Hotunan bikin sabuwar shekarar China ta miliyoyin mutane

An wallafa

Miliyoyin jama'a sun fara bukukuwan shigar sabuwar shekarar da ake lissafinta da bayyanar wata a ranar 1 ga watan Fabrairu. Wannan ne ya kawo karshen Shekarar Saniya zuwa Shekarar Damiya.

A man makes an offering of joss sticks at a temple in Hong Kong

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum na kafa wasu sandunan turaren wuta a wani wurin ibada da ke birnin Hong Kong
Spring Festival lights in the city of Handan, China's northern Hebei province. Photo: 30 January 2022

Asalin hoton, Costfoto/Future Publishing via Getty Images

Bayanan hoto, Dumbin jama'a sun fita zuwa tituna domin kallon yadda aka kayata bishiyoyi a birnin Handan da ke arewacin lardin Hebei na China
A dragon dance troop visits a restaurant in Chinatown in Bangkok, Thailand

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu 'yan rawa da siffar dabbar nan ta 'dragon' yayin da suke cin abinci a unguwar Chinatown da ke birnin Bangkok na kasar Thailand
A boy holding candles in Phnom Penh, Cambodia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani yaro dauke da kyandira a birnin Phnom Penh na kasar Cambodia
A person cracks an egg on a tiger sculpture for blessings at a Chinese temple in Phnom Penh, Cambodia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum na fasa kwai a kan wani mutum-mutumin damisa domin neman albarka a wani wurin ibada a Phnom Penh na Cambodia
Cai Shen Ye, the God of Fortune, walks around the Kapasan Chinese village in Surabaya, Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana zagayawa da Cai Shen Ye, wanda masu bauta a China ke kira Ubangiji Mai Azurtarwa a kauyen 'yan China da ke Surabaya na kasar Indonesiya
Performers play instruments in Yokohama, Japan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu makada na gudanar da wasanni a birni Yokohama na kasar Japan
A man prays in Palembang, Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum na yin addu'o'i a birnin Palembang na kasar Indonesiya

Akwai hakkin mallaka akan dukkan wadannan hotunan.