Bidiyon matan da suka yi kasadar shiga rijiya don neman ruwa ya ja hankalin mutane a Indiya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wani bidiyo da ya yaɗu kamar wutar daji na yadda aka ga wasu mata biyu sun kama bangon rijiya suna ƙoƙarin fitowa daga cikinta ya nuna irin matsanancin rashin ruwan da ake fama da shi a Madhya Pradesh da ke yankin tsakiyar Indiya.

Bidiyon ya nuna matan sun ɗane bangon rijiyar ta ciki ba tare da igiya ko wani abu da za su zura su ɗebi ruwan ba.

Yanayin rashin ruwa da ƙafewar rijiyoyi da gulbi sun tursasa al'ummar ƙauyen Ghusiya sayar da rai irin wannan wajen neman ruwa.

Akwai wasu sassan da yawa a Indiya da ke fama da matsanancin rashin ruwan.

Bidiyo da dama da ke nuna Indiyawa suna sanya rayuwarsu a haɗari wajen neman ruwa na yaɗuwa akai-akai.

A watan Afrilu, an ga wani bidiyon na wata mata da ta shiga cikin rijiya a jihar Maharashtra don neman ruwa.

Wani rahoto da aka fitar a shekarar 2009 ya bayyana Indiya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe 17 da suke fama da matsanancin ruwan sha.

Rahoton ya ce jihohin Madhya Pradesh da Punjab da Rajasthan da Uttar Pradesh da Gujarat da Uttarakhand da kuma Haryana na daga cikin waɗanda lamarin ya fi ƙamari a can.

A jihar Madhya Pradesh, kusan duk lokacin bazara sai an samu matsalar ƙarancin ruwa.

Gwamnatin jihar ta yi alkawarin samar da ruwan famfo a kowane ƙauye nan da shekarar 2024. Amma har yanzu miliyoyin mutane ba sa samun ruwan sha.

A ƙauyen Ghusiya, al'ummar garin sun ce za su ƙauracewa zaɓukan da za a yi a bana don nuna adawarsu da gwamnatin.

"Sai mun shiga can cikin rijiya muke samo ruwa. Akwai rijiyoyi uku a nan, duk sun kusa ƙafewa. Babu ruwa a rijiyoyin burtsatse," kamar yadda wata mata ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI.

"Ma'aikatan gwamnati da shugabannin siyasa kan zo nan ne kawai a lokacin yaƙin neman zaɓe. A wannan karon mun yanke shawarar ba za mu yi zaɓe ba har sai an samar mana da ruwan sha," in ji ta.

Indiyawa da dama sun yi ta mayar da martani a shafukan sada zumunta kan abin da suka kira "bidiyo mai ɗaga hankali" inda suka nemi jami'ai da suka kai wa ƙauyen agaji.

Indiya ita ce ƙasar da ta fi kowace haƙo ruwa a ƙarƙashin ƙasa a duniya - kuma da yawan mutane da hakan suka dogara don samun ruwa a kullum.

Amma kusan kashi biyu cikin uku na gundumomin ƙasar na cikin barazanar rasa ruwan da ake samu ta ƙarƙashin ƙasar, a cewar Bankin Duniya.

An yi ƙiyasin cewa Indiya za ta fuskanci matsanancin ƙarancin ruwa nan da shekarar 2050, inda birane 30 za su faɗa cikin wannan yanayi.