Shin za a iya raba mutum da matsayinsa na dan kasar Birtaniya?

People protesting against the Nationality and Borders Bill on 27 February 2022

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Ashitha Nagesh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Community Affairs correspondent, BBC News
  • An wallafa

Gwamnati za ta samu 'yancin kwace wa mutane 'yancinsu na zama 'yan kasa ba tare da sun sani ba a karkashin sabon karfin ikon da 'yan majalisar dokoki suka kada wa kuri'a.

Nan ba da dadewa ba ne ake sa ran shirin - wanda bangare ne da kudirin dokar zama ɗan kasa da kan iyakoki - mai cike da takaddama - zai zama doka.

Mene ne zama dan kasa?

Dan kasa matsayi ne na doka. 'Yan kasar Birtaniya suna da 'yancin da doka ta tanadar musu na zama a kasar, har ma da samun dama ta ilimi, da kyautata jin dadi, da kiwon lafiya. Za kuma su iya kada kuri'a.

Har wa yau, zama dan kasa shaida ce, kuma yakan zama wani bangare na tunanin dan Adam na jin cewa ana tafiya tare da shi.

Wasu mutanen da ba 'yan kasa ba na da 'yancin zama na dindindin a Birtaniya tare da mutane da dama da ke da 'yanci iri daya, duk da cewa ba za su iya kada kuri'a a zabuka ba.

Za su samu matsayi na cigaba da zama a kasa.

Me aka yanke shawarar yi?

A karkashin sabuwar dokar, za a bai wa ofishin lura da shige da fice karfin iko na soke 'yancin zama dan kasa na mutane ba tare da an shaida musu ba.

Gwamnati ta bayyana cewa za ta yi amfani da wannan ne kawai a yanayin halin da ba a saba gani ba; kamar idan mutum na wurin da ya zama fagen yaki, ko yana boye a inda ba zai yiwu a tuntube shi ba.

Amma masu fafutika sun bayyana cewa matakin zai haifar wa da kariyar zama ɗan kasa cikas, sannan akwai yiwuwar zai fi shafar kabilu 'yan tsiraru.

Mece ce sabuwar dokar?

A halin yanzu, sakataren harkokin cikin gida zai iya cire wa mutane 'yancinsu na zama dan kasa a bisa wadannan dalilai:

  • Saboda ''amfanin jama'a'' kuma ba zai sa su zama wadanda ba su da kasa ba
  • Idan mutum ya samu takardar izinin zama dan kasa ta hanyar damfara
  • Idan abubuwan da mutum ke aikatawa zai zubar da kimar Birtaniya kuma za su iya neman izinin zama dan kasa a wani wuri

Ofishin lura da shige da fice na bukatar sanar da mutum, wanda daga baya yana da damar daukaka kara - duk da cewa hakan wani mataki ne mai daukar tsawon lokaci.

Ofishin lura da shige da fice na kuma bukatar amincewa cewa mutumin ya cancanci neman zama dan kasa a wata kasar. Birtaniya ce ke da alhaki a karkashin dokar kasa da kasa ta kauce wa barin mutane ba tare da suna da kasa ba.

Mutane nawa ne aka kwace wa zama dan kasa?

Babu jimillar adadin a halin yanzu.

Amma kuma Ofishin lura da shige da ficen ya bayyana cewa tsakanin shekarar 2010 da 2018, mutane 19 ne a kowace shekara da aka kwace wa zamansu na 'yan ƙasa wanda hakan ya fi wa jama'a alkhairi'', kana mutane akalla 17 a kowace shekara saboda aikata zamba.

Shafin intanet na dokar shige da fice ta Free Movement ya bayyana cewa bincikensu ya yi nuni da cewa mutane fiye da 460 ne aka kwace wa zamansu na 'yan ƙasa daga 2006 zuwa 2020 - 175 a bisa dalilai na tsaro, yayin da 289 kan aikata zamba.

Su wanene wadannan mutane?

Cikin fitattun mutane da aka ƙwace wa zamansu na 'yan ƙasa na baya-bayan nan, ita ce Shamima Begum, daya daga cikin 'yan mata dalibai uku a gabashin Landan da suka tafi kasar Syria a shekarar 2015 don taimaka wa kungiyar masu da'awar kafa kasar Musulunci (IS).

An haifi Mis Begum a Birtaniya, iyayenta 'yan asalin Bangladesh ne kuma shekarunta 15 lokacin da ta bar kasar.

A cikin watan Fabrairun 2020, wata kotu ta yanke hukuncin cewa kwace wa Mis Begum 'yancinta na zama 'yar ƙasa ya saba wa doka saboda ''asalinta 'yar kasar Bangladesh ce", don haka kasancewarta 'yar kasar Birtaniya ba zai sa ta zamo ba ta da kasa ba. Kasar Bangladesh ta bayyana cewa batun ba a nan ya tsaya ba, kuma ba za a amince ta shiga cikin kasar ba.

A cikin watan Fabrairun shekarar 2021, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa ba za a amince ta dawo Birtaniya ba don ta daukaka kara a kan matakin da aka dauka a kan ta.

Daya wanda shi ma aka kwace wa 'yancin kan batu na tsaron kasa, shi ne Tauqir Sharif, wani ma'aikacin agaji daga Walthamstow. Ya koma kasar Syria a shekarar 2012 tare da matarsa, kuma an kwace masa 'yancin zama dan kasa a 2017.

Ofishin shige da fice ya ce ya yi amanna cewa Mista Sharif na da alaka da kungiyar al-Qaeda. Amma ya musanta ikirarin, tare da kiran matakin a matsyin rashin adalci da kuma wariyar launin fata.

Ya batun sauran kasashen?

'Yan asalin kasar Birtaniya haifaffun Amurka ba za a iya kwace musu 'yancinsu na zama 'yan ƙasa ba saboda 'yancinsu na haihuwa ne karkashin kundin tsarin mulkin Amurka.

Amma kuma, wadanda suka zama 'yan kasar Amurka - wato mutanen da suka yi kaura zuwa Amurka - za a iya kwace musu a bisa dalilai kadan da suka hada da kasancewa cikin wata haramtacciyar kungiya saboda samun takardar zama dan kasa ta hanyar zamba.

A kasar Australia, za a iya kwace wa mutum 'yancinsa a bisa dalilai na tsaro da sauran al'amuran tsaron kasa, idan suna da takardar zama dan wata kasar daban.

Za a iya kwace wa mutum 'yancin zama ɗan ƙasa bisa dalilai na cin amanar kasa, da rashin biyayya da sauran al'amuran da suka shafi tsaron kasa a kasashen Kungiyar Tarayyar Turai 16, da suka hada da Girka, da Faransa da kuma Romania.

A shekarun baya, Birtaniya ta kwace wa karin mutane zamansu na 'yan ƙasa fiye da kowace kasa ban da kasar Bahrain, kamar yadda wani rahoto da Cibiyar Lura da Mutanen Ba Su da Ƙasa ya bayyana.