Hotunan Afirka na mako: Daga 4 zuwa 10 ga watan Maris 2022

An wallafa

Zababbun hotunan Afirka da 'yan nahiyar a wasu nahiyoyi a wannan mako:

Short presentational grey line
Kananan yara suna kallon masu gasar ninkaya ta Dakar, babban birnin Senegal, ranar Lahadi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kananan yara suna kallon masu gasar ninkaya ta Dakar, babban birnin Senegal, ranar Lahadi.
A woman prayer above a cave in Ngor, Dakar in Senegal - Friday 4 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mata 'yar kasar Senegal tana addu'a ranar Juma'a yayin da Sufaye mabiya darikar Layene suke addu'o'i a Dakar. Wanna shi ne karon farko da ake gudanar da irin wadannan addu'o'i tun bayan barkewar annobar korona
Female wardens and female detainees dance together at a prison in Ouagadougou, Burkina Faso - Tuesday 8 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mata ma'aikatan gidan yari da kuma fursunoni a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, suna rawa tare ranar Talata domin bikin Ranar Mata ta Duniya…
Women taking selfies in front of a International Women's Day poster showing the Ivorian first lady, Abidjan, Ivory Coast - Tuesday 8 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A babban birnin Ivory Coast, wato Abidjan, mata suna daukar hoton selefi a kusa da wata fosta da ke dauke da hoton mai dakin shugaban kasa a wani bangare na bikin Ranar Mata ta Duniya...
South Africa singers Ntombi Ngcobo Mzolo (L) and Linah Ngcobo (R) at the First Annual Basadi In Music Awards Official Launch in Johannesburg, South Africa - Tuesday 8 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar ce kuma, mawaka 'yan kasar Afirka ta Kudu Ntombi Ngcobo Mzolo (Hagu) da Linah Ngcobo (Dama) suka yi murmushi a hoton da aka dauke su lokacin bikin mawaka da aka yi a Johannesburg domin yaba wa irin basirar da mata suke da ita…
A woman with a poster saying: "Nigeria cannot make progress without her women" takes part in a protest in Ikeja, Lagos in Nigeria - Tuesday 8 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan matar ta shiga zanga-zangar Ranar Mata domin nuna fushinsu kan Majalisun Dokokin Najeriya kan watsi da kudurorin doka game da mata. An yi zanga-zangar ce a Lagos da wasu biranen kasar.
A girl in pink boxing gloves in Lagos, Nigeria - Saturday 5 March 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Asabar a Lagos, wannan yarinyar Nigerian girl wears boxing gloves for a training session…
Damben yara a Lagos kudancin Najeriya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Damben yara a Lagos kudancin Najeriya
Wata mata na sowa a lokacin zanga-zangar adawa da juyin mulki a Sudan a Khartoum a ranar Talata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata na sowa a lokacin zanga-zangar adawa da juyin mulki a Sudan a Khartoum a ranar Talata.
Masu turin a kori kura da ke kwasar shara a Lagos

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu turin a kori kura da ke kwasar shara a Lagos
Magoya bayan ƴan adawa a Zimbabwe na zanga-zanga a Bulawayo a ranar Asabar kafin zaben cike gurbi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan ƴan adawa a Zimbabwe na zanga-zanga a Bulawayo a ranar Asabar kafin zaben cike gurbi
Mai dinkin tufafin zamani Kenneth Ize yana murna a bikin nuna dinkin tufafin mata a Paris

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mai dinkin tufafin zamani Kenneth Ize yana murna a bikin nuna dinkin tufafin mata a Paris
Nau'in tufafi da dinkin Najeriya da aka nuna a Paris

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nau'in tufafi da dinkin Najeriya da aka nuna a Paris

Dukkanin hotuna na da hakkin mallaka.