Tarihin Juyin Mulki a Burkina Faso

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin 24 ga watan Janairun 2022 ne sojojin da ke adawa da gwamnati a Burkina Faso suka tabbatar da karɓe iko da ƙasar bayan tsare Shugaban Ƙasar Roch Kabore.
Wani soja a gidan talabijin na ƙasa ya bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Kabore tare da rusa majalisa.
Rahotanni sun ce sojojin sun kuma kulle iyakokin kasar. Sanarwar da sojojin suka fitar na dauke da sa hannun kanar Henri Sandaogo Damiba, wanda ake ganin shi ne ya jagoranci juyin mulkin.
Ba wannan ne karo na farko da aka fara juyin mulki a Burkina Faso ba.
Jam'iyar MPP ta Mr Kabore ta ce an yi yunƙurin kasha shugaban kasar da wasu ministocinsa.
Gwamnatin Roch Kabore ta sha fuskantar suka kan gazawa wurin daƙile hare-haren kungiyoyin ta da kayar baya.
Tun da farko wasu dakarun ƙasar ta Afirka ta Yamma sun nemi a kori wasu manyan jami'an soja da kuma samar da ƙarin kayan aiki don yaƙar masu iƙirarin jihadi.
An jiyo harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa da kuma wasu barikin soja ranar Lahadi da dare a Ouagadougou babban birnin ƙasar.
A baya sojojin sun musanta labarin yunƙurin juyin mulki ko kuma cewa an kama shugaban ƙasar, amma kuma a yanzu kusan ta tabbata cewa sun yi juyin mulkin .
Rahotanni na cewa ana tsare da Shugaba Kabore ne a wani sansanin soja.
Wasu labaran masu alaƙa
Kazalika, sojoji sun kewaye gidan talabijin na gwamnatin ƙasar.













