Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Dembele, Torres, Leno, Adamu, Garner da Raphinha

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaba na Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane, mai shekara 30, zai sanar da kungiyar cewa yana son barinta a bazara. (Fabrizio Romano)
Bayern Munich ta kusa cimma yarjejeniyar biyan fam miliyan 34 kan Mane. (Matteo Moretto)
Liverpool ta tuntubi wakilan dan wasan gaban Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 25. (Sport)
Chelsea ma na zawarcin Dembele. (Mundo Deportivo)

Asalin hoton, Getty Images
West Ham da Southampton na sa ido kan dan wasan gaban Red Bull Salzburg mai shekaru 20 Junior Adamu. (Mail)
Dan wasan bayan Villarreal da Spain Pau Torres, mai shekara 25, yana dab da komawa Manchester United bayan da wakilansa suka tafi Ingila domin ci gaba da tattaunawa. (Cadena Ser)
Leicester City na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Manchester United James Garner, mai shekara 21, bayan da ya taka rawar gani a lokacin da yake zaman aro a Nottingham Forest. (Mirror)
Arsenal na son karbar fam miliyan takwas da rabi daga hannun Benfica kafin sayar mata da mai tsaron ragarta Bernd Leno, mai shekara 30. (Sun).

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban Leeds United dan Brazil Raphinha, mai shekara 25, na iya fifita komawa Manchester United kan Barcelona. (Express)
Bournemouth da Rangers na zawarcin golan Crystal Palace da Ingila Jack Butland, mai shekara 29. (Sun)
Aston Villa da Southampton suna cikin rukunin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan bayan Peterborough na Ingila Ronnie Edwards, mai shekara 19. (Sun)
Tottenham ta shaida wa Villarreal cewa tana son fam miliyan 17 kafin sayar mata da dan wasan tsakiyarta dan asalin Argentina Giovani Lo Celso, mai shekara 26. (Sun).

Asalin hoton, Getty Images
Spurs din na kuma gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Croatia Ivan Perisic, mai shekara 33, daga Inter Milan. (Fabrizio Romano)
Paris St-Germain na son dauko dan wasan Everton da Brazil Richarlison, mai shekara 25. (Mail)
Barcelona na zawarcin Jules Kounde da kuma Kalidou Koulibaly na Senegal, mai shekara 30 (Mundo Deportivo)











