Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen 2023: Abin da masana ke cewa kan sabon jadawalin zaɓe a Najeriya
Masana sha'anin siyasa a Najeriya sun fara tsokaci kan sanarwar hukumar zabe mai zaman kan ta INEC, na jadawalin babban zaɓe na 2023, inda za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.
Wannan ya biyo bayan rattaba hannu kan sabon daftarin dokar zaɓen da shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a ranar Juma'a, ko da yake da fari an kai ruwa rana kafin shugaban ya amince da dokar.
Dakta Abubakar Kari malami ne a jami'ar Abuja, kuma mai sharhi kan lamuran siyasa a Najeriya wanda ke shaidawa BBC cewa daman hurumin hukumar zaben ne ta fitar da jadawalin, kuma doka ta tanadi a yi hakan shekara guda gabannin zabe.
Kari ya ce ko da yake a baya sun fitar da irin jadawalin, amma saboda sauye-sauyen da aka samu dole ta sanya su sake sabon lale. Ya ce kuma dole su yi hakan bayan nazari kan dokar da tantance komai ya yi daidai da wannan doka.
''Duk da ya ke akwai bambance-bambance da dama tsakanin dokar zabe ta shekarar 2010 wadda a kai amfani da ita a zaben 2015 da wannan sabuwar ta 2023, a gani na manyan bambancin da ke tsakaninsu shi ne; ɗole jam'iyyun siyasa su yi zabukan fidda gwani, da mika sunayen wadanda suka samu nasara, akalla watanni shida gabannin babban zabe wanda a baya ba haka lamarin ya ke ba.
A yanzu jam'iyyu su na da damar fara gangamin yaƙin neman zabe da wuri, kamar yadda sashe na 94 na wannan sanbuwar dokar ya nuna, wato kwanaki 150 kafin ranar zabe, wannan ma babban sauyi aka samu a kan jadawalin zaben.''
Wasu dai na ganin wannan jadawali zai fuskanci cikas, saboda shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan majalisar dokoki su sake gyara a wani sashe na dokar da ya haramtawa masu rike da mukamai a gwamnati shiga zabukan jam'iyya da sauransu.
Sai dai Dakta Kari ya ce, sashe na 84 karamin sashe na 12 da ake takaddama a kai na hana masu rike da mukamai shiga zabukan fidda gwani da sauransu, idan za su yi hakan sai dai su ajiye aikinsu, ba zai taba shafar kwaskwarimar da za a yi wa jadawalin zabe ba sannan majalisa ta na damar sake nazari ta yanke hukunci.
Ko sauyin da aka samu a ranakun zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da na gwamnoni zai iya kawo cikas ga zaben?
Abubakar Kari ya ce ko kadan, saboda sauyin baki daya na mako guda ne, saboda jadawalin farko da hukumar zaben ta fitar da wanda aka yi a yanzu bambancin mako guda ne kacal tsakaninsu, dan haka babu wani tasiri ko cikas da zai yi wa zabukan da ke tafe na 2023.
Hukumar zaben ta ce za a gudanar da zaɓen 'yan majalisun tarayya tare da na shugaban ƙasar.
Zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce an zaɓi ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 360 kafin kaɗa ƙuri'a.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen "a lokacin da ya dace".