Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Canada ta katse alaka da kamfanonin sadarwa na China
Canada ta hana manyan kamfanonin sadarwa na China biyu shiga hada-hadar hada katafaren aikinta na intanet na 5G.
Daman an dade ana sa ran kasar za ta dauki wannan mataki, wanda da shi yanzu Canadar ta bi sahun wasu manyan kasshe biyar da ke yi wa kansu lakabi da ''Five Eyes'' wadanda ke musayar bayanai na sirri, kasshen da suka hada da Amurka da Birtaniya da Australia da kuma New Zealand.
Yanzu duk kamfanin Canada da ya riga ya sanya wata na'ura da katafaren kamfanin Huawei ko ZTE na China suka samar, za a nemi ya cire ta.
Shi dai tsarin sadarwar intanet na 5G yana da inganci sosai, inda yake da sauri, kamar walkiya, kuma yana kunsar bayanai mau dama fiye da tsarin 4G.
Kafin a kawo ga wannan mataki, tun da farko a watan Satumba na 2018 Canada ta ce za ta yi nazari a kan irin barazanr da ake ganin na tattare da amfani da na'urorin da kamfanonin Huawei ko ZTE na China ke samarwa.
Sai dai wata biyu bayan wannan sanarwa sai aka kama babbar jami'ar kul da harkokin kudi ta kamfnin na Huawei, Meng Wanzhou, a Canadar, bisa umarnin kamatn da aka bayar daga Amurka, wand kuma hakn ya ki ga rama wa kura aniyarta, inda ita ma China ta kama wasu 'yan Canada biyu, kodayke dai a lokacin hukumomin China sun nuna cewa kamen da suka yi wa mutnen ba shi da nasaba d wancan kame da aka yi wa jami'ar kamfanin na China.
An dai saki dukkanin mutanen uku a watan Satumba na shekarar da ta wuce bayan Meng Wangzhou ta cimma yarjejeniyar dage gurfanar da ita gaban shariar da masu gabatar da kara na Amurka.
Sanarwarkasr ta Canada ta hana sanya na'urorin kamfanon na China, ta sa yanzu kasar na da alakar musayar bayanan sirri da sauran kasashen da ba s mu'amulla da kamfanonin na China kamar Amurka wadda ta na ce cewa kamfanin Huawei da ZTE barazana ne ga tsaron kasa, sboda alakarsu ta kut da kut da gwamnatin China.
Kuma shigar da su aikin sanya na'urorin sadarwa na intanet na 5G, zai ba w China damar satar bayanai da za a rika aikawa ta wannan hanya.
Ministan masana'antu na Canada, Francois-Philippe Champagne, ya yi bayanin dalilin daukar wannan mataki nasu:
Ya ce, ''Wannan bai taba zama wata gasa ba. Wannan abu ne da ya kunshi daukar matakin da ya dace. Wannan abu ne da ya shafi samar da tsarin kare kayanmu, in ce, a wannan zamani na 5G, a al'amuran da suka shafi intanet, a wannan lokaci da muke ta dogaro a harkokinmu na rayuwar yau da kullum a kan intanet dinmu, wannan ne matakin da ya dace, kuma muna farin cikin sanar da shi yau, saboda hakan ne zai tsare intanet dinmu ga al'ummominmu da za su zo nan gaba.''