Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Mutum fiye da dubu tamanin ne suka shiga Najeriya don gudun hijira’
Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa fiye da mutum dubu tamanin ne suka shiga kasar daga kasashen waje a matsayin 'yan gudun hijira.
Shugabar hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana hakan a tattaunawarta da BBC Hausa a yayin da ake bikin tunawa da Ranar 'Yan Gudun Hijira ta Duniya, wato ranar 20 ga watan Yuni.
Ana bikin a kowacce shekara domin jawo hankalin jama'a kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijira suke ciki tare da wayar da kawunan jama'a kan 'yancinsu.
Hajiya Imaan ta kara da cewa mutanen da suka shiga Najeriya sun fito ne daga kasashe talatin da hudu.
"Muna da 'yan gudun hijira daga kasashe kusan talatin da hudu yanzu haka, kuma wadanda suka yi rajista su kusan dubu tamanin da hudu ne. Mutanen da suka fi shigowa Najeriya sun fito ne daga Kudancin Kamaru saboda ana rikici a yankin Ambazonia,' in ji shugabar hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya.
Ta kara da cewa gwamnatin Najeriya tana ware makudan kudade domin tallafa wa 'yan gudun hijirar kamar yadda dokokin kasashen duniya suka bukaci ta yi.
Hajiya Imaan ta ce wadannan 'yan gudun hijirar suna da zabi uku: ko dai su ci gaba da zama a Najeriya, ko su koma kasashensu idan sun gamsu da yanayin da ake ciki a can, ko kuma Najeriya ta kai su wasu kasashen.
Sai dai ta bayyana cewa Najeriya ta riga ta gina musu makarantu da asibitoci da sauran abubuwan more rayuwa da za su samar musu da kwanciyar hankali.