Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugabannin Turai uku sun jefa rayuwarsu cikin haɗari don ganawa da Zelensky
Ukraine ta yaba wa karfin halin shugabannin Turai uku wadanda suka yi doguwar tafiya mai hadari ta jirgin kasa zuwa Poland domin nuna goyon bayansu yayin da birnin ke fuskantar karin hare-haren Rasha.
Firaministan Poland da na Slovenia da kuma na Jamhuriyar Czech ne suka gana da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a ranar Talata da yamma yayin da dokar hana zirga-zirga ta fara aiki a Kyiv.
Poland ce dai ta kirkiri wannan tafiya, bayan da Tarayyar Turai ta yi gargadi a kan hadarin da ke tattare da yinta.
Firaministan Czech ya ce Ukraine na fada ne domin domin 'yancinta.
Firaminista Petr ya rubuta a shafinsa na tuwita bayan ganawar tasu ''mun yaba da kwazanku na yaki mun sani cewa kuna yaki ne domin rayuwarku. Ba ku kadai ba ne a wannan fafutuka ba, kasashenmu suna tare da ku.''
Shi kuwa Mateusz Morawiecki na Poland cewa ya yi Turai ba za ta taba kasancewa yadda take ba idan ta yi rashin nasara a yakin na Ukraine.
Ya rubuta cewa ''za ta kasance wadda aka yi galaba a kanta, aka kunyata ta kuma za ta zama abar tausayi".
Mista Morawiecki, da Mista Fiala, da kuma Janez Jansa na Slovenia su ne wasu shugabannin kasashen duniya na farko da suka ziyarci Shugaba Volodymyr Zelensky tun bayan da rasha ta kaddamar da yakin mamayar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.
An ruwaito shugaban yana cewa "Ziyararku wani babban goyon baya ne ga Ukraine,"
Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya rubuta a tuwita cewa an tattauna kan batun gagarumin takunkumin da aka sanya, ciki har da batun daukar Rasha a matsayin mai daukar nauyin ta'addanci.