'Yan bindiga sun ƙi sakin dagacin Rijana da 'ya'yansa 'duk da biya musu buƙatunsu'

Asalin hoton, Daily Trust
'Yan bindigar da suka sace dagacin garin Rijana na Jihar Kaduna har yanzu na ci gaba da riƙe shi da 'ya'yansa duk da cewa an biya musu wasu buƙatu da suka nema.
'Yan fashi masu garkuwa da mutane sun sace Dagaci Ayuba Dodo Dakolo ranar Alhamis tare da 'ya'yan nasa uku a gonarsa da ke yankin.
Sai dai wani mazaunin yankin da ke da ilimin yadda lamarin ya faru ya shaida wa BBC Hausa cewa sun sako biyu daga cikin 'ya'yan nasa. Amma ya nemi mu ɓoye sunansa.
Sai dai kuma baya ga 'ya'yan nasa, 'yan bindigar sun sace wasu 'yan mata da samari fiye da 10 waɗanda su ma ke hannunsu ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Garin Rijana na kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadda ta yi ƙaurin suna wajen sace-sacen mutane da 'yan fashin daji ke yi.
"Bayan an biya musu buƙatun da suka nema sai suka turo da wasu'
"Jiya (Alhamis) sun ce suna buƙatar a saya musu man fetur da shinkafa da sauran wasu abubuwa kuma a kai musu, kuma na samu labarin an yi duka waɗannan abubuwa amma suka ƙi sakin sa," a cewar majiyar.
Mutumin ya ƙara da cewa bayan an kai musu kuma sai suka sake gindaya wasu sharuɗɗan.
"Kayan ba su wuce kayan abin ci ba da kuma kayan shaye-shaye."
Halin da ake ciki a Rijana
Garin na Rijana na cikin halin jimami, inda mutane suka yi cirko-cirko suna jiran tsammani, in ji mutumin.
"Lokacin da na je ban tarar da jami'an tsaro a gidan sarkin ba, amma dai akawai talakawansa da mukansantansa suna jiran su ji ci gaban da aka samu daga wajen 'yan bindigar.
"Tabbas akwai jami'an tsaro, suna nan a bakain titi. Kana zuwa za ka gan su suna kaiwa da komowa. Amma matsalar ita ce, yanzu sun ('yan bindigan) ce ba za su bari a yi noma ba.
"Ko a jiya an gan su kan babura da yawa sun yi gabas, sun sake nausawa cikin dajin.
"A cikin gari, jami'an tsaro na ba mu haɗin kai gaskiya. Akwai DPO a garin, da kuma kaftin ɗin soja da ke kula da rundunar soja da ke kula da sintiri a kan hanya. Sai dai ko suna da wani shiri mu farar hula ba za mu sani ba."
Mutumin ya ƙara da cewa manoma na cikin fargaba "saboda idan har mutum ya bar garin da kilomita ɗaya ba lallai ne ya dawo ba".
Yadda tsaron yankin Ƙatari zuwa Rijana ya gagari jami'an tsaro

Asalin hoton, Kaduna State Government
Garuruwan Katari zuwa Rijana sun kasance yankin da 'yan bindiga ke yawaita cin karensu babu babbaka kan matafiya, inda ko a wannan lokaci ana suka tare jirgin kasa tare da buɗewa fasinjoji wuta.
Mutane da ake cewa sun rasu sun kai bakwai sannan sama da 22 sun jikkata, sannan akwai wasu da dama da ba a ji duriyarsu ba tun bayan hari kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja dauke da fasinjoji 970 a watan Maris.
Masana na ganin matsalar tsaro a Najeriya na ci gaba da gagarar hukumomi ganin cewa a kodayaushe da an soma tunanin sauki sai abubuwa su sake rincabewa.
Dr. Kabiru Adamu wanda ke nazari da sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya na cewa ba abin mamaki ba ne a ce akwai manufar siyasa kan abubuwan da ke faruwa kan tsaro a Najeriya, sai dai ya ce wannan batu zargi ne.












