Afcon 2021: Fifa ta yi jajen rasa rayuka a filin wasan a Olembe a Kamaru

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta aike da sakon ta'aziyya ga ƴan uwan waɗanda suka mutu a wajen filin wasan Olembe na Yaounde a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a Kamaru.

Aƙalla mutum takwas ne suka mutu yayin da 38 suka jikkata, bayan da wasu suka yi ƙoƙarin kutsawa filin wasan da Kamaru da ke karɓar baƙuncin gasar ke fafatawa da Comoros a Yaounde.

Filin Olembe da ke ɗaukar ƴan kallo 60,000, an taƙaita yawan waɗanda za su shiga kallon wasanni a filin saboda annobar korona.

Amma an ambato hukumomin da ke shirya wasannin na cewa kusan mutum 50,000 suka yi ƙoƙarin shiga kallon wasan Kamaru da Comoros.

Sanarwar da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar ta ce "Fifa na jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da hukumar ƙwallon Kamaru da hukumar ƙwallon Afirka bayan mummunan abin da ya faru a filin wasan Olembe."

Hukumar ƙwallon Afirka ta ce tana gudanar da bincike kuma tana tuntubar hukumomin Kamaru kan al'amarin da kuma matakan tsaro.

Caf ta ce babban sakatarenta Veron Mosengo-Omba ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti a daren litinin bayan faruwar al'amarin.

Tsohon ɗan wasan Kamaru Djemba-Djemba wanda ya kallo wasan Kamaru inda ta yi nasara kan Comoros 2-1 ya bayyana al'amarin a matsayin "abin baƙin ciki.

"Muna ciki amma muka ji baƙin labarin cewa wasu sun mutu a wajen filin wasa, wannan labari ne marar daɗi domin Kamaru ta yi ƙoƙarinta a wannan gasa kuma ta gina manyan filayen wasanni," in ji shi.

Ya ƙara da cewa wannan al'amari zai jefa wasu ƴan Kamaru zaman makoki, bayan wasu sun tafi domin goyon bayan ƙasarsu, wannan mummunan al'amari ne da ya faru ga Kamaru.