Coronavirus: Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya ya kai 254,222

An wallafa

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanan adadin mutanen da suka kamu da korona kullum a Najeriya, daga ƙididdigar hukumar NCDC. Muna sabunta shi ne da zarar an samu sabbin bayanai kullum.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 38 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Juma'a 18 ga watan Fabrairun 2022 a faɗin ƙasar.

Jihar Lagos ce ke sahun gaba da yawan wadanda suka kamu da koronar da mutum (18), sai kuma Cross River mai (7), birnin Tarayya Abuja na da mutum (7), sai kuma Oyo (5), ita kuwa jihar Kano mutum (3), sai kuma Nasarawa (3), da Ekiti (1) daga karshe sai Rivers (1)

Yanzu dai adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta ya kai 254,222, amma an sallami mutum 230,530 daga asibiti bayan sun warke.

Yawan waɗanda suka rasa rayukansu sanadin cutar ta korona kuwa ya kai 3,141.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.