Zaben 2023: Zabukan fid da gwani a jam'iyyar PDP a Najeriya na fuskantar cikas

PDP

Asalin hoton, PDP

An wallafa

Deliget-Deliget na Jam'iyyar PDP a jihohi daban-daban na Najeriya na can na jefa kuri'a domin zaɓen wadanda za su yi wa jam'iyyar takarar 'yan majalisun jihohi da tarayya a zaɓen badi.

Tun jiya Lahadi ne aka fara yin zaɓen amma kuma rahotanni na nuna cewa a wasu wuraren zabukan sun ci gaba a har wayewar garin yau Litinin.

Tuni dai rahotanni suka ce jam'iyyar ta dage zabukan kwata-kwata a jihar Imo saboda wata gardama kan jerin sunayen deliget, wato wakilan jam'iyyar da ke zaben wanda zai tsaya takara.

Alhaji Yusuf Abubakar Dingyadi na daga cikin kwamitin da ke gudanar da zaben fitar gwanin a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriyar, ya kuma musanta bayanan da jaridu suka buga.

Ya fada wa BBC cewa zaɓukan na tafiya lami lafiya a mafi yawan jihohi, in ban da wurare kalilan a kudancin kasar.

Ya ce an samu fahimtar juna ta hanyar maslaha tsakanin 'yan takara, inda kuma hakan bai yiwuwa ba ana ci gaba da jefa kuri'a don fitar da wadanda suka yi nasarar samun tikitin tsayawa takarar.

Sai dai lura da yadda ƙasar ke cikin matsalar rashin tsaro, Yusuf Dingyadi ya ce sai da rakiyar jam'ian tsaro aka iya fara gudanar da zaɓukan a wasu yankunan jihar ta Kaduna.

''Sakataren kwamitin gudanar da zaɓen Malam Hamisu Anani ya samu rakiyar jam'ian tsaro sun je har Birnin Gwari don ganin cewar an gudanar da zaɓen lami lafiya. Hakama a Giwa, hakama a wasu kananan hukumomin da ake ganin akwai matsala,'' in ji shi.

Ya kuma tabbatar da cewa labaran da suke samu na nuna cewa zaɓukan na gudana ba tare da wata matsala ba har a Kudancin ƙasar in ban da jihar Imo, kuma a cewarsa hakan bai rasa nasaba da matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankin.

Dama wasu jaridun cikin gida sun ambato cewa a jihar Legas har zuwa lokacin fadauwar rana a jiya Lahadi babu alamun deliget-deliget ko masu gudanar da zabe a dandalin da aka tsara gudanar da zabukan.

Kazalika rahotanni sun ruwaito cewa babbar jam'iyyar adawar ta dakatar da zabukan fidda gwanin kwata kwata, a dalilin rudani da aka samu kan sunayen deliget-deliget da aka tantance don jefa kuri'a.

To amma Yusuf Dingyadi ya musanta hakan, inda ya ta'allaka barakar da aka samu a jihar ta Imo da rashin tsaro, musamman yadda ƙungiyar 'yan awaren IPOB ke tada kayar baya a yankin.

Yana yiwuwa a jihar Imo akwai kananan hukumomin da ake ganin suna da matsala, ko irin saboda barazanar da ake gani ta IPOB da wata barazanar da ake gani ta tsaro.''

Kawo yanzu babu wasu bayanai kan kammala zaɓukan a inda ba a samu matsala ba, amma ana sa ran bayanai su rika fitowa nan gaba kadan, kan yadda zabukan suka gudana a fadin kasar.