Durban July: Hotunan sukuwar dawaki mafi ƙayatarwa ta Afirka ta Kudu

    • Marubuci, Joseph Winter
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Ana sa ran dubun dubatar 'yan Afirka ta Kudu za su kama hanyar birnin Durban a ranakun ƙarshen makon nan saboda bikin shekara na Durban July, inda ake gudanar da tseren dawaki mafi girma.

Sai dai da yawa daga cikinsu za su je ne saboda kwalliya da kuma tallata ƙayan ƙawa.

An baje kolin kayayyakin ƙawa don nuna baiwar da masu ƙirƙira na ƙasar ke da ita.

An zaƙu a ga bikin na wannan shekara saboda shekara biyu ke nan ana gudanar da shi a ɓoye saboda annobar korona da ta addabi duniya.

Daga cikin fitattun da ke halartar bikin akwai tauraruwar fim Jessica Nkosi.

Tabbas akwai sauran jama'a da za su kalli tseren dawakin.

Bikin har wa yau, wata dama ce ta tayar da komaɗar tattalin arzikin ƙasar, wanda ya samu naƙasu sakamakon ambaliyar ruwa a kusa Durban a watan Afrilu, da kuma tarzomar da aka yi shekarar da ta wuce bayan an ɗaure tsohon Shugaban Ƙasa Jacob Zuma.

Amma dai ga mafi yawan mutane, nuna kwalliya da tallata kayan ƙawa ne a gabansu.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.