Ukraine war: Yankin Bucha ya cika da gawarwaki a yashe da tankokin ƴaƙi da aka kone

    • Marubuci, Daga Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Bucha
  • An wallafa

Wani yanki na garin Bucha ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da suka zama tamkar maƙabarta ga burin Rasha na yin kawanya da ƙwace babban birnin Ukraine, Kyiv, domin hambarar da gwamnatin Shugaba Volodymyr Zelensky.

Wannan na zuwa kwana biyu ko uku bayan sojojin Rasha sun tsallaka Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu, lokacin da dakarun Ukraine suka murkushe yunkurin masu mamayar ta hanyar yi musu kwanton-bauna a yayin da suke kan hanyarsu ta shiga garin na Bucha.

An tarwatsa ayarin sojojin a ɗaya daga cikin ƙwanton-ɓauna na Ukraine domin takawa dakarun Rasha burki.

Tawagar BBC ta samu damar shiga Bucha saboda a ranar Juma'a dakarun Rasha suka kammala ficewa, a wani mataki da Rasha ta ce yaƙinta zai karkata a gabashin Ukraine.

Rasha ta ce, ba tare da wata hujja ba, ta cimma manufar yaƙinta a tsakiyar Ukraine, kuma ba ta haɗa da ƙwace birnin Kyiv ba.

Makonni biyu ko uku a yakin Rasha ya ƙare. A kan titin Bucha ana iya ganin dalilin.

Manyan dakaru daga cikin sojojin sama na Rasha sun shiga cikin garin a cikin motoci masu sulke waɗanda za a iya ɗauka a jirgin sama. Sun kutsa ta tashar jirgin sama na Hostomel, da aka kai wa hari kuma sojojin Rasha suka kwace da suka sauko daga jirgi mai saukar angulu a ranar farko ta mamayar Ukraine. Ko a lokacin dakarun Ukraine sun turje.

Lokacin da suka ratsa ta Bucha kan hanyar zuwa Kyiv, ba su sha da daɗi ba.

Hanyar ƙarama ce kuma a miƙe, mafi saukin yi wa kwaton ɓauna. Shaidu sun ce sojojin Ukraine sun kai wa ayarin hari ne da jirgi marar matuki samfurin Bayraktar na Turkiya. Wasu makwabta sun ce akwai ƴan sa-kai na Ukraine a yankin.

Duk da haka yi nasarar aikatawa, motar da ke jagoratar ayarin ta tsaya kuma hakan ya sa sauran suka maƙale. Ba a taba tarkacen ba.

Matasan da suka shiga aikin soja sun gudu, in ji mutanen yankin, kada a mayar da su ga ikon Ukraine. Wani mutum mai kimanin shekaru 70 wanda ya kira kansa Uncle Hrysha, ya ce: "Na ji tausayinsu, sun kasance matasa, ƴan 18 zuwa 20."

Ya nuna kamar Rashawa, a yayin da suke koƙarin ficewa Bucha, ba su da wannan tausayin. Aƙalla gawar maza 20 ne ke kwance kan titi lokacin da dakarun Ukraine suka shiga garin. Wasunsu an ɗaure hannayensu a baya. Magajin garin ya ce sun binne mutum 280 a makeken ƙabari.

Wasu fararen hula ƙalilan da suka tsaya sun ce sun yiƙoƙarin kaucewa ƴan Rasha. Sun haƙa itace domin samun wuta suna dafa abinci saboda babu gas da wuta da ruwa duk sun katse.

Masu kawo gaji suna kawo ɗauki daga Lviv a gabashin Ukraine, da kuma wasu ƙasashe da ke da nisa da yaƙin.

"Wannan ne burodi na farko da muka smau a cikin kwana 38, in ji wata mata da ake kira Maria.

Mutane da dama da suka gudu zuwa kasashen waje, sun rufe ƙofofin tsaro.

Ƴan mil kaɗan daga, wurin da aka tafka ɓarna ya kai zuwa filin jirgin saman Hostomel. Dakarun sojin saman Rasha sun yi kokarin amfani da shi a matsayin sansanin kutsawa zuwa Kyiv.

An tarwatsa jirgi mafi girma tun da farko, yana cike da tarin ramuka. Jirgin da kansa wanda ƴan Ukraine ke kira mafarki (Mriya) ya malale a baya da tarkace na injina a warwatse. Makomarsa ta kasance manuniya ga abin da ke faruwa a Ukraine.

An kashe kuɗin ƙasa wajen samar jirgin, a matsayin babbar alama ta ƙarfin Ukraine na samar da babban aiki a sassan duniya.