Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Malam Muhammadu Idrisa
An haifi Malam Muhammad Idrisa a jiihar Gombe arewa maso gabashin Najeriya, kuma ya fara karatun a hannun mahaifinsa Modibbo Idris Biri, wanda daga baya Allah ya yi masa rasuwa tun lokacin yana da karamin shekaru.
Bayan rasuwar mahaifin Malam Muhammadu Idrisa ne kuma daga nan a unguwarsu ta Jeka-da-fari aka kai shi wata makaranta ta wani malami da ake kira malam Yahuza wanda shi ma daga baya Allah ya yi masa rasuwa.
Daga nan in ji malamin ya taba karatun babbaku da farfaru, da kuma karatun Alkura'ani wanda ya ce har ya kai har izu biyar.
Kana in ji malamin akwai yayansa malam Ahmadu Idrisa wanda bai dade da rasuwa ba, shi ya rika tarbiyantar da shi bayan rasuwar mahaifinsu.
"To shi ya kai ni wata makaranta ta Alhaji Baba Manu ana ce masa ABM, aka saka ni a ajin malam Magaji, shi ma ya rasu Allah ya yi masa rahama, a nan muka yi karatun Alkur'ani har muka sauke,'' ya ce.
Bayan sauke karatun Alku'ani a makarantar malam Magaji ne in ji malamin, daga nan suka fara karatun Furu'a kamar yadda aka saba a arewacin Najeriya, kuma sun karanta Kawa'idi da Ahalari, da Ishimawi, har ya zuwa iziyya.
Bayan kammala karatun a wannan makaranta ne malamin ya shiga makarantar Boko, wanda yayansa malam Ahmadu Idrisa ya saka shi a makarantar firamare har ya kammala, kuma daga nan ya shiga Makarantar Sakandaren Kimiyya inda ya yi shekara uku.
"To lokacin ana yin tsarin karatun nan na 6-3-3-4 ne ake yi, sai aka tura mu muka yi jarrabawa inda daga nan na samu na tafi makarantar da ake kira Comprehensive School - a nan na karasa karatun,'' malamin ya bayyana.
Malam Muhammadu Idrisa ya kuma bayyana cewa daga nan ne ya koma makaranta ya yi karatun Diploma a fannin ilimin addinin Islama da harshen Larabci, kuma bayan ya kammala ne ya koma wata makaranta da ake kira Bin Saleh inda ya yi diploma a fannin harshen Larabci.
Malamin ya kuma yi karatu a wani bangare na Jami'ar Maiduguri da ta bude a cikin Kwalejin Ilimi ta Tarayya a jihar Gombe inda ya yi karatun digiri a fannin harashen Larabci.
Ci gaba da karatun zaure
Kamar a bangaren abinda ya shafi karatu na gida, in ji malamin, akwai malaman da suka rika karatu a wajensu - karatun zaure kenan, kuma in ji shi, babban malamin da ya fi amfanuwa da shi babu kamar malam Ahmadu Waziri wani babban malami a garin Gombe inda ya taba karatu a wajensa, ya yi Risala, ya yi Askara har Muhutisar na taba a wajensa.
Daga nan kuma akwai wani malami da ake kira malam Audu a nan unguwar Jeka-da-fari Gombe inda malam Muhammadu Idrisa ya yi karatu a wajensa kuma yafa fara karatun tafsirin Alkur'ani, sannan sai ya cigaba da karanta Muhutisar a wajensa.
Bayan nan ne kuma ya koma wajen wani malami da ake kira malam Musa a Tundun Wada amma ya rasu, inda a wajensa ya karasa tafsirin Alkur'ani da Muwadda Malik.
Bayan rasuwar malam Musa ne malam Muhammadu Idrisa ya koma hannun malam Bashir Khalifan Modibbo Jobbo, inda ya sake maimaita tafsirin Alkur'ani sannan ya karanta wasu litattafai da suka shafi addinin Musulunci.
Rayuwa cikin karatu
Malam Muhammad Idrisa ya bayyana irin gwagwarmayar da ya yi ta neman ilimi a hannun malaman zaure da dama da ya zauna a gabansu, inda ya bayyana cewa a cikin surorrin Alkur'ani mai girma akwai wacce ta ba shi matukar wahala kafin ya hadda ce ta.
"Lallai a cikin Alkur'ani Izassama'un Shakkat ita ce ta fi wahalar da ni - ta wahalar da ni da gaske, don ina ina tunawa na sha bulala a wurin haddarta a wajen malaminmu malam Magaji na Loddo kafin in samu ta zauna min, ta b ani wahala sosai