Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilan da ke sa 'yan siyasar Najeriya suke sauya sheka a siyasa
A daidai lokacin da wa'adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta bayar na jam'iyyun siyasa su mika sunayen wadanda za su yi musu takara a matakai daban-daban, wani abu da ya fito fili shi ne yadda wasu 'yan siyasa suka yi wuf suka sauya sheka domin samun takara a wasu jam'iyyun.
Yawanci dai ana alakanta sauye-sauyen da rashin akida ko manufa a siyasa duk da cewa wasu masana kimiyyar siyasa na cewa ba haka abin yake ba.
BBC ta duba wannan batun, inda ta yi hira da wasu kwararru kan harkar siyasa.
A kodayaushe, kakar siyasa na tare da da kakar sauya sheka a Najeriya. Yayin da wadanda suka yi nasara a takara mukaman shugaban kasa da na gwamnoni ke kokarin zabo wadanda za su taimaka musu, da dama wadanda suka sha kaye, ko kuma ba su gamsu da yadda aka gudanar da zabukan ba ke nasu kokarin ficewa daga jam'iyyun.
Kabiru Sufi masanin siyasa ne a birnin Kano da ke Najeriya kuma ya ce ddama ita siyasa kasuwar bukata ce.
"Duk inda aka samu rashin gamsuwa, akwai yiwuwar samun irin wadannan tsallake-tsallaken," in ji shi.
Sanata Adamu Aleiro na cikin 'yan siyasa na baya-bayan nan da suka sauya sheka. Ya fice daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Ya ce: "Mun koma PDP saboda rashin adalci da munanawa da kuma kiyayya da aka nuna mana a APC."
Ya kara da cewa sun koma PDP ne domin samun damar cin zabuka da taimaka wa jama'ar da ke goyon bayansu.
Sai dai cikin wadanda aka bata wa rai, ba dukkansu ne ke ficewa zuwa wata jam'iyyar siyasa ba. Wasunsu kan yi zamansu amma su rika yi wa jam'iyyar zagon kasa daga cikin gida.
Aliyu Sambo na cikin shugabannin jam'iyyar PRP a Kano kuma ya shaida wa BBC cewa hakan na yin illa ga 'yan takara da jam'iyyu.
"Wannan halin na raunata jam'iyyar kuma yana raunata 'ya'yanta. Sannan kai kanka, ba za ka yi tasiri a sabuwar jam'iyyar ba kamar yadda za aka yi a inda ka fito," a cewarsa.
Shin ya masana kimiyya ke kallon sauya sheka a dimokradiyyance?
Kabiru Sufi ya ce "Tsarin mulki ya bayar da damar sauya sheka, amma yawancin abubuwan da ke faruwa na da nasaba ne da yanke hukunci cikin gaggawa. Kuma ba a cika duba wadanda akida ta sa suka jajirce har ta kai su ga nasara ba."