GOAL, Aston Villa 1-1 Liverpool
Andrew Robertson ya farke wa Liverpool kwallonta, wasa ya dawo danye jagab
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sharhi kai-tsaye kan wasannin Premier mako na 11
Umar Mikail
Andrew Robertson ya farke wa Liverpool kwallonta, wasa ya dawo danye jagab
Kyle Walker ya ci wa City kwallo ta biyu, shewa ta barke a Etihad
Kiris ya hana a kara wa Liverpool kwallo, damar da Aston Villa ke samu tana amfani da ita kuma gaskiya babu alamun Liverpool za ta farke nan kusa
Raul Jimenez ne ya farke wa Wolves kwallonta
Anya kuwa Arsenal za ta sha a wasannan?
Karfa garin neman gira a rasa ido, domin Liverpool ta fito kwanta da kwarkwatarta neman farkiya
Fabián Balbuena ya farke wa West Ham daya...... anya kuwa wasan ba zai rikice ba?
Leandro Trossard ne ya ci kwallon
Man city ta farke kwallonta - Sergio Aguero ya dawo da wasan danye.
Akalla wannan tasawirar za ta fada maku abin da kuke bukatar sani game da yadda wasan ke guda na, 'yan wasan Man City baki dayansu suna cikin bangaren Southampton ban da biyu kacal.
Ana fafatawa
Levente fa sun farfado kuma har sun farke kwallon da Messi ya ziera masu a abugun finareti
Tim Cahill tsohon dan wasan Everton ya ce:
"Gasar Premier ta dauki zafi duk idanu na kan wasannin LIverpool da kuma na Manchester City, wanda sakamakon wasannin zai iya sauyawa a kowanne lokaci."
Mo Salah fa ya bata a wasan, shot biyu kawai ya iya bugawa raga ya zuwa yanzu, kuma kasa da sau 20 kacal ya taba kwallon
Jonjo Shelvey ya kara kwallo ta uku, da alama West Ham ta san inda ta dosa yanzu. Newcastle kuwa baki har kunne
Sadio Mane ya dada kwallo zuwa ragar Aston Villa sai dai gola Heaton ya cafke kayarsa, saboda haka babu wani hadari
Pep Guardiola ya sako Gabriel Jesus din kuwa, inda ya canji David Silva duka dai a kokarinsa na farke alakakai din da dakarun Southampton suka zira masa.
Liverpool da Man City da Burnley da West Ham dukkaninsu nema suke su farke kwallayen da aka zira masu a raga.
Lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci Gabriel Jesus yana motsa jikji a gefen fili, saboda haka babu mamaki a fdawo da shi cikin wasan.
Man City ta buga shot har 13 a minti 45 na farko, abin da ke nuna cewa lallai ta kagu ta farke wannan kwallo.
Ita kuwa Southampton ai sai inda karfinta ya kare domin dai tana so ne ta farfado daga abin kunyar da ya faru a makon jiya na 0-9 da Leicester ta dura mata.
Alkalin wasa Jonathan Moss ya ankara da abin da Sadio Mane ya aikata....
Sadio Mane ya yi wanwar a cikin yadi na 18 bayan matsi da ya sha daga dan wasa Frederic Guilbert.
Tuni aka ba shi katin gargadi kuma na jan kunnen kar ya bata wa alkalin wasa aikinsa.
An hutun rabin lokaci
Da alamar Brighton na ci gaba da dandana kudarta
To wane ne in ba Messi ba!
Barcelona na jan ragamar wasa tsakaninta da Levente a filin wasa na Estadio Ciudad de Valencia.
An tafi hutun rabin lokaci
Har yanzu Newcastle na kan gaba a wasan, an kammala zagaye na farko