Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka kai hari a Chibok bayan ziyarar Antonio Gutteres
Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari kan al`ummar Kautikeri da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
An kai harin ne a daidai lokacin da Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Gutteres yake wata ziyarar aiki a Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutum bakwai suka rasu sakamakon harin.
Wani mazaunin garin Chibok kuma jagora a garin Mista Ayuba Alamson ya yi wa BBC ƙarin bayani kan yadda lamarin ya faru inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin biyar da rabi na yammacin Talata.
Ya bayyana cewa sun afka cikin garin ta wurare biyu, inda wurin farko shi ne wani ƙauye da ake kira Kwada wanda akwai sansanin sojoji a ta wurin sannan kuma suka shiga garin ta bayan wani burtali wanda wuri ne da mayaƙan suka saba bi.
Mista Ayuba ya bayyana cewa bayan mayaƙan sun shiga garin, sun ta musayar wuta da ƴan banga da sauran masu kare garin.
Ya ce bayan kimanin mutum bakwai da aka kashe, mayaƙan sun ƙona mota ɗaya da kuma ɓalle wani shago inda suka kwashe kayan shago suka kuma cinna masa wuta.
Ya bayyana cewa a ƴan kwanakin nan, ana zaune cikin fargaba a ƙauyukan da ke Chibok inda ya ce sau da dama idan yammaci ya yi, jama'a kan kwashe iyalansu su kai su bayan gari domin tsoron kada mayaƙan Boko Haram su kai musu hari.
A cewarsa, tun bayan da aka sace ƴan matan Chibok a 2014, an kai wa Chibok da ƙauyukan da ke kusa da ita hari fiye da sau 90, sai dai babu wasu bayanai da suka tabbatar da hakan.
Ya ce akasari ƴan jarida ba su samun labarin halin da suke ciki inda ya ce a halin yanzu wasu mutane suna tunanin barin gari sakamakon ba su da ƙasar noma da kuma halin da za su yi noman.
Har yanzu dai rundunar sojan Najeriya ba ta ce komai ba kan wannan harin na baya-bayan nan da mayaƙan suka kai a Chibok ba.