Vladimir Putin: Me zai faru idan a hukumance shugaban Rasha ya ayyana yaki a kan Ukraine?

An wallafa

Mai yiwuwa Shugaba Vladimir Putin ya ayyana yaki kan Ukraine a hukumance a yau 9 ga watan Mayu, kamar yadda kafafen yada labarai da jami'an kasashen Yamma ke hasashe. Amma me sanarwar a hukance ke nufi? Sannan yaya sanarwar za ta kasance? Baki daya yaya lamarin zai kasance?

Gwamnatin Rasha ta kafe cewa tana "gudanar da aikin soja na musamman ne". An haramta amfani da kalmomin "yaki" da "mamaya" game da farmakin da kasar ke kai wa a Ukraine.

'Watakila a ayyana yakin a ranar 9 ga watan Mayu'

Sai dai gabanin jita-jitar da ake yadawa da sauya batutuwa, Sakataren Tsaron Birtaniya Ben Wallace ya shaida wa gidan rediyon LBC cewa, "Ina ganin zai tashi daga batun yin.... 'aiki na musamman'... Ya dade yana jan zarensa, yana sauya taku akai-akai, bai dai bayyana cewa, 'Ku, wannan yaki ne a kan 'yan Nazis... na bukatar ganin karin mayakan Rasha'...

"Sam ba zan yi mamaki ba... cewa zai ayyana yaki kan Ukraine a ranar 9 ga watan Mayu, 'Muna tsaka da yaki, da mayakan Nazi na duniya.'"

Amurka: 'Gagarumin abin mamaki'

Jami'ai a Amirka sun yi tsokaci kan shigen abin da zai faru. A farkon makon nan ne mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida Ned Price ya ce "zai zabo abin tashin hankali idan Moscow ta yi amfani da 'ranar nasara' ta ayyana yaki kan Ukraine, wanda ita a kashin kanta za ta ba su damar yin abin da ba su samu damar yi ba, amma yanzu tsaf za su aikata."

Kafar yada labaran CNN ta ambato wata majiya na cewa ta yiwu Putin ka iya amfani da wannan rana ko dai ya ayyana yaki kan Ukraine a hukumance, ko kuma ayyana nasarar da ya samu a abin da ya kira "aikin soji na musamman", ko ma fadada shi, ko ayyana duka biyun. Har wa yau, akwai rade-radin ta yiwu kai-tsaye zai ayyana yakin komai zai faru ya faru.

Sai dai an ce ayyana yakin a hukumance ya danganta kan goyon bayan da 'yan Rasha ke nunawa kan aikin sojin a Ukraine, da bai wa gwamnatin Rasha damar mayar da hankali wajen kara wa sojojinta kayan yaki cikin gaggawa domin cimma manufar da Putin ke da ita kan makwabciyar tasu.

Kremlin: 'Aikin banza'

A ranar Laraba mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya musanta rahoton yiwuwar ayyana yaki a hukumance da cewa "karya ne", kuma "zancen banza ne."

A ranar 2 ga watan Fabrairu, kwanaki biyu gabanin fara mamayar, Peskov ya musanta shirin kasarsa Ukraine, inda ya ce tsokanar fada ce kawai.

Ga abin da yake cewa a lokacin: "Idan za ku iya tunawa cikin daukacin tarihinta, Rasha ba ta taba kai wani hari ba. Sannan Rasha, wadda ta kai labari bayan fama da yake-yake da dama, ita ce kasa ta karshe a Turai da za ta yi amfani da kalmar 'yaki'.

Fafaroma Francis ya ce firaministan Hungary Victor Orban, ya shaida masa lokacin wani taro ranar 21 ga watan Afirilu, cewa gwamnatin Raasha tana shirin kawo karshen aikin soji a Ukraine ranar 9 ga watan Mayu.

A farkon watan Maris, Putin ya ce babu alkawarin ayyana dokar ta-baci saboda hakan na faruwa idan an yi wata kasa ta mamaye su.

Jerin matakan da za a iya bayyanawa da take dokokin kasa da kasa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Rasha ya bayyana kan "kotun soji":

  • Sojojin wata kasa su mamaye Rasha, ko karbar ikon soji, ko yanki ko fadada ayyukansu
  • Amfani da makamai kan Rasha. Misali, hare-hare ta sama ko ruwan bama-bamai
  • Toshe tashar ruwa ko tekun baki daya
  • Harin sojojin wata kasa kan sojin Rasha, ba tare da la'akkari daga inda aka girke su ba
  • Amincewa wata kasa a yi amfani da yankinta domin kai hari kan Rasha
  • Tura rundunar sojin wata kasa, ko makaman yaki da za a iya amfani da su domin yakar sojin Rasha.

'Lokacin yaki' da tsattsaurar dokar soji

Za a iya samar da Kotun soji, bayan a hukumance Rasha ta ayyana yaki kan Ukraine. Sai dai ba a yi bayanin wannan matakin a dokokin ba, an dai fadi cewa watakila a ayyana yakin.

Yakin ka iya sanyawa a gabatar da kotun soji, duk da cewa akwai bayanai daban-daban kan hakan. "Lokacin yaki" ana ganinsa matsayin alaka tsakanin kasashe biyu, wanda ka iya sanyawa a samar da "kotun soji" mataki na wata kasa da gwamnati.

Sashe na 18 a dokokin tsaro ya bayyana cewa: "Ana ayyana yaki ne ta hanyar amfani da dokokin gwamnati, misali wata kasa ta kai harin soji kan Rasha, sannan da lokacin cimma yarjejeniyar kasa da kasa kan gwamnatin Rasha."

Dokokin kasa da kasa

Dokokin kasa da kasa ba su amince a ayyana yaki ba sai lamura sun baci.

Batun matakin daukar matakin yaki da aka cimma a Hague a shekarar 1907, ta yi bayanin bai kamata a daukin matakin soji ba tare da an bada wa'adi ko kafin daukar matakin a fara da sasantawa, da wa'adi ko dai ayyanawa ko kuma gargadin fara yaki.

Dokoki da dama ne suka samanar da dokar soji mai tsauri a Rasha, ma'aikatar tsaro, ayyukan soji, atisayen soji.

Dokokin sun hau kan kusan dukkan wadanda ake da su a kasa, sun kuma shafi harkokin yau da kullum na 'yan kasa, da hukumomi, da tattalin arziki, da kasuwanci, da ayyukan 'yan jarida, da iko da siyasa da sauransu.

Karin karfin iko

Za a kara wa shugaban kasa da gwamnati karin karfin iko.

Za a iya haramta jam'iyyun siyasa, ko taruka, za a haramta duk wani abu da ya shafi taron jama'a, sannan gwamnati na da ikon haramta duk abin da ta ga dama ko abin da bai ma ta ba duk da sunan tabbatar da zaman lafiya a kasa.

Za a iya sanya tsauraran dokoki, ciki har da tafiye-tafiye kasashen waje, ko sauya inda kake zaune.

Za a sanya dokar takaita zirga-zirga, a kowanne lokaci gwamnati za ta iya kwace dukiyar mutane matukar bukatar sojoji ta taso.

Za a iya haramta sayar da makamai da sauran abubuwa. An rattaba dukkan matakan ne da wadanda za a dauka karkashin sashe na 7 na dokar sojin.

Shirin ko-ta-kwana

Karkashin dokar sojin, gwamnati za ta iya ayyana shirin ko-ta-kwana, zai iya zama na gama-gari ko tsaka-tsaki, gwamnatin ka iya killace wani bangare na kasar maimakon baki daya. Ba a cika daukar mataki irin wannan ba matukar aka ayyana dokar soji, amma dai za a iya gabatar da ita idan bukatar hakan ta taso.

Lamarin ba wai zai shafi sojoji ba, gwamnati ka iya samun kanta a ciki har da masana'antu da tattalin arzikin kasa baki daya.

Sojojin ko-ta-kwana

Rukunin wadanda ake fara amfani da su idan bukatar hakan ta taso, su ne sojojin ko-ta-kwana, wadanda ba sa aiki cikin rundunar soji amma za a iya kiransu idan aikin sojin ya taso. Rukuni na biyu ya kunshi sojojin da suka yi ritaya amma a shirye suke su yi aikin kasa.

Yawancin sojojin wadanda aka sake kira domin yin aikin kasa, za su iya samun tabbacin ba za su taba rasa aikinsu da suke yi ba. Hakan dabara ce ta kokarin ci gaban ayyukan gwamnati da masana'antu.

Ayyana yaki da fitowar soji ka iya magance matsaloli guda biyu, wanda yawancin kwararru suka lura sojojin na Rasha sun fara gajiya su na kuma fadi tashi ne. Rashin ayyana yakin da tirjewar soja na kin zuwa filin yaki wata matsala ce mai zaman kan ta.

'Tafiyar hawainiya' a ci gaba

A yanzu masu sa ido kan harin Rasha ga Ukraine na cewa ana tafiyar hawainiya maimakon samun ci gaba. Wani jami'in ma'aikatar tsaron Amurka da bai so a fadi sunansa ba, ya ce sojin Rasha na da kankanuwar nasara a gabacin biranen Izum da Popasna na Ukraine, sannan nasarar ta su ba yabo ba fallasa a sauran yankunan kasar.

Ma'aikatar tsaron Pentagon ta ce a bayyane ta ke karara sojojin Rasha na kasada, da kokarin kauce wa samun wadanda za su jikkata cikinsu kama daga sojin sama da na kasa har da na ruwa.

Samar da ayyukan yi

Jami'an gwamnatocin Birtaniya da Amirka sun ce, Rasha ta dauki kusan kashi biyu zuwa uku na sojinta sun girke a Ukraine.

A fakaice alamu sun nuna sojin Rasha na bukatar karin dakaru, musamman a banagaren kara daukar ma'aikata a fannin soji, wadanda akai rade-radin an dauka aika aiki amma na wucin-gadi karkashin ma'aikatar tsaron Rasha daga farkon watan Maris, ta hanyar amfani da shafin intanet na tallan ayukan farar-hula mai suna Headhunter da SuperJob.

Igor Strelkov

An yi ta tattaunawa a shafukan sada zumunta kan dokar sojin da kuma manyan janar din sojin da ake son tabbatar da ita da kuma wadanda za su jagorance ta. Yawancin kwararru kan ayyukan soji da masu shafukan sada zumunta na marawa dokar baya. Daya daga cikin 'yan ga-ni-kashe-nin dokar shi ne tsohon kwamandan sojin Rasha Igor Strelkov (sunansa na yanka Ghirkin), wanda ya yi fice kan rawar da ya taka lokacin da Rasha ta mamayi Donbas a shekarar 2014.

Tattalin arziki

Dokar soji ka iya shafar tattalin arikin Rasha.

An samu bambancin ra'ayi kan kungiyoyi daban-daban a batun dokar sojin. Misali, sanya kamfanoni su samar da kayayyakin da sojoji ke bukata. Hakkin na kan gwamnati ta biya kudaden.

'Yan kasa, kamar yadda dokar kasa ta tanada, ka iya shiga cikin aikin tsundum domin tabbatar da cewa an bai wa sojoji dukkan abubuwan da suke bukata ta kuma biyan kudaden komai yawansu.

Sashe na 8 na dokar kan dokar soji, zai ba da damar daukar matakan da ka iya shafar tattalin arziki, misali gabatar da tsauraran matakai na wucin-gadi ciki har da mamayar tattalin arzikin, da harkar kudade da safarar kayayyaki ba tare da shinge ko matsala ba.

Wadannan alamu ne da ke nuna rayuwa ka iya sauyawa idan a hukumance Rasha ta ayyana yaki kan Ukraine.