Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugabannin Turai da Amurka za su yi ganawa ta musamman kan Ukraine
Shugaba Joe Biden na Amurka na Brussels domin halartar tarukan tattaunawa kan rikicin Ukraine da ya tsananta.
Tsaro, takunkumi da kuma batun 'yan gudun hijira na Ukraine su ne manya a jerin abubuwan da shugabannin na NATO da Tarayyar Turai da kuma kungiyar manyan kasashe masu karfin masana'antu ta G7 za su tattauna a yau. Kuma manufar taron ita ce ta nuna cewa kan kasashen yamma a hade yake.
Shugaban na Amurka ya je Turai ne cike da fatan nuna hadin kan kasashen yamma a lokacin da tsaron nahiyar ke cikin barazana fiye da yadda ya kasance a gomman shekarun baya.
A taron na ranar Alhmis na kawancen tsaro na NATO, shugabanni sun shirya sanar da samar da ƙarin karfi na soji ga kasashen gabashi da kuma tsakiyar Turai, wadanda ke ganin suna cikin barazanar Rasha.
Haka kuma ana sa ran shugabannin za su amince da tura ƙarin tallafin soji ga Ukraine domin kawar da duk wata barazana ta harin makaman nukiliya ko kuma makamai masu guba, abin da Amurka ta ce kila gwamnatin Rashar na shirin yi.
Shugabannin Tarayyar Turai sun yi maraba da irin wannan gagarumin hadin kai da suka samu daga Shugaba Biden na shigar Amurka a dama da ita a wannan bukata, bayan shekaru na sabani da wanda ya gada Donald Trump.
Shugabannin na EU za su yi shirin tsara yadda za su kara kakaba wa Rasha sabbin takunkumi tare da shugaban na Amurka, kuma za su yi fatan cewa ya da wani shiri na musamman na bazata game da makamashin a tare da shi.
Kasashen Turai dai sun dogara sosai ga Rasha wajen samun makamashin na iskar gas da kuma danyen mai, abin da tarayyar take fatan ganin ta samu wani nau'in makamashin, ko kuma wata kafar da za ta rika samunsa daban da Rasha, wanda kuma Amurka ta yi alkawarin taimakawa.
Yana daga irin tallafin da kasashen za su ba wa Ukraine, inda Firaministan Birtaniya Boris Johnson a wurin taron zai sanar da karin taimakon makamai masu linzami har 6,000 da kasarsa za ta ba wa Ukraine.
Haka kuma a wurin taron Mista Johnson zai sanar da tallafin kudi na fam miliyan 25 da kasarsa za ta taimaka da su wajen biyan sojoji da kuma matukan jirgi na Ukraine.
Bugu da kari Birtaniyar za ta kuma samar da wasu kudaden har fam miliyan 4.1 ga BBC, domin ta taimaka wa sashenta na harshen Ukraine da Rasha tafiyar da ayyukansu a yankin.
An ruwaito Firaministan Birtaniyar na cewa kasarsa za ta yi aiki tare da kawayenta domin karfafa Ukraine ta fannin soji da kuma tattalin arzikinta, yayin da Ukraine din ke samun galaba a wannan fada.
Mista Johnson ya kara da cewa "wata daya da shiga wannan rikici, kasashen duniya suna da zabi, na ko dai su tabbatar da wanzuwar 'yanci a Ukraine ko kuma suna ji suna gani su rasa 'yancin a fadin Turai da duniya baki daya.''
Birtaniya ta ce sabon jerin tallafin da za ta bayar kari ne a kan wasu makamai masu linzami kusan 4,000 da ta riga ta bai wa sojojin Ukraine din.
Kuma kudaden da za ta bayar a yanzu kari ne suma a kan fam miliyan 400 da ta bayar na ayyukan jinkai da tattalin arzikin Ukraine in ji jami'anta.