Ƙayatattun hotuna na wasu abubuwan da suka faru a Afirka makon nan 3-9 Yunin 2022

An wallafa

Ƙayatattun hotuna na wasu abubuwan da suka faru a Afirka makon nan

Short presentational grey line
Madame Aboga, a stall keeper at the Ngobila Beach market in Kinshasa, DR Congo - Thursday 9 June 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Raye-raye ke nan da aka gudanar ranar Alhamis a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, don nuna murna da zuwan Sarki da Sarauniyar Belgium
Mermaid students at Merschool in Kayalami, South Africa - Friday 3 June 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dalibai a Afrika ta Kudu ke nan suke kwaikwayon aljanar ruwa a wani biki a makarantar Merschool da ke Kayalami
Black market gasoline products are sold on a road side in Paynesville, outside Monrovia, Liberia - Monday 6 June 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Litinin an ga yadda yan bunburutu ke sayar da fetur a gefen hanya a wajen birnin Monrovia na Liberia
A man sells black market fuel to a motorbike rider on a road side in Paynesville, outside Monrovia, Liberia - Thursday 6 June 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Liberia ta shiga matsanancin karancin man fetur da ake tunanin kutsen Rasha a Ukraine ne ya haifar da shi.
A boy harvests onion in Fayoum Province, Egypt - Thursday 9 June 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gundumar Fayoum a Kudancin Alkahira, babban birnin Egypt inda aka fara girbin albasa
A student handing out sweets before baccalaureate exams at the Sadiki High School in Tunis, Tunisia - Wednesday 8 June 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata daliba yayin da take raba alawa ga abokan karatunta, kafin su shiga aji don rubuta jarabawa a babban birnin Tunisia wato Tunis.
Students writing exams in a classroom in Gando, Burkina Faso - Friday 3 June 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dalibai ke nan ke rubuta jarabawar shekarar karshe a kauyen Gando da ke Burkina Faso
Children helping clean up a beach in Abidjan, Ivory Coast - Saturday 4 June 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Ivory Coast kananan yara ke tsince robobi a kan iyakar tekun Vridi da masu yawon bude ido ke zuwa shakatawa a Abidjan
The view from inside a house that is about to be demolished in Abidjan, Ivory Coast - Tuesday 7 June 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Har wayau a birnin Abidjan inda aka rusa gidajen wasu mazauna birnin saboda tsoron ambaliya.
Benedict Ogbu looking at photos of his late wife Theresa Ogbu in their home in Owo, Nigeria - Tuesday 7 June 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Benedict Ogbu zaune yana kallon hoton matarsa Theresa, wadda aka yi wa kisan gilla yayin harin Cocin Katolika da ke garin Owo a Najeriya.
Salif Keita gives concert at Turkiyeâs Presidential Symphony Orchestra (CSO) Ada Ankara venue in Ankara, Türkiye - 3 June 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mawaki Salif Keita, daya daga cikin manyan mawakan Afrika, kuma an gan shi a birnin Ankara na Turkiya yana wake wani taron biki.
Cherif Fall surfing during the A Great Day in the Stoke event in California, the US - Saturday 4 June 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani matashi ke wasan tseren cikin ruwa a Huntington Beach pier da ke California a Amurka
The women dancing during an event to honour the police in Addis Ababa, Ethiopia - Sunday 5 June 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadin da ta gabata ke nan a Habasha, inda aka gudanar da wani biki don karrama sojojin kasar a birnin Addis Ababa.
Two women at a protest in Khartoum, Sudan - Friday 3 June 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata ma ba a bar su a baya ba wurin gangamin tunawa da kisan masu bore a birnin Khartoum na Sudan a 2019. Akalla mutum 87 ne ake zargin sojoji sun kashe.
Black rhinos in Nairobi National Park with the city in the background, Kenya - Friday 3 June 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bakin karkandan ke kiwo a wani gandun namun daji da ke kusa da babban birnin Kenya wato Nairobi.
A field of sunflowers in Nakuru, Kenya - Sunday 5 June 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gonar fulawar 'Sunflower' a wata gona da ke garin Nakuru. Kwanan nan man gyada ya kara tsada a kasar.
Kenya's President Uhuru Kenyatta meets Africa Union soldiers in Mogadishu, Somalia - Thursday 9 June 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Alhamis kenan yayinda Shugaba Uhuru Kenyatta ke gaisawa da sojojin wanzar da zaman lafiya a Somaliya, inda za a rantsar da sabon Shugaban kasa.
A worker cutting electricity cables in Johannesburg, South Africa - Thursday 9 June 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana tsitstsinka wayoyin wutar da aka hada ba bisa ka'ida ba a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.
Queen Mathilde at the National Museum in Kinshasa, DR Congo - Wednesday 8 June 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Iyalan gidan sarautar Belgium za su cigaba da ziyara a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo har zuwa mako mai zuwa.
People take photos of the Kakuungu mask after its unveiling in Kinshasa, DR Congo - Wednesday 8 June 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wurin bikin, Sarki Philippe na Belgium ya mika sanannen mutum-mutumin Kakuungu, wanda daya ne daga cikin sama da kayan tarihi 80,000 da aka sace daga Jamhuriyar Dimkoradiyyar Kongo a lokacin mulkin mallaka.

Hotunan suna da hakkin mallaka