Yakin basasar Ethiopia: Matan da ke shan bakar wuya sakamakon yakin Habasha

An wallafa

An cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya a Habasha wata 16 da fara yakin basasa, domin a samu kai kayan agaji ga mutanen da ke fuskantar yunwa. Wannan rikici na arewacin yankin Tigray dai ya janyo an rika aikata muggan laifukan yaki kuma ko wanne bangare ya aikata wannan laifi, ciki kuwa har da abin da kungiyar kare hakkin dan adam ta kira "fyade a matsayin makamin yaki". Wakilin BBC Kalkidan Yibeltal ya tattauna da wasu mata da abin ya shafa a yankin Amhara mai makwabtaka.

Gargadi: wasu masu karatu za su iya jin wasu kalamai marasa dadi

Ta tabbata cewa komawa gidan da yan uwan Zemzem suka yi wata guda bayan tsere wa mamayar 'yan tawaye ba karamin kuskure ba ne.

Matashiyar, wadda muka sakaya sunanta saboda tsaro, ta tsere ne daga kauyensu da ke yankin Amhara tare da mijinta da jaririnta a watan Agustan bara. Karshe suka koma rayuwa a wani kauye da ya fi nasu muni.

Lokacin ana wata tara da fara yakin basasar yankin Tigray da ya tashi hankali.

Rikicin da 'yan TPFL ke jagoranta ya ci gaba da kamari inda suka mamaye kudancin lardin, tare da kwace yankin daga ikon gwamnati, ciki har da kauyen su Zemzem.

Ita da mijinta sun yanke shawarar komawa gida lokacin da abubuwan bukatar rayuwa suka yanke a kauyen. Amma bayan komawar su, sai suka hadu da wani gungun mayakan Tigray.

Suka zargi mijinta da cewa dan kwangila ne, kuma zai iya kasancewa daya daga cikin sojojin gwamnati da suka makale ko kuma daya daga cikin 'yan bidiga da ke a kauyen, mayakan sai suka fara yi masu tambayoyi,

Zemzem ta shaida wa BBC cewa an dauke su zuwa wani gida da ke gefen hanya inda aka yi mata duka tare da yi mata fyade. Wasu mayaka biyu ne suka yi mata hakan a gaban danta. Sun kashe mijinta lokacin da yake kokarin dakatar da su.

"Ina iya tunawa dana ya rika kuka sosai," in ji ta, lokacin da take bayar da labarin abin da ya faru a ranar 26 ga watan Satumba 2021,

"An zubar da jini ko ta ina... Na ci gaba da numfasawa amma ba ni da tabbacin ko ina raye. Jikina ko ta ina jini ne ke zuba. Kafafuna sun yi nauyi. Na kasa motsawa zuwa inda dana yake.

Wannan duka ya faru ne sakamakon dukan da aka yi mata.

Yaki ya barke tsakanin 'yan kungiyar TPLF - jam'iyyar siyasa da ke da iko da yankin kusan shekara 30 - da kuma gwamnati a watan Nuwamba 2020 watanni bayan fuskantar rikici.

An kashe dubban mutane a yakin - ciki har da fararen-hula - yayin da miliyoyi ke cikin halin bukatar kayan agaji, ake kuma zargin gwamnati da hana ba da damar shigar da kayan.

An zargi duka bangarorin biyu da kashe mutane ba bisa ka'ida ba tare da amfani da cin zarafi ta hanyar lalata domin tsora ta sauran mutane.

A watan Agustan bara, kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty ta zargi gwamnatin Habasha da kawayensu na Eritrea, da kuma dakarun Amhara kan cin zarafin mata.

Sun rika amfani da fyade "a matsayin wani makamin yaki domin rikita tunanin mutane", in ji babbar sakatariyar Amnesty Janar Agnès Callamard.

Daga baya kungiyar ta zargi TPLF da yin fashi da cin zarafi da kuma fyade ga mata a wurin duba ababen hawa a Amhara - wani abu da Ms Callamard ta ce "lafin yaki ne da kuma cin zarafin dan adam".

BBC ta yi kokarin ji daga bakin TPLF amma har yanzu ba su ce uffan ba.

Rahotanni sun nuna cewa dubban mata da 'yan mata da ke zaune a yankunan biyu sun yi ta fama da cin zarafi ta hanyar lalata, amma wata tawagar masu rajin kare dan adam daga Majalisar Dinkin Duniya ta ce "an rage yawan wadanda abin ya shafa" a wannan rikici.

An rawaito cewa a wata takwas din farko na wannan rikici an samu koken wadanda aka ci zarafi 2,200 a yankin Tigray sai kuma 940 a Amhara.

BBC ta tattauna da wasu mata hudu daga cikinsu, ciki har da Fatima wadda ta ce da yawa daga cikin matan ba su kai rahoton hare-haren da aka kai musu ba.

Ta yi aiki ne a matsayin mai kai abinci a wata mashaya lokacin da mayakan Tigray suka mamaye garin da take.

"Da misalin karfe biyu na rana suka shigo. (wadanda suke wucewa) suka ce mana mu yi maza mu rufe kofofinmu kuma muka yi hakan. Daga baya suka ce mu bude mu basu abin sha," in ji ta.

Da yamma wata tawagar sojoji ta dawo.

Lokacin da uwar gidan su Fatima ta ki bude musu kofa sai suka harbe ta suka yi mata rauni.

BBC ta ga munanan hotunan da aka dauka da waya.

Ita kanta Fatima wasu mutum biyu sun mata fyade a wannan yammacin, kwana guda bayan nan sai uku suka kara zuwar mata.

Wasu mata uku ma da ke aiki a mashayar an masu fyade.

'Ba zan taba manta abin da ya faru ba'

Fatima ta koma kauyensu ta ci gaba da aikinta - wata tawagar tarayya ta kara komawa domin korar mayakan Tigray daga Amhara ciki har da Kombolcha.

"Ba na zaton zan taba manta abin da ya faru da ni," ta gaya wa BBC, cikin yanayi na kuka da bacin rai, wata mata ma ta ce mayakan Tigray sun mata irin wannan fyade.

"A lokuta da dama abin kan dawo mani a mafarki. Watakila do dan na damu ne sosai, amma ko da yaushe nakanjin kamar za su kara dawowa,".

Diana Wondimu tana cikin tawagar asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya da suke aiki taimakawa wadanda aka yi wa fyade a Kombolcha.

"Mun rika samun wadanda aka yi wa fyade suka tsira daga duka yankuna a kuma duka matakin shekaru, in ji ta. "A ko da yaushe muna fagabar rataye kai" cikin wadanda suka tsira.

Zemzem na jin cewa za ta kara iya guduwa daga gida a karo na biyu. A baya ta zauna a sansanin 'yan gudun hijira.

Ta dade tana neman yadda za ta amayar da abin da ke cikin ranta amma ba ta samu ba.

"Na gaza yin kuka da farko, sai daga baya ne kukan ya zo."

Yawan cin sunayen da aka yi amfani da su cikin wannan labarin ba na ainihin matan ba ne.