Atiku Abubakar: Mukamin shugaban kasa ba ya bukatar mai jan-kafa wajen zaben mataimakinsa

An wallafa

Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ofishin shugaban kasa yana bukatar mutumin da ba shi da inda-inda.

A cikin wata sanarwa da ya saka wa hannu, Atiku ya bayyana cewa matakin farko da duk wani ɗan takarar babban muƙami ya kamata ya ɗauka a mulkin dimokraɗiyya shi ne ya zaɓi mataimaki.

Ana kallon wadannan kalamai na Atiku a matsayin shaguɓe ga takwarorinsa na wasu jam'iyyu, musamman jam'iyyar APC da NNPP da LP, da har yanzu ba su zabi mataimakansu na dindindin ba.

"Ofishi musamman irin na shugaban ƙasa na buƙatar mutumin da ba ya inda-inda wurin ɗaukar mataki," in ji Atiku.

"Shi ya sa a ƙasashe da suka samu ƙwarewa a dimokraɗiyya, batun ɗan takarar shugaban ƙasa ya zaɓi mataimaki da kuma yadda ya zaɓi mataimakin na bayar da dama a gane yadda ƴan takara suka shirya tunkarar aikin da ke gabansu."

A makon jiya ne Atiku Abubakar ya ɗauki Gwamnan Jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP.

Har yanzu dan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC Ahmed Bola Tinubu bai ɗauki mataimaki na dindindin ba sai dai ya ɗauki Ibrahim Kabiru Masari, ɗan jihar Katsina, a matsayin mataimaki na riƙo.

Haka shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam'iyyar Labour Party wato Peter Obi bai ɗauki ɗan takara na dindindin ba amma ya ɗauki Doyin Okupe, a matsayin mataimaki na riƙo.

Sun ɗauki matakin ɗaukar mataimaka na wucin-gadi ne domin kada su wuce wa'adin da hukumar zaɓe ta Najeriya ta saka na 17 ga watan Yuni inda ta ce kada wata jam'iyya ta kuskura ta wuce lokacin ba ta bayar da sunan ɗan takara ba.

Sai dai jam'iyyun na da wata guda su sauya sunan wanda suka ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Amma a martanin da Bola Tinubu ya mayar kan wannan batu na Atiku, ya ce "abin takaici ne da damuwa a maimakon PDP ta mayar da hankali kan yadda za ta sasanta cikin gidanta bayan saɓa alƙawarin da ta yi na cikin gida kan batun karɓa-karɓa inda take ta neman rigima," kamar yadda Tunde Rahman, mai magana da yawunsa ya bayyana wa BBC.

Ya kara da cewa: "PDP da sauran ƴan takararta na yin shishigi ga harkokin cikin gida na APC inda suke ɗaukar nauyin yaɗa farfaganda kan batun Musulmi da Musulmi su yi takara da sauran ihuce-ihuce.

Ya kuma buƙaci PDP da ta yi abin da ke gabanta da kuma sasanta ƴaƴanta da ba sa ga maciji da juna.