Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Multichoice: Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan karin kudin DSTV da GOTV
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
'Yan Najeriya da dama na nuna fushinsu a shafukan sada zumunta kan sanarwar karin kudin amfani da DSTV da GOTV da kamfanin talabijin na Multichoice na tauraron dan adama ya yi.
A ranar Talata ce kamfanin multichoice ya fitar da sanarwa kan sabbin kuɗaɗen da kwastamominsa za su biya a matakai daban-daban.
Kamfanin ya ce daga ranar 1 ga watan Afrilu, mutanen da ke amfani da nau'rar decodarsu wajen kallo za su biya N21,000 maimakon N18,400 a matakin kololuwa na premium.
Sannan masu amfani da GOTV a matakin kololuwa na max na N3,600 za su koma biyan N4,150.
Wannan sauyi ko karin ya zo wa 'yan kasar da dama da bazata musamman a wannan lokaci da 'yan Najeriya ke kuka da hauhawar farashi da tsadar rayuwa.
Mutanan da ke kokawa na tsokaci kan da wane za su ji a wannan rayuwa da komai ke kara kudi na walwala, baya ga koken sufuri da tsadar abinci da rashin man fetur.
Shi dai kamfanin Multichoice ya kare matsayarsa na wannan karin kudi kan yanayin kasuwanci a kasar da tsadar kayayyaki wanda ya ce su suka haddasa wannan sauya farashi nasa.
Abin da 'yan Najeriya ke cewa
Galibin 'yan ƙasar dai na tsokaci ne a shafukan sada zumunta irinsu Tuwita da kuma kwatanta kudaden da suke biya da yawan tashoshin da ake ba su.
Sannan suna duba zabin da ya rage a garesu ko ci gaba da amfanin da kamfanin ko sauyawa zuwa ga mai sauki.
Wasu kuma na kiran a kauracewa amfanin da Multichoice baki daya suna cewa akwai wasu hanyoyi ko kamfanonin da ake iya rungumar tsarinsu mai sauki.
"Kowa ya shirya, a kauracewa DSTV!!! Akwai Tstv kuma sun fahimci tattalin arzikin Najeriya, shiyasa suke bayar da kowacce tasha guda kan naira 1 a kullum. DStv bata damu da al'umma ba. Ita kasuwanci kawai. A kauracewa DStv, a saye TSTV!!!
Abin da gaske ne. Na ɓarnatar da kudi wajen biyansu kudin kallo ba tare da na moresu ba saboda ina yawaita tafiya shekarar da ta gabata duk da cewa tsoffin fina-finai suke nunawa na 1960 a lokuta da dama, yanu kuma sun yi kari? Na gaji lol. Bari na makalewa @netflix na daura laifi kan TSTV ba wai@DStvNg ko @GOtvNg
Masu MultiChoice, DSTC da GOTV sun kara kudi. Wannan shi ne lokaci mafi dacewa mutum ya mallaki TSTV mallakar 'yan Najeriya da biyan kasa da Naira 2 kan kowacce tasha. Naira N1000 ya ishe mutum tsawon wata 4 ga tashoshi daban-daban. Anan nake kallon karawar Elclasico tsakanin Real Madrid da Barcelona.
Ya tsari biyan ya koma?
Sanarwarsu ta nuna cewa tsarin Compact Plus da ake biya N12,400 zai koma N14,250, yayin da masu Compact zai koma N9,000 maimakon N7,900.
Tsarin confam zai koma N5,300 maimakon N4,615, yayin da masu Yanga za su koma biyan N2,950 maimakon N2,565.
Sannan masu amfani da dicodarsu ta GOTV za su biya N2,800 a tsarin Jolli maimakon N2,460.
Sannan ma su biyan Jinja kan N1,640 zai koma N1,900, masu GoTv Lite kuma za su koma biyan N900 daga N800.
Me hukumomi ke cewa?
Wadannan ƙarin kudi na zuwa ne 'yan kwanaki bayan hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki ta Najeriya ta bijiro da tsarin bai wa mutanen damar amfani da tsarin biya guda ba tare da kari ba na akalla shekara guda.
Sannan mutane na da zabin dakatar da tsarin da suke biya na kallo akalla sau hudu a shekarar, sannan dole Multichice ta bijiro da layukan tuntubarta kai-tsaye tsakanin kwastamominta a ko'ina ta dukkanin kafafan sadarwa.
Ko a shekara ta 2020 sai da Multichoice ya kara kudin tsarin tashoshinsa kuma sake aiwatar da irin wannan yunkuri ya fuskanci kalubale.
A shekara ta 2020 hukumar ta ce ta kaddamar da bincike kan Multichoice saboda zargin kamfanin da ake yi da babakere a kasuwar kamfanonin taurarin dan adam.
Multichoice dai na musanta irin wadanan zarge-zarge, sannan ya ce a kodayaushe burinsa shi ne inganta tsarikan da za su yi wa ma'abota amfani da tauraronta dadi da saukaka musu.