Ba'amurkiyar da ta amsa laifin cewa ta horar da bataliyar mata mayaƙan IS a Syria

An wallafa

Wata Ba'amurkiya ta amsa laifin cewa ita ta jagoranci wata bataliyar mata mayaƙan IS a Syria, tare da kitsa kai hare-hare Amurka.

An samu Allison Fluke-Ekren, da laifin taimaka wa ƙungiyar tare da horar da mata da ƴan mata sama da 100.

Matar, wadda uwa ce kuma malamar makaranta, ta zama shugabar matan ƴan IS ta bar Amurka a 2011, sannan ta yi aiki da kungiyar 'yan tadda a Libya kafin ta je Syria.

Ta fuskanci hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 20 bayan yanke mata hukunci a watan Oktoba.

Fluke-Ekren, mai shekara 42, tsohuwar dalibar ilimin halittu ce sannan malamar makaranta, ta je Syria don shiga kungiyar bayan da ta bar Masar da Turkiyya.

A yayin da ta ke tare da IS din, ta jagoranci bataliyar kungiyar mata mai suna Khatiba Nusaybah, a Syria.

Babban aikinta shi ne koyawa mata da yara yadda za su rinka amfani da makamai, kamar bindigar AK-47 da gurneti da amfani da rigar ƙunar baƙin wake a cewa jami'a.

A wata kotu da ke Virginia ranar Talata, ta amsa cewa ta horar da dukkan matan kungiyar, to amma ta ce ba ta taɓa kokarin koyawa yara komai ba.

Ta shaida wa kafar yada labarai ta CNN cewa, "Ba mu da shiri ko niyyar horar da ƙananan yara mata a tsarin kungiyar".

Ana kyautata tsammanin wasu daga cikin matan za su bayar da shaida a kanta a yayin sauroron shari'ar.

Fluke-Ekren, wadda aka fi sani da Moniker Umm Mohammed al- Amriki, ta taba zama a Mosul, na Iraƙi, bayan da mayakan IS suka kama ta.

A cewar masu shigar da karar, daya daga cikin shaidu ya bayar da shaida a kanta game da tsatstsauran ra'ayinta abin da ake gani ya wuce hankali.

Ba'amurkiyar ta kuma amsa cewa sun tattauna a kan yadda za a kai hari Amurka, ciki har da kai hari kan wata jami'a da kuma rukunin shaguna.

Shaidan ya ce, matar na ganin cewa duk wani da za a kai idan ba a yi asarar aryuka masu yawa ba to aikin banza ne.

Bayanan matar sun nuna cewa mijinta na biyu mamba ne a Ansar Al-Sharia, wata kungiyar masu tayar da kayar baya da ta kai hari wata harabar Amurka a Benghazi, da ke Libya a 2012.

Ita da mijin nata wanda aka kashe daga baya a wasu hare-hare ta sama, sun karbi shugabancin kungiyar.

Iyalanta dai sun sha fadawa kotun cewa a hana ta nemansu don su ba bu su ba ita.

Iyalan nata sun ce ta ci amanarsu don haka ta daina tunanin ma ta sansu.