Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
DR Congo: 'Yadda gahawa ta sauya rayuwata baki ɗaya'
An san Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo a matsayin kasar da kungiyoyin 'yan tawaye da dama ke zalinci fiye da ingancin gahawarsu, amma akwai wani shiri na kokarin canza hakan, in ji Moses Sawasawa.
Manoma tun kaka da kakani sun rika noman gahawa na Arabica a wani yanayi mai kyau da tuddai a tsibirin Idjwi da ke tafkin Kivu, da ke tsakanin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda.
A baya-bayan nan, dubban tsaffin mayakan da suka hada da Koko Bikuba, sun ce aiki a nan ya sauya rayuwarsu.
Lokacin da muka isa wannan wurin, mutane sun dinga jin tsoronmu," in ji ɗan shekara 37. "Rayuwata ta sauya albarkacin wannan aikin. Ina kula da yara shida da suke karatu."
Ko da yake Mista Bikuba bai so ya bayyana abin da ya faru a baya, amma ya ce ya yi matukar nadamar yadda ya cutar da kasarsa musamman ma al'umma kasar".
Galibin tsoffin mayaka a nan sun fito ne daga Masisi da ke lardin Kivu ta Arewa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, wanda aka kwashe shekaru ana fada.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa sama da mayakan sa-kai 120 ne ke kai hare-hare a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, mai arzikin ma'adanai da kungiyoyin masu dauke da makamai ke amfani da su.
Wani abu da ake farantawa Mista Bikuba shi ne yadda wasu mutane a garin na Idjwi wadanda da farko sun dauke shi da abokan aikinsa a matsayin "barayi da masu kisa" amma yanzu sun karbe su da hannu biyu.
Ya kara da cewa, "ba na fuskantar matsala a cikin wannan daji a yanzu kuma ina da rufin assiri ," in ji shi, sakamakon aikin da ya yi a fannin aikin gona.
Kusan tsoffin mayaka 2,400 ne ke aiki a matsayin manoma a Idjwi a kungiyar manoman gahawa watau SCPNCK.
A cewar kungiyar galibinsu tsoffin mayaka ne, ko da yake wasu, ciki har da Mista Bikuba, a baya sojoji ne.
Ƙungiyar tana sayar da gahawarta ga ƙasashe irinsu Amurka, Faransa da Belgium.
Gilbert Makelele wanda shi ne shugaban kungiyar ya ce a shekara 2012 aka soma shirin karkashin wani shiri na samar da zaman lafiya - amma kuma ya so ya shawo kan matsalar masu fasa-kwauri wadanda a cewarsa, suna daukar gahawa daga tsibirin Idjwi da ke kan iyaka da kasar Rwanda inda za su sayar da shi a kasashen duniya a farashi mai sauki.
Ya yi alfaharin cewa SCPNCK "yana taimaka wa tsaffin mayakan don samun kudinsu ba wai daga sace-sace ko fyade ba - kowa a cikin sojojin Kongo yana wannan wuri saboda rashin aikin yi".
Kungiyar ta SCPBCK tana samun tallafin gwamnati kuma jakadu da dama sun ziyarci garin domin fahimtar yadda suke aiki, na baya-bayan nan shi ne jakadan Amurka a DR Congo, Mike Hammer.
Ana yabawa gahawar Arabica ta wannan yanki saboda " ingancinsa kuma ba shi da bauri sosai, in ji Isabelle Prigo dan kasuwa daga Belgium.
Daga bishiyoyin kofi ne ake samun gahawa wanda aka fara nomawa a Habasha dubban shekaru da suka wuce.
A cikin noman zamani, ana shuka tsiron a cikin buhunan ƙasa, sannan a ɗauki kimanin watanni biyar ana shuka su kafin a dasa su cikin gonaki.
Gandun daji irin na Idjwi suna da kyau saboda filin yana taimakawa wajen dakatar da zaizayar ƙasa.
A wannan hoton ana iya ganin shukan gahawa a wata gona
A nan ne ake samun 'ya'yan itacen gahawa jajayen - wanda aka fi sani da cherries - bayan an tsince su da hannu daga bishiyar.
Jacques dan shekara 29 tsohon mayaƙi ne ke yin busar da gahawa tare da abokan aikinsa.
Wannan wani mataki ne na kula da ingancin gahawar, inda ake cire duk wani yayan gahawar da suka lalace ko bai karasa nuna ba.
Daga baya, ana cire jajayen bayan gahawar a wani tsari da ake kira milling.
Bayan an wankewa, sai a busar da gahawar.
Tsohon soja mai shan gahawa Bisimwa Kabo, mai shekaru 27, yana da alhakin tabbatar da cewa samfurin ya kasance mafi inganci.
Sai dai idan aka samu baragurbi a ciki wannan kan iya ɓata ɗanɗanon duka.
Mataki na ƙarshe shi ne zuba busar da 'yayan gahawa a cikin buhunan da aka shirya don bayarwa.
Sai an fitar da gahawar zuwa kasahen waje ake gasawa tare da nikawa
A shekarun 1980, mun kasance muna fitar da gahawa zuwa Amurka, Sudan da Habasha," in ji Christine Mugoli jami'a a ofishin kula da albarkatun noma na Kongo, ta kara da cewa abin da ake nomawa a shekara ya kai tan 500,000 idan aka kwatanta da ton 10,000 kacal a yanzu.
Gwamnati ce ke kula da harkar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje shekaru da dama da suka gabata, amma a yau yana hannun kungiyoyin hadin gwiwa, in ji ta, duk da cewa ana shirin saka hannun jarin gwamnati.
"Ana iya cewa gwamnati ta yi watsi da al'adun gahawa kadan," in ji ta.
"Har yanzu muna son mu mayar da matsayinmu a jerin kasashen da ke kan gaba wajen samar da gahawa a Afirka da ma duniya baki daya."
Koko Bikuba yana fatan shirin zai ga nasarar da aka yi a tsibirin Idjwi.
"Ina rokon hukumomi su kara inganta tsaro a gabashin kasar, don haka sauran sojoji masu irin wannan buri su samu damar amfani da irin wannan dama."
Dukkanin hotuna na da haƙƙin mallaka.