Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukumomi sun ce mutum tara sun mutu sakamakon fashewar tukunyar gas a Sabon Gari ta Kano
Ma'aikatar jinkai ta Najeriya ta ce an ciro gawar mutum tara daga baraguzan ginin da ya rushe sakamakon fashewar tukunyar gas a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar.
Lamarin ya faru ne ranar Talata a Aba Road da ke Unguwar Sabon Gari a birnin na Kanon.
"Mutum biyu sun jikkata sakamakon fashewar kuma an dauke su zuwa Asibitin Sojin Sama da ke Kano. Kazalika an kammala aikin ceto bayan an kwashe barazguzan ginin," in ji sanarar da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na Tuwita.
Da farko dai, wasu rahotanni sun nuna cewa bam ne ya fashe a wata makaranta da ke yankin na Sabon Gari sai cdai hukumomi sun musanta hakan.
Sarkin Kasuwar Sabon Gari Nafi'u Nuhu Indabo ya shaida wa BBC cewa lamarin ya rutsa da mutane da dama ciki har da yara ƴan makaranta.
Wakilinmu na Kano, Khalifa Dokaji, ya je wajen da abin ya faru, wato makarantar Winner Kids Academy da ake zargin a can aka ta da bam din.
"Rufin makarantar ya yaye saboda ƙarfin abin fashewar. Dukkan hanyoyin da suke kusa da wajen sun cika maƙil da jama'a waɗanda ke cike da damuwa da alhini," in ji Dokaji.
Tuni Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano CP Sama'ila Dikko da shugaban hukumar DSS na Jihar suka halarci wajen, sannan motocin asibiti sun je don kwasar waɗanda harin ya rutsa da su.
CP Dikko ya shaida wa BBC cewa tukunyar gas da ake walda da ita a wajen ce ta fashe, "amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa," in ji Kwamishinan.
Ya ƙara da cewa an gano gawarwaki huɗu kuma ana ci gaba da bincike. Amma Khalifa Dokaji ya ce ana iya ganin jini ta ko ina a wajen da kuma wasu sassan jikin mutane.
Jami'an tsaro sun yi ta ƙoƙarin shawo kan mutane waɗanda da alama ke fusace, don su bari a yi bincike kan musabbabin faruwar lamarin.
An daɗe ba a ji labari mai kama da wannan ba wato na kai harin bam a jihar Kanon, dalilin da ya sa hakan zai jefa mutane cikin ruɗanin wa yake da alhakin hakan.
Ba a Kano kaɗai ba, an samu sauƙin tashin bam a faɗin Najeriya a shekarun bayan nan, ba kamar a da ba da hakan ya zama kusan ruwan dare.