Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu huɗu da suka jawo dala ta haura N600 a Najeriya
A ranar Asabar 22 ga watan Mayun 2022 ne dalar Amurka ta ƙara tsada idan aka kwatanta ta da nairar Najeriya, inda a karon farko a tarihi aka sayar da dala ɗaya a kan naira 610 a kasuwar bayan fage.
Sai dai duk da haka, dalar ba ta sauya farashi ba a hukumance a kan naira 419.
Amma ƴan ƙasar da dama da suka dinga ƙaroafi a kan hakan sun bayyana damuwa a kan yadda dalar ba ta samuwa a hukumace daga bankuna ko da mutum yana da sahihan takardun yin tafiya wata ƙasa, wacce gwamnati ta sharɗanta cewa za a iya bai wa mutum
Mutane da dama da BBC Hausa ta zanta da su sun nuna matuƙar damuwa kan wannan hawa da dalar ta sake yi, sun kuma bayyana takaicin da suke ji na yadda dalar ba ta samuwa ta daɗin rai.
Kazalika mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta kan wannan tashin gwauron zabi da dala ta yi a kan naira.
Lamarin tashin dala abu ne da yake taɓa kowa a ƙasar, saboda a kowane lokaci dalar ta tashi to sai an samu ƙaruwar farashin abubuwan yau da gobe ko da kuwa wanda ake kasawa a titi ne.
Ga abin da wasu ke cewa a dandalin Tuwita:
@Dsage_BigHeart ya yi shaguɓe ne da cewa: "Yanzu dala ɗaya ana sayar da ita a kan naira 610, lallai Najeriya tana samun ci gaba, sai ya saka alamun dariya😂😂.
@mayorsoaga ya ce: "A yanzu da dala ta kai sama da naira 600, hakan na nufin matsakaicin albashin ma'aikaci na tsawon kwana 30 a ƙsar bai wuce dala 50 ba."
@JFK__1 ya ce: "Dala ta kai naira 610… Najeriya kar ki kashe mu.
Me ya jawo tashin dalar?
BBC Hausa ta tattauna da wasu ƴan kasuwar canji ta bayan fage da kuma ƙwararru kan tattalin arziki, kuma kusan duk bakinsu ya zo ɗaya, inda suka bayar da dalilai huɗu da suke ganin sun jawo hakan.
1. Ƙaruwar tafiye-tafiye
Wani masanin tattalin arziki Dr Shamsudden Muhammad, ya shaida wa BBC cewa ƙaruwar tafiye-tafiye da aka samu saboda sassauta dokokin kullen korona da ƙasashen duniya suka yi ya sa dalar ta sake tsada, saboda kuɗi ne da ake buƙata don yin bulaguron.
"Kwanan nan masu zuwa Umara sun ƙaru, ga masu zuwa ƙasashen duniya don kasuwanci, duk waɗannan abubuwa ne da ke sa dala ta ƙara tashi," in ji masanin.
Sannan akwai masu yin tafiye-tafiye domin neman lafiya zuwa ƙasashen waje wanda shi ma duk da dala ake amfani, kuma mutane na kokawa cewa ba sa samu daga bankuna ko da sun bi halastattun hanyoyin da gwamnati ta tanada don a samu a farashin gwamnati.
Ya ƙara da cewa kuma tun da gwamnati ba za ta iya bayar da isasshiyar dalar ba dole a nema a wajen ƴan kasuwa, wanda su kuma suke ƙara mata kuɗi don ƙaruwar buƙatarta.
2. Zaɓukan fitar da gwani
Wasu ƴan kasuwar canji uku da BBC Hausa ta zanta da su a birane daban-daban da suka haɗa da Abuja da Kano da kuma Lagos, sun ce hada-hadar zaɓukan fitar da gwani da ake ta yi a ƙasar na daga cikin dalilan da suka sa dalar ta yi tsada.
Sun tabbatar da cewa daga ƙarshen makon da ya gabata zuwa makon da ake ciki, sun yi ciniki sosai daga wajen ƴan siyasa da ke sayen dala suna bayar da naira.
"Dama ita dala wani sa'in ta kan yi tsada ne idan akwai tsananin buƙatar ta a kasuwa.
"To su ƴan siyasa sun fi jin daɗin mu'amala da ita saboda ba sai sun dinga yawo da kuɗi mai yawa na naira niƙi-niƙi ba suna dakonsu.
"Ƴar dala kaɗan a ambulan ta isa su sallami jama'arsu ba tare da an ankara ba. Amma maganar gaskiya kam mun yi ciniki a ƴan kwanakin nan daga wajen ƴan siyasa," in ji dukkan mutane ukun da suka buƙaci a sakaya sunayensu.
3. Ƙaruwar sayo kaya daga ƙasashen waje
Wannan ma wani dalili ne mai zaman kansa da ke sa farashin dala ke ta'azzara in ji masanin tattalin arzikin.
"Har yanzu ƴan kasuwa manya da matsakaita a Najeriya shigo da kaya suke yi daga ƙasashen waje irin su China da UAE da Indiya da sauran su.
"To wannan dalili ya sa buƙatar dalar na ƙaruwa, sai kuma take ƙara yin tsada, Aka kuma hadu da buƙatarta da ƴan siyasa ke yi, wannan shi ya sa ta yi wannna tashin gwauron zabin."
4. Ɗalibai masu karatu a ƙasashen waje
Wani dalili da ke sa farashin dalar ƙara tashi har da rububin da ɗalibai masu fita karatu ƙasashen waje ke yi na sayenta kamar yadda Dr Shamsudden ya faɗa.
Ko a ranar Talata 24 ga watan Mayu wani bincike da babban bankin ƙasar ya gudanar, ya bayyana yadda a cikin watannin uku, 'yan kasar suka kashe fiye da dala miliyan 220 wajen neman ilimi a kasashen waje.
Wannan ƙiyasi kawai ya isa nuna yadda buƙatar dala take ƙaruwa a ƙasar, domin da dalar ne ake biyan kuɗin karatu a ƙasashen wajen.