Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Petrópolis: Yadda ake neman kusan mutum 200 da suka ɓace a Brazil
Rashin kyawun yanayi ya kawo cikas a kai ɗauki da neman waɗanda suka ɓace a birnin Petrópolis na Brazil, kwana huɗu bayan ambaliyar ruwa.
Masu aikin agaji a ƙasar dole suka rinƙa dakatar da ayyukansu a ranar Asabar saboda ruwa mai ƙarfi. Sun bayyana cewa babu alamun za a samu ko mutum guda da rai.
Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa mutum 146 ne suka rasu, ciki har da aƙalla yara 27 da matasa inda akwai mutum 191 da har yanzu ba a gani ba.
Sama da mutum 900 ne aka ajiye su a makarantu da wasu wuraren sakamakon iftila'in da ya fada musu.
Ko a ranar Asabar sai da ma'aikata suka rinƙa amfani da shebir da diga domin tona ɓaraguzai da kwashe laka. Haka ma masu aikin sa kai na bayar da taimako.
Masu aikin neman na amfani har da zarto a wasu wuraren da kuma taimakon karnuka masu sunsuna guda 41.
A ɗaya daga cikin unguwannin da lamarin ya fi ƙamari, kusan gidaje 80 ne zaftarewar ƙasa ta yi wa illa. Haka kuma kusan mutum 400 ne suka shiga aikin gayya a ranar Lahadi.
Ruwan saman da aka yi a ranar Talata ya zarta matsakaicin ruwan da aka yi a Fabrairu wanda ya jawo zaftarewar ƙasa da kuma ambaliya a birnin na Petrópolis, wanda wuri ne na masu zuwa yawon buɗe ido da ke arewacin Rio de Janeiro.
Shugaba Jair Bolsonaro wanda ya bi ta wurin da lamarin ya faru a saman jirgi a ranar Juma'a, ya bayyana cewa birnin ya lalace matuƙa inda ya ce ya yi kama da filin yaƙi