Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yakin Ukraine: Hotunan yadda mazauna Irpin suke ficewa daga birnin yayin da Rasha ke rusa gidajensu
Farar-hula a Ukraine, wadanda sojojin kasar suke taimakawa, suna ficewa daga karamin birnin Irpin, wanda ke da nisan kilomita 20 daga Kyiv, babban birnin kasar.
Hanyar da suke bi domin ficewa daga birnin tana cike da matukar hatsari, inda wasu ke yin tafiyar-kafa a kan hanyoyin da aka yi wa ruwan alburusai da kuma gadojin da aka lalata.
Birnin Irpin ya tsinci kansa a tsakiyar fafatawar da aka kwashe fiye da mako daya ana yi tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine.
Hare-haren da ake kai wa da makaman atilari da kuma ta sama sun yi sanadin lalacewar wurare da dama, inda a hari guda kadai aka lalata wani rukunin gidaje baki dayansa.
A 'yan kwanakin nan, jiragen kasa sun rika kwashe mutane, galibinsu mata da kananan yara, daga wajen birnin Irpin da ke bayan Kyiv, babban birnin kasar.
A farkon makon nan, an dauki hotunan bidiyon yadda ake barin-wuta kan wani rukunin gidaje da ke Irpin.
Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka