yawa a Premier ta bana - Hudu kawai ta ci cikin 11
An tashi kuma Manchester United ta sha kashi a hannun Bournemouth, sun yi rashin nasara a hudu daga cikin wasa 11 da suka buga a kakar bana.
Nathan Ake shi ne dan bayan da ya hana United ganin raga a wannan wasa mai cike da kujiba-kujiba. Dan wasan shi ne bangon Bournemouth.
Wilson na Bournemouth ya karbi kati saboda faduwar karya da ya yi a tsakiyar fili
Minti uku kacal aka kara
Minti hudu ya rage a tashi daga wasan. Ba mu san inda Solkjaer zai sa kansa ba idan aka tashi haka
L. Cook ya canji Harry Wilson
Kiris ya hana Greenwood ya jefa kwallo amma ta daki turke ta fito
Greenwood ya karbi Daniel James yayin da Brandon Williams ya sauya Aaron Wan-Bissaka.
Ashley Young ya bugo kwana amma 'yan bayan Bournemouth sun tsige ta ba tare da wani hadari ba.
Minti 78 da fara wannan wasa amma har yanzu United ba ta samu nasarar zare kwallon ta ba. Ba ta nuna wata alamar yin hakan ma domin har yanzu rawar da take takawa ba wata mai armashi ba ce.
Kiris ya hana Harry Wilson ya kara kwallo ta biyu amma De Gea ya hana ta shiga
Kusan shekara daya kenan Jesse Lingard bai zira kwallo a gasar Firimiya ba, wannan ne lokacin da ya kamata ya nuna kansa, bayan ya karbi Andreas Pereira
Bournemouth ba ta amfana da bugun tazarar da ta samu ba.
Ashley Young ne ya ture Adam Smith a bakin ragar United, shi kuma lafari ya bayar da bugun tazara a wuri mai hadarin gaske. Sai dai Bournemouth ba ta amfana daga damar ba.
An bai wa Lindelöf katin gargadi bayan taka Harry Wilson
Manchester United ba su da tabbas ko za su iya sauya wasan a minti daya kamar yadda suka yi a wasansu da Chelsea.
An bai wa Steve Cook katin gargardi bayan fitar da Rashford da ya yi......
Jesse Lingard na motsa jiki zai shigo wasan......
Harin farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci yayin da Ryan Fraser na Bournemouth ya dada wa De Gea kwallo amma mai tsaron ragar na United ya kama ta ba tare da wani ji ba.
Yanzu haka Man United ce ke fafatawa da Bournemouth, inda Bournemouth din ta cilla wa United kwallo a raga a minti na 45 ta kafar Josh King.
Barkanmu da saduwa a wannan shafin da zai kawo maku rahotanni kai-tsaye na Premier da sauran wasannin lig lig na kasashen Turai a yau Asabar.
Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge ne ke maku barka da rana