Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Samuel Kanu: Dalilin da ya sa muka biya kuɗin fansar miliyan 100 kafin a sake ni
Shugaban Cocin Methodist a Najeriya, Samuel Kanu, ya ce sai da aka biya naira miliyan 100 kafin 'yan bindiga su sake shi tare da wasu malamn Kirista biyu da aka yi garkuwa da su.
An sace Dr Kanu ranar Lahadi a kan wata babbar hanya a lokacin da yake komawa gida daga wata coci a kudu maso gabashin ƙasar, inda 'yan gwagwarmayar kafa ƙasar Biafra ke fafutikar ɓallewa daga Najeriya.
An sako shi bayan shafe awa 24 a hannun masu garkuwar.
Ya shaida wa BBC yadda 'yan bindigar suka nuna masa wani rami da suka jefa gawarwakin wasu da suka sace a baya.
Sun yi barazanar kashe shi da abokan tafiyarsa idan ba a biya kuɗin ba.
Malamin addinin ya ce Cocin Methodist ce a Najeriya ta tattara kuɗin, waɗanda aka ɗiba a buhu biyar da suka ƙunshi naira miliyan 20 kowanne.
Ya ƙara da cewa jami'an tsaron Najeriya ba su shiga lamarin ba.
Cikin wata sanarwa, rundunar sojan Najeriya ta musanta hannu a garkuwa da shi bayan wasu su zargi rundunar.
A kwanan nan an gabatar da wani ƙudirin doka a majalisar tarayya mai cike da ce-ce-ku-ce da zimmar daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane.
Har yanzu ana ci gaba da riƙe malaman ɗariƙar Katolika biyu da aka sace a Jihar Katsina bayan 'yan bindiga sun haura cocinsu tare da yin awon gaba da su da kuma wasu mutum biyu.
Tun daga 2011, an ba wa 'yan bindiga kuɗin fansa aƙalla dala miliyan 18, inda aka biya fiye da rabin kuɗin a tsakanin 2016 zuwa 2020, kamar yadda cibiyar SBM Intelligence da ke Jihar Legas ta bayyana.
Ana ci gaba da samun ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga, ciki har da masu iƙirarin jihadi, yayin da ake tunkarar babban zaɓe a 2023.