Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Sterling, Nemanja Matic, Saliba, Harry Kane da Rudiger

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Raheem Sterling
An wallafa

Dan wasan gaban Manchester City da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 27, na cikin jerin 'yan wasan da AC Milan ke son saya a yayin da ake rade-radin cewa za a cefanar da zakarun na Italiya sau 18 a kan fam miliyan 850 (Gazzetta dello Sport)

Real Madrid da Barcelona na sha'awar sayen dan wasan bayan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 29, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana amma yana sha'awar ci gaba da zama a Stamford Bridge. (The Athletic)

Manchester United za ta samu tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai idan tana son dauko dan wasan gaban RB Leipzig da Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 24. Nkunku yana kan idon United bayan ya zura kwallaye 30 a wasanni 44 a bana. (Sport Bild)

A halin da ake ciki, Manchester United ta sake farfado da sha'awarta ta sayen dan wasan bayan Villarreal dan kasar Spain Pau Torres, mai shekara 25, a bazarar nan. (Manchester Evening News)

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jose Mourinho

Tsohon kociyan kungiyar ta Red Devils Jose Mourinho yana sha'awar kawo Nemanja Matic zuwa Roma bayan dan wasan tsakiyar Manchester United da Serbia din mai shekara 33, ya bayyana cewa zai bar Old Trafford (Tuttomercatoweb).

Tottenham na da kwarin gwiwar ci gaba da rike dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 28, a bana, kuma suna tunanin komawa kungiyar Brentford don dakko dan wasan tsakiya na kasar Denmark Christian Eriksen, mai shekara 30. Spurs din kuma suna sa ido kan dan wasan tsakiyar Leicester da Belgium, Youri Tielemans, mai shekara 24. (Times)

Newcastle na shirin kawo karshen sha'awarta ta sayen Darwin Nunez na Benfica, mai shekara 22, yayin da dan wasan gaban na Uruguay ke son zuwa kulob din gasar zakarun Turai, inda ake kallon dan wasan Brentford na Ingila Ivan Toney, mai shekara 26 a matsayin madadinsa. (Telegraph)

Dan wasan bayan Arsenal da Faransa William Saliba, mai shekara 21, ya ce akwai yiwuwar ya ci gaba da zaman aro a Marseille bayan karshen kakar wasa ta bana. (Le Parisien)

William Saliba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, William Saliba

Sai dai Atletico Madrid na son siyan Saliba, wanda ya koma Arsenal a shekarar 2019 daga Saint-Etienne. (L'Equipe)

Dan wasan gaban Arsenal dan kasar Ingila Eddie Nketiah, mai shekara 22, yana son buga wasa a kai-a kai kuma ana alakanta shi da Leeds da Crystal Palace da kuma West Ham. (The Beautiful Game Podcast)

Brighton ta tuntubi dan wasan gaban Arsenal Khayon Edwards, mai shekara 18, wanda ya ci kwallaye 17 sannan ya taimaka aka ci shida a wasanni 22 da ya buga a makarantar koyar da wasanni ta Arsenal. Chelsea ma na neman Edwards. (Mirror).

Tottenham na son dauko dan wasan Roma da Italiya Nicolo Zaniolo, mai shekara 22. (Calciomercato)

Noussair Mazraoui

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Noussair Mazraoui

Bayern Munich na dab da kammala cinikin dan wasan Ajax da Morocco Noussair Mazraoui, mai shekara 24. (Fabrizio Romano)

Golan Crystal Palace dan kasar Sipaniya Vicente Guaita, mai shekara 35, yana son komawa Valencia, inda ya shiga makarantar horaswa, kafin ya yi ritaya daga buga wasa. (AS)

Tsohon kocin Norwich Daniel Farke ya fito a matsayin wanda zai maye gurbin Sean Dyche a Burnley yayin da shima tsohon kocin West Ham da West Brom Slaven Bilic shi ma ke nuna sha'awar aikin. (i Paper)