Idriss Deby: Abu biyar da suka kamata ku sani shekara guda bayan kashe shugaban Chadi

Asalin hoton, Getty Images
An kashe Fil Mashal Idriss Deby a fagen-daga, lokacin da ya je karfafa wa sojojin Chadi gwiwa a yakin da suke yi da 'yan tawayen kasar, kwana guda da sanarwar nasararsa a zabe bayan ya shafe shekaru 30 kan karagar mulkin kasar.
Dansa Janaral Mahamat Kaka Deby Itno, shi ya dare karagar mulkin kasar, da nufin shirin babban zabe, da tabbatar an dawo da mulkin dimukaradiyya turbar da ta dace cikin watanni 18, wadda sau daya aka taba hakan kamar yadda kundin zaben kasar na 98 ya bayyana.
Kamar yadda wani mai bincike a cibiyar ci gaba da kare ayyukan ta'addanci, Agassiz Baroum, ya ce 'yan Chadi sun gaji da yakin shekara da shekaru da ake yi a kasar.
"Lamarin ya fara juyewa siyasa-siyasa, saboda yanzu suna da makamai dalilin da ya sa ake ba su muhimmanci ke nan. Amma duk da hakan ana ci gaba da samun matsalolin kai hare-hare. Akwai tarin jama'ar da ke son zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai an samu hakan sannan an kuma yi aiki da su sannan za a kai ga gaci,'' in ji shi.
Shin me ya sauya a kasar Chadi, shekara guda bayan mutuwar Shugaba Idriss Deby Itno?
Sabon kwamitin riko da gwamntin Soji ta samar
An jingine kundin tsarin mulkin jamhuriyar na hudu na 4 ga watan Mayu 2018, shekaru uku bayan samar da shi domin maye gurbinsa da wanda kasar ke amfani da shi shekaru 22 da suka gabata. A yanzu shi ne tsarin da ake bi a Chadi mai rassa uku kuma duka a cikin gwamnati.
Da farko, akwai fannin da sojoji ke tafiyarwa, aikinsu shi ne tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaron kasa. Wannan fannin dan marigayi Idriss Deby wato Mahamat Debby da wasu manyan janar din soji hudu ne jagoranta.
Tun farkon watan Mayu, Mahamat Debby ya nada fanni na biyu da ke kula da harkokin gwamnati, mai mambobi 40.
Albert Pahimi Padacke ne ke jagorantar gwamnatin, kuma shi ne firaminista na karshe da ya yi aiki tare da marigayi Deby, an nada shi bayan sake nazarin kundin tsarin mulki na 2018.
Sai fanni na uku, wata majalisar dokokin wucin-gadi, mai mambobi 93, wanda su ma Mahamat Deby ne ya kafa su.
Rikita-rikitar siyasa kan gwamnatin riko
An dauki watanni biyar kafin kafa gwamnatin rikon sojin Chadi da mika mulki, su kafa sauran rassa biyu masu muhimmanci na gwamnatin-riko.
Gwamnatin-rikon mai mutane 133, wanda yawancinsu dama mabobin gwamnatin da ta gabata ne, an kuma hada da wasu daga cikin 'yan adawa ne da suka amince da sabuwar gwamnati, sun kuma amince a hadu domin tabbatar da kasar kan turbar daidai.
Sai dai fa ba duka ne suka aminta da hakan ba, musamman wasu daga cikin sun ki aminta da wannan sasanci da kuma tafiya tare.
Babbar jam'iyyar kawance ta Wakit Tama, da kungiyoyin farar hula da na kare hakkin dan adam sun dade da shelanta rashin amincewa da tsare-tsaren marigayi Deby, musamman na sauya wa'adin mulkin shugaban kasa da ya yi har karo shida.

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 6 Afirilu 2022, shugaban jam'iyyar Wakit Tama, ya sanar da dakatar da tattaunawa da gwamnatin Chadi mai-ci.
"Mun gano cewa babu wani abu da za a tattauna akai na hakika. Tun lokacin da muka fara tattaunawa da su, mun gano babu wata aniya ta kawo sauyi a tare da su. Kamar yadda muka ga abin da ya faru a taron da aka yi a birnin Doha na kasar Qatar, ana son bai wa fanninsu fifiko, ya yin da sauran za su zam 'yan amshin shata.
Za mu iya duba halin da muke ciki a yanzu, idan suka nuna aniyar sahihiyar tattaunawa za mu amince, amma idan ba haka ba to babu mu a wannan tafiyar," in ji Master Max Loalngar, shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta Chadi, kuma mai sa ido kan hadin kan kasa na, Wakit Tama.
Amma ga Success Masra, daya daga cikin shugabannin 'yan adawa kuma shugaban jam'iyyar da ake kira Transformers, ya ce kamata ya yi a ce wadanda suka jagoranci gwamatin-rikon ba za su tsaya takara a zabe mai zuwa ba.
''Matukar ana son mika mulki cikin tsanaki kamata ya yi jagoran CMT da sauran janar din nan 14 da sauran 'yan tawagar da suka zaba a mulkin na riko, su mika mulki salin-alin domin kawo karshen komai, su mika ga wata tawaga mai tabbatar da dorewar dimukradiyya wadda 'yan Chadi suka zaba, amma idan ba haka ba za su tsaya takara, don haka ya kamata su sauka.''
Kawo yanzu gwamnatin rikon ta Chadi ba ta ce uffan kan ikirari da zarge-zargen da 'yan adawa suka yi.
Yaushe za a yi zabe?
Kamar yadda hukumomin Chadi suka bayyana, kafin dawo da tsarin mulki yadda ya dace, gwamnatin riko ta sanya kan alhakin shirya taron 'yan kasa domin tattaunawa, wanda shi zai zama makomar Chadi.
Wannan zaman tattaunawar ne zai bada damar daukar matakan da suka dace, domin tabbatar da dimukradiyya, da sahihin zaben da kowa zai aminta da shi.
"Daman lamari irin wannan ya gaji tsaiko da jan kafa. Ba laifinmu ba ne, mun sanya lokacin zaman tattaunawar a watan Janairu, amma hakan ba ta yiwu ba. Ba mu ji dadi ba, kuma mun ba da hakuri, muna fatan za mu kammala komai mu mika mulkin cikin watanni 18 kamar yadda muka tsara, wannan shi ne abin da muke son yi.
Kuma shugaban Mulkin riko ba za taba saba lokaci da gangan ba. Ai soja ne, kuma ya na cikin gwamnatin nan tun da fari," in ji mai magana da yawun gwamnati, Abderaman Koulamallah a hirarsa da BBC.
Gwamnatin riko, lokacin gagarumar zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa gwamnatin riko ba ta kawo karshen ayyukan jam'iyyun siyasar Chadi ba, 'yan adawa da masu rajin kare hakkin dan adam sun shaida wa BBC an kashe akalla mutum 17 a zanga-zangar da aka dinga yi ta kin amincewa da ci gaban mulkin soja.
Shugaban hukumar kare hakkin dan adam a Chadi, Maître Max Loalngar, ya shaidawa BBC, ''Ni din nan na san an kahe mutane 18, wadannan su ne mutanen da aka kashe saboda sun fito zanga-zanga tun ma a lokutan baya na zabuka da kuma wannna lokacin da sojoji ke mulki.''
Amma hukumomi sun musanta hannu a kisan farar-hular, kamar yadda ministan yada labarai Abderaman Koulamallah, ya shaida wa BBC lokacin da muka tuntube shi kan batun sasantawa da 'yan adawa.

Asalin hoton, Getty Images
Ina batun babban taron kasa?
A wajen jawabinsa na farko ga 'yan kasa, a ranar 29 ga Afirilu 2021, shugaban gwamnatin riko, Mahamat Idriss Déby Itno ya yi kira ga 'yan kasar su amince a zauna domin tattauna makomar kasarsu.
''Ta hanyar soyayya, da fahimta, da aminci, da yafiya, da jajircewa ne kadai za mu sake gina kasarmu. Mu na kira ga duk masu ruwa da tsaki, da 'yan kasa na gari, su zo mu yi wannan tafiya mai cike da tarihi da kalubale, domin samawa matasan kasarmu ingantacciyar makoma,'' in ji shi.
An dai shirya fara tattaunawar share fage nan da makonni biyu masu zuwa, wato 13 Maris a birnin Doha na Qatar, da nufin tattaro 'yan kasar da wasu ba sa ga maciji da juna, da shugabannin al'umma, da na soji, da na 'yan siyasa da sukai gudun hijira, sai dai har yanzu babu tabbas kan ko za a cimma abin da ake bukata.











