‘Yan siyasa sun juya wa yan Najeriya baya ne?

An wallafa

A daidai lokacin da ake ci gaba da samun matsaloli musamman na tsaro da matsin tattalin arziki da sauran matsaloli waɗanda suka yi wa rayuwar ƴan Najeriya tarnaƙi, su kuwa ƴan siyasa a ƙasar na ci gaba da gudanar da hidimominsu na neman yadda za su lashe zaben 2023.

Babu wani abin da aka fasa a hidimomin siyasa tun bayan da aka kaɗa gangar siyasa a ƙasar inda ƴan siyasa da suka haɗa da ƴan majalisa da gwamnoni da manyan iyayen jam'iyyu da sauran masu ruwa da tsaki a siyasa ke ci gaba da zagayawa jihohi suna tallata kansu da ƴan takararsu da jam'iyyunsu domin samun nasara a zaben da ke tafe.

Ko a ƙarshen makon da ya gabata, sai da aka samu rahoton kashe kusan mutum 50 a Jihar Zamfara sai dai da alama hakan bai dauki hankalin 'yan siyasa ba.

Bugu da ƙari a cikin shekarar nan ne aka sace sama da mutum 60 a jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja inda har aka kashe wasu, an sace jama'a da dama a garuruwan arewacin Najeriya musamman jihohin Neja da Zamfara da Kaduna da Sokoto.

Ana cikin wannan hali aka rinƙa fama da wahalar man fetur da dizal wanda hakan ya ƙara kudin sufuri da kuma kayan masarufi a kasuwanni, talakawan ƙasar na fama da tsadar rayuwa.

Ga ɗalibai na gida a zaune saboda yajin aikin ASUU, duk da tuni wasu ɗaliban suka kama sana'o'i amma irin rashin wutar latarkin da ake fama da shi yana naƙasa ƙananan masu sana'o'i da dama da kuma karya ƙwarin gwiwar sabbin-shiga sana'o'i kamar su kansu ɗaliban.

A taƙaice babbar matsala dai musamman a arewacin Najeriya ita ce ta ƴan bindiga kuma duk da wannan matsala ƴan siyasa ba su fasa kashe kuɗaɗensu ba da fita yaƙin neman zaɓe.

Ina matsalar take?

Dangane da wannan matsala, BBC ta tattauna da Dakta Abubakar Kari wanda mai sharhi ne a kan siyasa kuma Malami a Jami'ar Abuja inda ya ce abin da wannan lamari ke nunawa shi ne aƙidu da alƙiblar ƴan siyasar Najeriya kwata-kwata sun sha bamban da na sauran al'umma.

"Yayin da al'ummar Najeriya ke cikin ƙunci da halin ha'ula'i abubuwa suke ta ƙara taɓarɓarewa, amma su ƴan siyasar Najeriya abin da ya sha musu kai kawai shi ne gwagwarmaya da kuma neman iko.

"Wannan kuma abu ne mai hatsari ƙwarai da gaske kuma abin da yake nunawa shi ne cewa ko da sun samu nasara babu tabbacin za su inganta rayuwar jama'a," in ji Dakta Kari.

A cewarsa, bisa dukkan alamu abubuwan da suka dami ƴan siyasar Najeriya kuma suka fi ba fifiko ba su ba ne abubuwan da jama'a ke so a magance musu ba.

"Idan aka ci gaba da samun irin wannan giɓi, wata rana abubuwan ba za su yi daɗi ba saboda idan har al'umma ta gane za ta yanke ƙauna ga ƴan siyasa da gwamnati da kuma shuwagabanni."

Mafita

Ganin yadda waɗannan lamuran ke faruwa, a cewar Dakta Abubakar Kari mafita ita ce yan siyasa su guji fifita buƙatunsu kan buƙatun al'umma.

Ya bayyana cewa ko da ƴan siyasa sun samu nasara sun ɗare kan madafun iko, ba lallai su ji dadin mulkin ba ko kuma ya ɗore idan jama'a ba su cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali.

"Masifa za ta ci gaba da ruruwa a cikin ƙasa muddin ba su samo bakin-zaren ba wajen ganin cewa an magance manya da ƙananan matsaloli da suka addabi ƙasa," in ji Dakta Kari.