Zaben fitar da gwani na APC: Taron APC ya mamaye muhawarar shafukan sada zumunta a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙarshen tika-tika tik, in ji masu iya magana. Kuma yau ake gobe sai labari.
Dandalin Eagle Square da ke babban birnin Najeriya Abuja ya dauki harama tsaf don zaɓen fitar da gwani na ƴan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Sai dai rikici ya cukuikuye jam'iyyar ta APC gaba ɗayanta gabanin taron.
Daga dambarwar rashin tsayar da magana ɗaya a tsakanin gwamnonin jam'iyyar, sai batun cimma matsaya da yin sulhu, lamarin da ya gagara, sai batun ra'ayin shugaban jam'iyya da kuma maganar da shugaban ƙasa ya yi cewa ba shi da ɗan takara.
A yanzu kuma da aka wayi gari a ranar zaɓen sai ga kiraye-kirayen neman shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu ya sauka, biyo bayan rahotannin da ya yi cewa a zabi Shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan a zaman dan takarar Shugaban kasa na jam'yyar.
Sai dai da alama a ƙarshe dole wuƙa da nama su koma hannun daliget, waɗanda su ne za su yi zaɓen, don haka ma ake ganin su a amtsayin masu ƙarfin faɗa a ji a wannan gabar.
Ƴan Najeriya dai sun kasa yin shiru kan wannan zaɓe, domin kuwa tuni suka cika shafukan intanet waɗanda su ne manyan kafafen sadarwa a yanzu, inda suke bayyana ra'ayoyinsu.
Yayin da wasu suka mayar da hankulansu wajen tattaunawa a kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar gabanin zaɓen fitar da gwanin, wasu kuma sun mayar da hankali ne wajen faɗar wanda suke ganin shi ne zai yi nasara a zaɓen.

Abin da ake faɗa a shafukan sada zumunta
A shafin tuwita dubban mutane ne suke tattauna wannan batun, kuma maudu'in #APC Convention na cikin wadanda suka fi tashe.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Unilorin Marlian@TheMarlianya ce: "Ya Ubangiji, a yau mu ƴan Najeriya suna jira mu ga ayoyinKa kan abin da ya shafi zaɓen fitar da gwani na APC. Allah Ka shige mana gaba.
Stoner Dedoyin @omo_iya_bobo1ya rubuta a tuita cewa: "Zaɓen jam'iyyar APC a yau ya zama tamkar babban zaɓe na ƙasa💯😂..."
Wani kuma mai suna PeeJee @Sijibaba daliget ya bai wa saƙo inda ya ce: "Ya ku daliget don Allah ku zaɓi mutumin kirki a zɓen fitar da gwanin APC na yau."
Baffa @captain_awaisu ya ce: "Irin ƙarfin da APC ke amfani da shi a zaɓn fitar da gwanin nan da a ce mana duk wanda ya zama shugaban ƙasa na gaba ya yi amfani da irinsa cikin wata uku ya magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan."
Malomo @baloo1010 ya ce: "Zaɓen fitar da gwanin APC tamkar babban zaɓe. Daga masu faɗa a ji sai maciya amana."

Daga Facebook

Asalin hoton, Presidency
A shafin Facebook ma dai batun taron shi ya fi jan hankali, inda fiye da mutum 12,000 ke tattaunawa a kansa.
Amma mun ɗauko ra'ayoyin mutane ne a shafinmu na BBC Hausa Facebook.
Asia Dalhat ta ce: "Yadda suke ta kai wa da komowa a kan fitar da dan takaran shugaban kasa da haka suke yi don shawo matsalar tsaro, da an samu sauƙi sosai.
Princess mufeedah: "Ya Allah ka mana zabin alkairi a wanan mulkin, ya Allah ka zaba mana wanda zayi mana adalci a wanan kasar, Ya Allah ka ceto wannan ƙasar daga wannan masifar da muke ciki ameen👏👏.
Shi kuwa Ibrahim Mahuta raha ya yi cewa: "Delegates fa ai kasuwa ta bude, anma da shugaban jam'iyya zai masu bakin ciki."
Shi ma Muhammad Auwerl ya taya Ibrahim rahar da cewa: "Su delegates baki har kunne za a zo a ci banza."
Buhari Baba ya ce: "Ya Allah yadda jam'iyyar nan ta shiga ruɗani Allah duk wasu mugayen ƙasar nan ka saka su cikin ruɗanin da ba za su iya fitar da kansu ba.
A can shafin matambayi ba ya ɓata na Google ma dai dubban mutane ne ke neman bayanai kan abin da ya shafi taron d akuma ƴan takarar.










