Satomi: Yadda 'yan sanda suka kama mutum huɗu bisa zargin dukan wata mata a Maiduguri

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum huɗu cikin tara waɗanda ake zargi da kai hari shagon abincin wata matashiya da ke babban wajen wasan yara na Jihar Borno.

A cikin makon nan ne dai wani bidiyo ya rinƙa yawo a shafukan sada zumunta wanda ya nuna yadda wasu mutane suna zabga wa wata mari da kuma zaginta.

Wadda aka rinƙa duka a bidiyon mai suna Fadila Abdulrahman, na da shagon sayar da abinci ne mai suna Zuhura Restaurant a Maiduguri, inda waɗanda suka ci mutuncin nata suka rinƙa iƙirarin cewa ta yi wa ɗan majalisa Ahmed Satomi butulci.

Sai dai Ahmed Satomi ya musanta batun, tare da cewa ba shi da wata alaƙa da wadanda suka aikata wannan lamari.

Bayan dukan da ta sha, wasu hotuna da Fadila ta wallafa a shafin Facebook sun nuna yadda matasan suka yi kaca-kaca da wajen sayar da abincin nata.

Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun nuna ɓacin ransu kan wannan lamari da kuma kira da a bi mata haƙƙinta.

Me Fadila ta ce game da wannan harin?

.

Asalin hoton, Facebook/Fadila Abdulrahman

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa wasu mutane ne da ba ta san ko su wane ne ba suka je shagonta a cikin Keke Napep inda suka tambaye ta ko tana biyan gwamnati haraji a inda ta kafa shagonta, amma a cewarta, tuni ta daddale da babban manajan wajen wasan yaran na Jihar Borno kan lamarin.

Ta bayyana cewa mutanen sun shaida mata cewa hukumar kula da filaye da safayo ta jihar ne suka turo su domin rushe shagonta cikin minti 30, amma a cewarta, tana ganinsu ta san ƴan daba ne.

A cewarta, nan take mutanen suka fara fasa shagon nata inda ta ce a lokacin da suka soma, sai ta fara faɗa da su inda su kuma suka rinƙa dukanta da zaginta har suka rushe shagonta.

BBC ta tuntuɓi Fadila Abdulrahman domin jin ƙarin bayani amma ba mu same ta ba.

Wannan layi ne

Me Injiniya Satomi Ahmad ke cewa?

..

Asalin hoton, Borno Community Watch

Injiniya Satomi Ahmad wanda shi ne ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Jere a Majalisar Tarayyar Najeriya ya nisanta kansa daga kai wa Fadila hari da rushe mata shago.

A cikin bidiyon dai, an ji matasan da suke dukanta suna ta ambatar sunan Satomi, sai dai ya shaida wa BBC cewa wannan lamari ya zo masa da mamaki da ban haushi da ban takaici .

"Ba da yawuna aka yi ba, ban san lokacin da aka yi ba, ba a sanar da ni lokacin da za a yi ba kuma ban san ko su waye suka yi ba, yadda kowa ya gani a soshiyal midiya haka ni ma na gani," in ji Satomi.

Satomi ya bayyana cewa bayan kama waɗanda ake zargin ya je ofishin ƴan sanda kuma waɗanda aka kama sun ganshi a zahiri ba su gane shi ba saboda ba su sanshi ba, in ji shi.

Me ƴan sanda suke cewa dangane da wannan lamari?

Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Borno Kamilu Sha Tambaya ya shaida wa BBC cewa yanzu haka sun kama mutum huɗu cikin saura biyar cikin waɗanda ake zargi.

A cewarsa, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu na kai wa Fadila hari kuma za su ci gaba bincike a kansu.

Ƴan sandan sun yi Allah-wadai da wannan lamari inda suka ce za su yi iya bakin ƙoƙarinsu domin hukunta irin waɗannan mutanen da ke cin zarafin jama'a.

Dangantakar Satomi da Fadila

Injiniya Satomi ya bayyana cewa wurin da Fadila take sana'arta shi ne ya bata kuma ya taimaka mata wurin karatunta ya kuma ce a baya Fadila ta kasance mai taimaka masa kan harkokin sada zumunta.

BBC ta tambaye sa ko ya taɓa samun matsala da Fadila, amma a cewarsa yau shekara ɗaya bai san me ya yi mata ba inda ya ce ta sha saka hotonsa a shafin Facebook tana zaginsa amma bai taɓa ce mata komai ba.

BBC ta tuntuɓi Fadila domin jin ta ɓangarenta kan dangantakarta da Injiniya Satomi da kuma iƙirarin da Satomi ya yi amma wayarta ba ta shiga.

Wannan layi ne