Hotunan wasu yankunan Ukraine kafin da bayan hare-haren Rasha

    • Marubuci, Daga The Visual Journalism Team
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Hare-haren makamai masu linzami na Rasha sun lalata da ɗaiɗaita birane da garuruwa da ƙauyuka a faɗin Ukraine.

Waɗannan hotunan na nuna kafin da kuma bayan ɓarnar da aka yi wa fararen hula tun bayan kutsen Rasha a farkon wancan makon.

Yayin da ya ragewa dakarun Rasha taƙi kaɗan su shiga birnin Kyiv, an kai munanan hare-haren sama a birnin.

Wannan benen na hoton da ke ƙasa makami mai linzamin Rasha ne ya lalata shi a ranar Asabar 26 ga watan Fabrairu.

Ƙaramin birnin Irpin da nisan kilomita 20 a arewa maso yammacin Kyiv ya samu kansa a gaba-gaba wajen zama fagen dagar yaƙin dakarun Rasha da Ukraine a cikin makon da ya gabata.

Hare-haren sama da na makaman atilari sun yi mummunar ɓarna a yankin, inda har wani harin ya lalata gaba ɗaya wannan ginin na hoton da ke ƙasa.

Kharkiv, birnin na biyu mafi girma a Ukraine ya zama shi ne wanda Rasha ta fi kai wa hari tsawon kwanaki kuma a yanzu an lalata cibiyar birnin.

Jami'ai a Ukraine sun ce an shafe dare ana lugude a gidajen mutane da sauran yankuna a ranar Laraba ta hanyar harba makamai, wanda masu shigar da ƙara na Majalisar Ɗinkin Duniya suke bincike a matsayin laifukan yaƙi.

A garin Borodyanka kuwa mai nisan kilomita 60 a arewa maso yammacin Kyiv, hare-haren sama na Rasha ne suka lalata gidajen mutane.

Wani bidiyo da jirgi marasa matuƙi ya ɗauka ya nuna girman ɓarnar, inda har yanzu wani ɓangare na ginin da ababen hawar da ke kusa da shi ke ci gaba da cin wuta.

Chernihiv, wani birni mai nisan kilomita 120 a arewa maso gabashin Kyiv, shi ma ya sha hare-hare a kwanakin da suka wuce daga dakarun Rasha da suka kutsa daga arewa.

Jami'ai sun ce fiye da mutum 30 ne suka mutu a ranar Alhamis sakamakon hare-haren da aka kai unguwannin mutane da birnin, ciki har da makaranta da kuma wani dogon bene mai ɗauke da gidajen mutane.

Hotunan da tauraron ɗan adam ya ɗauka a ƙauyen Rivnopillya da ke kusa da birnin Chernihiv daga arewacinsa, sun nuna ramuka a ƙasa da hayaƙin da ke tashi a gidajen da suike cin wuta sakamakon hare-haren makamai masu linzami da dakarun Rasha suka kai.

Daga Dominic Bailey da Mike Hills da Lucy Rodgers da kuma Zoe Bartholomew.