Hotunan Afrika na mako daga 21 zuwa 27 Janairun 2022

An wallafa

Zabbabbun fittattunn hotunan Afrika na wannan makon.

Short presentational grey line
Wani karamin yaro ya daga karfen nauyi a garin Soweto da ke Kasar Afrika ta Kudu ranar Alhamis.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani karamin yaro ya daga karfen nauyi a garin Soweto da ke Kasar Afrika ta Kudu ranar Alhamis.
Wasannin tsalle-tsalle abu ne na ganin dama a wajen wani atisaye a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasannin tsalle-tsalle abu ne na ganin dama a wajen wani atisaye a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Ranar Asabar da Safe.
Mutane na duba katin riga-kafinsu na korona yayin da ake gagarin aikin allurar a Abuja, ranar Laraba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mutane na duba katin riga-kafinsu na korona yayin da ake gagarin aikin allurar a Abuja, ranar Laraba.
Haka kuma a ranar Larabar ne aka dauki wannan hoton inda wata mata ke sayen gashin kari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Haka kuma a ranar Larabar ne aka dauki wannan hoton inda wata mata ke sayen gashin kari
Wani mutum ke nan a kan doki yayin bikin gargajiya (daba) a garin Garwa da ke arewacin Kamaru.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum ke nan a kan doki yayin bikin gargajiya (daba) a garin Garwa da ke arewacin Kamaru
Wata 'yar kallon gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka ke nan da ake yi a Kamaru, wadda ta shirya wa tsananin zafin da ake yi, a Yaounde ranar Litinin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata 'yar kallon gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka ke nan da ake yi a Kamaru, wadda ta shirya wa tsananin zafin da ake yi, a Yaounde ranar Litinin.
A ranar Litinin ne mai karbar bakunci, Kamaru ta kara da Komoros - Nan mutane ne a titi a birnin Douala da ke kudu maso yammacin Kamarun ke kallon wasan a titi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin ne mai karbar bakunci, Kamaru ta kara da Komoros - Nan mutane ne a titi a birnin Douala da ke kudu maso yammacin Kamarun ke kallon wasan a titi
Sai dai abin da masu kallon wasan ba su sani ba, shi ne an sami turmutsutsu a daya daga cikin kofofin shiga filin wasan inda mutane takwas suka mutu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sai dai abin da masu kallon wasan ba su sani ba, shi ne an sami turmutsutsu a daya daga cikin kofofin shiga filin wasan inda mutane takwas suka mutu
A nan wata yar Moroko ce ta shiga murnar da ake yi a birnin Rabat bayan da kasarta ta doke Malawi ranar Talata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Duk da hadarin da ya faru an ci gaba da gasar inda kasashe suke ta fafatawa domin zuwa matakin dab da na kusa da karshe. A nan wata yar Moroko ce ta shiga murnar da ake yi a birnin Rabat bayan da kasarta ta doke Malawi ranar Talata
Wani dan kasar Gambia yana mamakin yadda kasarsa wadda zuwanta na farko ke nan gasar Afirka ta doke Guinea, ranar Litinin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani dan kasar Gambia yana mamakin yadda kasarsa wadda zuwanta na farko ke nan gasar Afirka ta doke Guinea, ranar Litinin
Ranar Laraba, Masu goyon bayan Mali sun aike da sako a siyance inda suka daga mutum-mutumin jagoran juyin mulkin kasarsu Kanar Assimi Goita, wanda ya bata wa kungiyar Ecowas rai, saboda kin cika alkawarin da ya yi na yin zabe a kasarsa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba, Masu goyon bayan Mali sun aike da sako a siyance inda suka daga mutum-mutumin jagoran juyin mulkin kasarsu Kanar Assimi Goita, wanda ya bata wa kungiyar Ecowas rai, saboda kin cika alkawarin da ya yi na yin zabe a kasarsa
Duk da kokarin da magoya bayan Najeriya suka yi- kamar yadda wannan a Garoua take shirin yadda za ta yi a wajen kallo ranar Asabar, Tunisiya ta doke Kasarta daga gasar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Duk da kokarin da magoya bayan Najeriya suka yi- kamar yadda wannan a Garoua take shirin yadda za ta yi a wajen kallo ranar Asabar, Tunisiya ta doke Kasarta daga gasar
Ranar Asabar dan damben Kamaru Francis Ngannou ya doke France Ciryle Gane, inda ya ci gaba da rike kambunsa na ajin manyan 'yan dambe a fafatawar da suka yi a birnin Kalifoniya a Amurka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Asabar dan damben Kamaru Francis Ngannou ya doke France Ciryle Gane, inda ya ci gaba da rike kambunsa na ajin manyan 'yan dambe a fafatawar da suka yi a birnin Kalifoniya a Amurka.
Dan tseren keken Eritrea Biniam Girmay lokacin da yake murnar zama na biyu a gasar tsere ta Mallorca a ranar Alhamis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan tseren keken Eritrea Biniam Girmay lokacin da yake murnar zama na biyu a gasar tsere ta Mallorca a ranar Alhamis
Wani dan wasan kiriket na Uganda, Christopher Kidega, yake murnar nasarar jefa kwallo a wasansu da India a gasar kofin duniya ta yan kasa da shekara 19 da ke gudana a Trinidad da Tobago.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani dan wasan kiriket na Uganda, Christopher Kidega, yake murnar nasarar jefa kwallo a wasansu da India a gasar kofin duniya ta yan kasa da shekara 19 da ke gudana a Trinidad da Tobago
Taron mutane ke nan suke wanka saboda tsananin zafi a bakin tekun Muizemberg da ke Afirka ta Kudu a lardin Western Cape

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Taron mutane ke nan suke wanka saboda tsananin zafi a bakin tekun Muizemberg da ke Afirka ta Kudu a lardin Western Cape
Kungiyoyin kwadago da masu zanga-zanga ke nan rike da tutocin nuna goyon bayan Falasdinawa a gaban ofishin kasuwancin Isra'ila a birnin Johannesburg ranar Alhamis

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kungiyoyin kwadago da masu zanga-zanga ke nan rike da tutocin nuna goyon bayan Falasdinawa a gaban ofishin kasuwancin Isra'ila a birnin Johannesburg ranar Alhamis
Nan wata mata ce take leke ta tagar gidanta da mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama da aka sanya wa suna Ana, ta lalata a wani kauye da ke kudancin Malawi, ranar Laraba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan wata mata ce take leke ta tagar gidanta da mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama da aka sanya wa suna Ana, ta lalata a wani kauye da ke kudancin Malawi, ranar Laraba
Hotunan gidaje da hasumiyoyi a yankin tsohon birnin Alkahira, na Masar ranar Litinin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hotunan gidaje da hasumiyoyi a yankin tsohon birnin Alkahira, na Masar ranar Litinin
Wani mutum rike da kaji yana magana da jami'an rijistar masu zabe ranar Talata a babban birnin Kenya, Nairobi, domin yi masa rijista kafin zaben da za a yi a watan Agusta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum rike da kaji yana magana da jami'an rijistar masu zabe ranar Talata a babban birnin Kenya, Nairobi, domin yi masa rijista kafin zaben da za a yi a watan Agusta

Images subject to copyright